5

853 64 0
                                    

💥 *💥AUREN F'ARI....* 💥💥

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
*(home of expert and perfect writers)*💡

       *SLIMZY✍🏻*
_Wattpad@slimzy33_

*SADAUKARWA:*
*HAUWA'U MU'AZU AMIR RUMA...*

                    *5*

Kallon jikinta tayi ta daga kai tana kallonsu rike da kwallon,sauran ukun yaran kanwar ummah ne dik jikinsu yayi sanyi kallon rumaisa tayi wacce annuri ya bayyana a fuskarta da gangan tayi hakan,sosai kwallon ta batawa jidda jiki sakamakon dattin dake jikinta....kallon juna sukayi da Ramlah wacce ke kallon ikon allah,cije lebe tayi kawai "muje ciki ramlah"tayi gaba ramlah na biye da ita sunyi taku zuwa goma rumaisa ta sheke da dariya ta juya ga yaran dake tsaye "ya naga dik jikinku yayi sanyi?oya mu cigaba da gashi"suka dau ihu suka cigaba da ball dinsu,

Sosai zuciyar jiddah keyi mata zafi dangane da abinda rumaisa tayi Mata a gaban bakuwa dikda ramlah tasan halin su dama,a parlor sukayi sallama suka shiga ummah na zaune gefenta wata matashiyar budurwa ce hannunta rike da plate din abinci tanaci ta bude baki zata amsa ta gimtse maganarta "au ashe dangin Allah wadai ne"ta yunkura ta mike hannunta rike da plate tazo giftasu ta ja tsaki ta watsawa jiddah wata harara....daga bayanta taji an rugumota "oyoyo anty jiddah"lumshe ido jiddah tayi ko baa fada mata ba afee ce masoyiyarta ita kadai ke sonta "oyoyo afeen anty jiddah ashe kina ciki"

Da faraar ta "ehh ina ciki keda Anty ramly ne sannunku da zuwa ku karasa mana"ta dan saketa suka karasa parlorn,ko kallonsu ummah batayi ba saida suka zauna cikin faduwar gaba jiddah ta hadiyi wani miyau "barka da war Haka ummah ina yini?"ta dan zamo daga kujerar,bata ko kalleta ba "barka dai...sai yanzun kika gadamar zuwa?ina tun tuni yace kizo ki jirashi anan kika biya yawonki tukunna?"ta kalli gefen ramlah...sunkuyar da kai ramlah tayi ta hadiyi wani miyau mai kauri ganin kallon da ummah tayi mata sai ta dan washe baki "ina yini ummah?an wuni lafiya?"

Jimm kadan ummah tayi "lafiya"ta mike tana kokarin dauke plate din dake gabanta da sauri ramlah ta tare ta "ummah bari a kai miki kawo"...saida Ramlah taga ummah ta juyo cike da kissa ta take kafar jiddah ta dago jajayen idonta ta kashe Mata ido alamar ta karbi plate din jiki babu kwari jiddah takai hannu zata amsa,da sauri ummah ta dakatar da ita "au ai ba irin tarbiyyar taki daya da kawarki ba,ita tasan ya kamata tunda saida ta miki nuni da ki amshi plate a hannu na ki kai zaki amsa,koda yake ba laifinki bane haka kikaga uwarki nayi"

  Tsaki taja tayi gaba ta barta nan tsaye tana mika hannu,sosai ranta keyi mata suya,sunkuyar da kai Ramlah tayi tana jinjina yadda zata zauna da wanan a matsayin uwar miji idan ta mallaki Abdallah...komawa tayi ta zauna cike da bacin rai...

*******
  Yana kokarin fitowa da mota ,zai sake fita Abdallah yayi parking a kofar gidan, Yana hango Abdallah ya fad'ada murmushinsa sai yayi parking ya fito Yana dariya,fitowa Abdallah yayi fuskarsa a dan daure ya harde hannu "common man ya ka hardemun hannu haka ko gaisawa bazamuyi ba?dik fushin banje gidanka naga amarya bane?"

"Ehh...ace dik yadda nake dakai inyi aure har yau bakasan gida na ba bakasan matana ba?haba bilal wallahi banji dadi ba ranan har abincu aka shirya maka bakazo ba"...jimmm kadan Bilal yayi yana sosa kai gaskiya bayajin yadda yaga jiddah sukai ido da ido ya tabbatar da ta aminta dashi a matsayin yaya zaije a matsayin abokin mijinta,idan yaje ai komi ya lalace shikenan ya zaiyi da sonta da yakeyi?...tabosa Abdallah yayi "malam kabar wanan tunanin da kakeyi ka taho muje gidana dan yau din nan nakeso muje dakai ka maida motarka ga motana nan muje kawai"...kallonsa bilal yayi ya sauke ajiyar zuciya bashida option da ya wuce ya bisa amma ta yaya zaije gidan ya fito basu hadu da jiddah ba..."owk bari in maida motana ciki yau dai inje in ga amarya inci girkinta kona huta da gorinka".. murmushi Abdallah yayi alamar yaji dadi haka bilal ya juya da motarsa cikin gida yayi parking sauri sauri ya shiga ya shaidawa momynsa zaije gidan Abdallah tayi masa Allah ya kiyaye ya fito har Abdallah ya tada mota ya shiga suka kama hanya....

AUREN FARI....Where stories live. Discover now