25

842 82 14
                                    

*💥💥AUREN FARI...💥💥*

               *SLIMZY✍🏼*
          _Wattpad@slimzy33_

*SADAUKAR WA:*
*HAUWAU MU'AZU AMIR RUMA...*

                      *25*

Kwankwasa kofar rumaisa tayi ummah tana tsaye gefenta,sau biyu rumaisa ta kwankwasa ramlah bata ko ce musu komi ba sai gyara zama da tayi saida suka sake kwankwasawa sanan kamar bazatayi magana ba tace "a bude ne a Murda a shigo mana wai waye ne yake kwankwasa kofar?"ta karasa tambayar tana yatsina fuska hade da watsawa kofar wata uwar harara,.

Cikin faraa rumaisa ta bude ta shiga ta budewa ummah kofar "shigo ummah"...ummah ta shigo "assalamu alaikum"tace cike da faraa tana kallon ko ina a parlorn kamshin turaren daki ne ya daki hancinta tadan gyada kai tace "masha allahu....komi acan acan iyyeeee Alhamdulillahi"tana rataye da jakarta,

Ramlah bata motsa daga zaunen da take ba saidai fuskarta babu yabo babu fallasa ummah ta karasa cikin parlorn ta nemi kujera ta zauna "y'ata amarya masha allahu"

"Barka da zuwa ummah,ashe kune ai bansani ba ma"tayi maganar a dakile daga zaunen da take,

Ummah kallonta tayi kamar ba ramlar da ta sani ba ganin yadda ta gaisheta babu wani girmamawa tana zaune kafa daya kan daya"yadai Ramlah...bakida lafiya ne naga yanayin naki hakan ko Abdallah ne ya tabamun yar tawa?"

Dan zaro ido ramlah tayi "me kikagani?kinga wani canji ne ummah...umhmmm ummah kenan babu fa karki wani d'an damu"

Girgiza kai ummah tayi ta dubi rumaisa,rumaisa ta juyar da kanta gefe kamar Bata fahimci me ummah ke nufi ba dan tasan kallon da biyu tai mata shi,shiru na dan wani lokaci sanan Ramlah ta katse shirun "ina afnan ne?...naga kowa yazo ganina ita kadai ce bata zo ba"

Yar dariya ummah tayi "afee tana gida batajin dadi zazzabi take fama dashi kwana biyu jikin babu dadi"

  "Wayyo"....ramlah tace hade da kauda kai.....

Shiru ummah tayi kusan minti ashirin da shigowarsu ko ruwa ramlah bata basu ba,gyada kai tayi to kodai ita batasan ya kamata bane sai an sanar da ita?koda yake sabon aure ce batasan kan abun ba,abinda ta tuna shine da ta shigo jiddah ke fadawa kitchen ta cika mata gabanta da kayan ciye ciye kafin tayi abinci....gimtse wanan tunanin tayi "ammm y'ata a kawomun ruwa mai sanyi"

Abu na farko kenan daya fara batawa rumaisa rai,lallai ma anty ramlah wato saida ummah ta roki ruwan sanyi....katsewa rumaisa tunani ramlah tayi "amm rumaisa,dan shiga kitchen ki kawowa ummah ruwa da lemo mana akwai chichin da diblan ki dibo muku"tana kai karshe ta mike "ni bari in shiga ciki inyi sallah dan banyi azahar ba"

Ta mike tana kada kwankwaso wata tafiya ramlah takeyi tamkar da gayya take kugunta ne ke motsi a cikin doguwar rigar dake jikinta kanta ko dankwali babu,

Kasa hakuri ummah tayi ta dakatar da rumaisa data mike cike da kunci da bacin rai,ummah tace "ummm tabdijan ga wata sabuwar yar iskar.... Anya kuwa ramlah ce yata dana sani?dika yaushe akayi auren?"

Murmushin takaici rumaisa tayi bata cewa ummah komiba ta nufi kitchen ta dibo chin chin ya jero a tray ta dauko musu lemo fanta ta fito saiga ramlah da hijab a hannu ta fito "ammm rumaisa nasan fanta zaki dauko dan maida ki dauko muku sprite ko coke mana don fantar nan ta Abdallah ce naga yana so"

Kasa hakuri ummah tayi ta watsawa ramlah wani kallo "tou tunda na d'ana ne idan ya dawo ace nice nasha fanta dan dai nasan ko carton goma nakeso Abdallah zai siyamun'ummah tasa hannu ta bude fantar zuciyarta na tsananin tafarfasa,

Tabe baki ramlah tayi ta shige ciki abunta...

Rumaisa da ummah drink din kawai suka sha suka maida hankali akan tv.....sallamar kannen ramlah ce tasa su ummah maida dubansu a wadanda suka turo kofa cike da hayaniya,yar budurwa ce da yara maza biyu sai wata ma wadda zasuyi kai da me kama da ramlaj....rike hab'a budurwar tayi cikin ihu da daga murya "wooooowwwwww......masha allahu anty ramlah....haka gidanki ya hadu"tayi wani juyi dukkansu sukasa ihu cikin parlorn ko rufe kofar basuyi ba,

AUREN FARI....Where stories live. Discover now