23

835 93 22
                                    

*💥💥AUREN FARI...💥💥*

               *SLIMZY✍🏼*
          _Wattpad@slimzy33_

*SADAUKAR WA:*
*HAUWAU MU'AZU AMIR RUMA...*

WANAN SHAFIN KACOKAN SADAUKARWA NE A GAREKI K'AWATA *FEEDHOM.....*💥 MARUBUCIYAR *MATAR ABDALLAH* ....KO KUNSAN YANZUN HAKA TANA NAN DA LABARI MAI KAYATARWA WANDA YAFI *KWAD'AYI*  DADI DA ILIMANTARWA....KU GARZAYA DOMIN NAMU BA IRIN NASU BANE NAIRA 200 KACAL YA ISHEKI KI MALLAKI *SILAR* *WAYE?...* SON SO NAKEYI MIKI K'AWATA❤️❤️🥰🥰💋

                      *23*
Parking motarsa yayi a harabar gidan,bin cikin gidan ramlah takeyi da kallo babu abinda ya canja sai kyau gidan da ya kara mata dikda babu wani abu na gyara da yayi dangane da aurensa,kallonsa tayi suka hada ido ta sunkuyar da kai,karasa parking yayi ya dubeta "muje Ramly"yadda ya kira sunanta ba karamin dadi yayi mata ba,bude motar tayi ta fito wata irin iska mai sihirtaccen dadi ce take kadawa a garin sakamakon hadarin da akayi ruwa bai sauka ba....yana tafe tana biye dashi har suka karasa balcony din da zai sadaka da parlorn gidan.....yana kokarin bude kofa mai gadi ya karaso ya dan sunkuya "barka da zuwa ranka ya dade, Allah ya sanya alheri yasa albarka"

"Ameen baba,ammm a kunna tanki mana sanan zan fita ka kula da gidan inada meeting bayan ishai na awa daya,idan an dauke wuta a kunna gen"

"Tou ranka ya dade"....satar kallon ramlah mai gadi yayi hade da jinjina kai yana tafe yana waigensu har ya karasa wajen zamansa,

A parlor ta zauna ta sunkuyar da kai,kunna globes yayi ya kunna Ac hade da fanka ya wuce sashensa,minti kadan ya fito ya cire rigar shaddarsa sai farar singlet da wandon shaddar,

A gabanta ya sunkuya ya cire mata gyale,lumshe ido tayi yana karewa fuskarta kallo,gabaki daya ta sauya masa zuwa fuskar jiddah....da sauri ya kauda kai gefe cikin faduwar gaba,.... kusan minti uku suna a haka ta bude idonta taga kansa a gefe ga hannunsa rike da fuskarta,muryarta a sarke tace "yadai....dear"..."umm umm babukomi ramlay"dagota yayi ya rungumeta sosai a jikinsa ya zame dankwalin kanta yana shafa sumar kanta da tasha gyara yana shafawa wani sihirtaccen kamshi ke fita daga jikin ramlah,bugun zuciyoyin su a tare suke harbawa ramlah bata taba tsintar kanta cikin wani yanayi me kama da hakanba kissing din wuyanta yayi yana shafata a hankali ya rada mata a kunne "am sorry amaryata,banji dadi ba daya kasance yau kina amarya zan fita inje meeting headquarter dinmu amma banida yadda zanyi...inaso in gina mana rayuwa ne hope ranki be baci ba"

Yadda takeji yasa ta kasa amsa masa sai kada masa kai tayi alamar batayi fushi ba,kissing dinta yayi a goshi yaja ta ya Kai ta dakin ta wanda ya kasance tsohon dakin jiddah ada....

*******
Bilal karo sukayi da sagir a kofar shiga parlor "ya man,ina kokarin zuwa insameka sai gaka kuma?lokacin sallah ya karato muje masallaci ko?"

Shiru bilal yayi yana jiyo sautin dariyarsu a tare gabansa na cigaba da faduwa,yanaji muryar kamar ta jiddarsa saidai bayaso yayi abun kunya, tabosa sagir yayi "mutumina yane naganka hakan meke faruwa ne?"
. girgiza kai kawai bilal yayi"babukomi muje masallacin"

"Owk"a tare suka jero suka nufi massallaci,

Ammiey cike da tsokana tace "anya wanan bakuwar bazanyiwa dana kamunki ba kuwa?wanan kyau haka? Masha Allah tubarkalla amma ku fulanine ko?"

Sunkuyar da kai jiddah tayi tana murmushi "Ammiey abbana ne bafullatani mutumin ruma ne, mahaifiyata ma tanada dangantaka da fulani dan kakarmu mace bafullatana ce"

Zainab ta mike "bari inje inyi sallah nidai,don ke nadan kina onnnn koh?"tace cikin sigar tsokana,

Walida kanwar zee ta amshe "kedai yaya zee akwai tsokana ita bata cika son magana ba amma ke kiyita zuba"

AUREN FARI....Where stories live. Discover now