*💥💥AUREN FARI...💥💥*
*SLIMZY✍🏼*
_Wattpad@slimzy33_*SADAUKAR WA:*
*HAUWAU MU'AZU AMIR RUMA...**15*
Cikin kankanin lokaci jikin jiddah yayi zafi rau Tana kwance jikin ummah Tana rawar sanyi,"jiddah naji jikinki yayi zafi zazzabi ne ke damunki?meyafaru?"..cike da damuwa ummanta ke tambayarta,
Bakin ciki da takaici yasa abeedah jan tsaki ta mike ta fuce daga parlorn,wani kululun bakin ciki ya tokarewa yaya ib wuya ganin yadda jiddah ke rawar sanyi cikin bacin rai a fuskarsa yace "tashi ki shiga ciki ki sauya kayan jikinki kiyi sallah""Tou yaayah ib"ta mike jikinta sai rawa yakeyi,ummah kuwa kallo tabi jiddah dashi ta girgiza kai "wanan yaro to meyake damunsa haka?".
A kufule ib yace "wulakanci ne ai tantagaryar dan iska ne shiyasa ni tun farko bemun ba saboda dan girman kai ne"
"Yanzun dai bari muga zuwansa tukunna muji ta bakinsa tunda munji nata ai ko? Dole aji bangarori biyu ibrahim shine adalci"
Kada kai kawai yaya ibrahim yayi ya mike ya dubi ashmah dake zaune tana kallon film din labarina a tashar arewa 24 "ke kawomin abinci bangarena"be ce komiba ya fice,...itama ashmah ta mike ta nufi kitchen....
*******
A kofar gida Abdallah yayi parking motarsa ya kashe ya fito yayyafi ake ruwan ya tsagaita sai sanyi da garin yayi ya kwankwasa gate din gidan,mai gadi yaleko ta wata yar kafa ganin me knocking din yasa ya bude "barka da zuwa ranka ya dade"
"Barka dai baba,...nace jiddah ta dawo gidan nan kuwa?"ya tsare me gadi da ido cikin tashin hankali,Irin kallon da Abdallah keyiwa baba yasa ya tabbatar akwai matsala yana hango tsabtsar bacin rai da tashin hankali a tare dashi , jimmm jadan baba yayi "ehh bata dawoba tun fitarta da shuaibu driver yazo ya dauketa bata dawo ba"
"Bata dawo ba?kace bata dawo ba?"muryarsa a dashe yake maganar cikin tashin hankali,
"Ehh ...bata...daw...o ba"
Da sauri Abdallah ya juya ya fice ko rufe kofar gidan beyi ba ya fada motarsa ya tada motar ya nufi gidan su ummah....
*******
Zazzaune suke suna cin abinci banda afee da juya cokalo kawai takeyi,hankalinta gabaki daya baya tattare da ita Allah yasa dai bawani abu bane ya sami Anty jiddah....bana fatan Anty jiddah taje gida da kumbyrarriyar fuskar nan domin ummansu bazataji dadi ba,Cokalin fried rice ummah takai baki idonta ya sauka akan afee dake juya abinci tun dazun,"ke afnan meye Haka wani irin cin abinci kikeyi tun dazun?dubi yan uwanki kowa ya gama ke sai juya abinci kikeyi"
Kwalkwal afee tayi da ido nan da nan idonta ya kawo ruwa,ta kalli sashen da abbansu ke zaune yana cin abincu kamar hadin baki suka hada ido "yadai auta...menene bakison abincin ne?"
Yatsina fuska meenah tayi "babu wani rashin so abbah,iyayi ne don ta ganka ai ita ce suka dafa abincin tare da mai aiki ta taimaka mata..kawai dai taganka ne zata soma sanaben data saba"
Wani kallo abbah yayiwa meenah nan da nan ta natsu tati gummm da bakinta "ke afee meke faruwa kika kasa cin abince ne?"
Dire cokalin afee tayi kwallar da take boyewa ta gangaro mata,abbah ne kadai zai saurari maganarta saboda shi yasan hakkin dan adam don haka dole ta sanar dashi ta ankarar dashi shacin hannu data gani a fuskar jiddah,"ina jinki afee"...shiru parlorn yayi suna kallonta,wata uwar harara rumaisa ta watsawa afee da jan dan tsaki Wanda ita kadai tajishi..."abbah...dama ina jin tsoron kada wani abu ya samu anty jiddah ne naga har yanzun yaya Abdallah be shigo ba,kuma be kira yace yaga anty jiddah ba...dama ina zargin...naga..."..bata karasaba Abdallah ya bankado labule ya shigo ya tsaya cikin tsananin bacin rai da tashin hankali ...duka suka juya fuskokinsu akansa suna kallonsa,cikin kosawa ummah tace "kai kuma lafiya na ganka Haka?meke faruwa abdallah zaka shigo mana parlor babu ko sallama,me akayi ina jiddar?"ta jero masa tambayar tana karewa fuskarsa kallo, idanuwansa sunyi jajir,
YOU ARE READING
AUREN FARI....
General Fictionwayace miki ana bawa namiji dama?babu abinda yake canja namiji sai ikon allah idan kince zaki iya canja Abdallah to kin yaudari kanki mazaasu hali irin na Abdallah wadanda basu da lokacin matansu saina aikinsu daban suke basa taba canjawa don haka k...