*💥💥AUREN FARI...💥💥*
*SLIMZY✍🏼*
_Wattpad@slimzy33_*SADAUKAR WA:*
*HAUWAU MU'AZU AMIR RUMA...**26*
A kofar gidan Abdallah yayi parking motarsa ko ciki be Shiga da itaba,fitowa yayi cikin sauri ya nufi makeken gate din gidan ya shiga kwankwasawa,
Mai gadi ne ya bude karamar kofar gidan don ganin me kwankwasawa suka hada ido da Abdallah nan da nan yaja da baya ya tsugunna "barka da zuwa ranka ya dade"
"Barka dai"Abdallah yace beko tsaya gaisuwar da suka saba ba ya shige cikin sauri a bayansa mai gadi ke tafiya cike da gulma yake tambayarsa "yau ko meke faruwa oho uwar tazo ga dan ya shigo a fusace,hmmmm kila dai wani gagarumin lamarin ne yake faruwa"juyowa yayi cikin sauri ya nufi gate wajen zamansa,
Da sallamarsa ya shiga parlorn idanuwansa sunyi jajir kamar gauta,tana inda take zaune ta fad'ad'a faraarta "oyoyo Abdallah na dikda nayi fushi ai Abdallah ka shareni ka mance da mamanka ko?"
Karasawa yayi ya tsugunna gabanta yana shafa kai "kiyi hakuri hajiya gwaggo....wallahi abubuwa ne suka sha kaina shiyasa banzo na gaisheki ba"
"Abubuwa ne sukasa ka mance dani uwarka Abdallah?kokuwa kanajin tsoron zuwa gaisheni saboda ka saki matarka ka auro aminiyarta?.... Abdallah kenan yanzun dik ba wanan ba mu gaisa Bari in kawo maka ruwan sanyi da lemo"tana karasa magana ta mike ta nufi kitchen dinta,
Bin parlorn yayi da kallo babu abinda ya canja hajiya gwaggo akwai tsafta gashi bata taba haihuwa ba itace kanwar mahaifinsa da ke mugun sonsa,kamshin turare ne ko ina a parlorn,shigowarta ne yasa ya daidaita natsuwarsa ta dire masa tray na lemo da ruwa da cup,da kansa ya dauka ya zuba ruwan exotic mai sanyi yasha sosai sanan ya ajiye ya sunkuyar da kansa,..
Shiru hajiya gwaggo tayi tana karantar yanayin nasa kafin tayi gyaran murya cike da lallashi tace "yadai Abdallah na?naga yau dan gwaggo kamar yana cikin damuwa,meya faru meke tafe da kai?"
Shiru yayi kafin daga bisani ya soma magana "hajiya....ina cikin damuwa mai yawa kai na ya kulle munkai matsayin da matar dana auro yau take cemun tunda bana bata kulawa banida lokacinta saina aikina itama zata kawo kwarto gidana kamar yadda jiddah ta kawo me debe mata kewa",
Tafa hannu hajiya gwaggo ta shigayi "Innahlillahi wa innah ilaihi rajiun...me kake fada haka Abdallah?ita amaryar taka take fadin hakan?kai dan kwal ubanka ban ganeba me kake nufi?"
Gumi ne ya karyowa Abdallah "irin matsalar da muka samu da jiddah kenan,gwaggo kaf mata na basu rasa ci ba basu rasa sha ba ballantana sutura amma basuda wani aiki daya wuce complain banida lokacinsu bana basu hakkinsu bana musu soyayya....gwaggo irin yanayin aikina wallahi banida lokacin kaina kuma dik abubuwan da nakeyi da kudin da nake nema inayi ne don in sama mana abinda zamu rufawa juna asiri....gwaggo am the kind of person that am not that romantic,ni banason nacewa mace inyita hira ina bibiyar mace kamar bindi wai soyayya Sam ba haka nake ba irin haka ne ya faru tsakanina da jiddah....ashe amanata suke ci itada aminina bilal shine na saketa na auri ramlah itama ga abinda take fadamun yanzun, yanzun abinda ke damuna be wuce tunanin jiddah da yake hanani sukuni dare da rana, babbar matsalar ummah na,basu jitu da jiddah ba tace batada tarbiyya yanzun ga Ramlah ma ta fara kawo complain dinta"
Tausayin Abdallah da haushinsa ne ya lullube hajiya gwaggo "masha allahu....haka nakeson ji Abdallah bakaga komi ba,ai dik abinda yake faruwa nasani inbaka saniba har gidan su jiddah naje mahaifinka ya turani da niyyar dawo da ita suka sanarmun da rashin mutuncun da kayi Abdallah haka na dawo babu gwiwa,sanan dik abinda kayiwa jiddah anfadamun"

YOU ARE READING
AUREN FARI....
General Fictionwayace miki ana bawa namiji dama?babu abinda yake canja namiji sai ikon allah idan kince zaki iya canja Abdallah to kin yaudari kanki mazaasu hali irin na Abdallah wadanda basu da lokacin matansu saina aikinsu daban suke basa taba canjawa don haka k...