*💥💥AUREN FARI...💥💥*
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
*(home of expert and perfect writers)*💡*SLIMZY✍🏻*
_Wattpad@slimzy33_*SADAUKARWA:*
*HAUWA'U MUA'ZU AMIR RUMA...*_Sakon gaisuwa da fatan alheri gareku:_
*SLIMZY FANS GROUP*
*SLIMZY NOVELLAS GROUP*
*SLIMZY HOUSE OF NOVELS*
*MRS OMAR HOUSA NOVELS*
*AUREN FARI FANS GROUP*
*JIDDAH HOUSA NOVELS*
*RUBUTACCIYAR KADDARA FANS*
*ZAUREN HASKE* *WRITERS**da sauran groups din da ban kira sunansu ba da wadanda suke aikomin da sako na jinjina da yabo slimzy na godiya....ina kaunarku fisabilillahi😫❤😍*
*12*
Cikin sauri ramlah ta karasa gaban madubi tana kallon kanta,babu makeup a fuskarta amma yadda fuskarta tayi ita kanta tayiwa kanta kyau nan da nan ta warware gashinta ta gyara parking kananan kalaba dake kanta tabar guda ta gefen fuskarta,powder ta shafa da lipgloss,ta gyara girarta cikin mintuna da basu wuce biyar ba,can gefen gado ta hango bakin gyalenta ta dauka ta yane kanta har zata fita tadawo ta feshe jikinta da turare,
Karar bude kofarta yasa duka suka juya da dubansu gareta har ummahnta kallon yar tata takeyi "ina zuwa kuma ramlatu da yamman nan?"
Farrr tayi da manyan fararen idanuwanta "ummah bako nayi a waje ina zuwa,idan na dawo zanyi miki bayanin komi"bata jira cewar ummah ba ta fice suka bi ta da kallo....
Key yayiwa motarsa yana son tafiya kusan minti goma bata fito ba to me takeyi mtsww yaja tsaki,hangota yasa ya dakata,fuskarta sai sheki takeyi ga wani annuri dake fita kallonta yayo sau daya ya kauda kansa har ta karaso, gefensa ta tsaya mazunin driver daga waje "ina yini sir Abdallah...fatan kana lafiya"..jinjina kai yayi ya ja numfashi ya furzar yana shakan kamshin turaren ta,"lafiya lau...ya jikin?"a takaice yayi tambayar hade da kallonta cikin wani yanayi,
Take Ramlah ta fahimci yana cikin wani yanayi me kama da damuwa don haka ta nisa cike da kissa "lafiya lau saidai inata kewar aikina yau kawai banji dadi ba baroka da nayi da ayyuka fatan dai kasamu gamawa batare da wata matsala ba"
Jinjina mata kai yayi "ehh na gama"...hannunsa yakai kujerar dake gefensa inda ya ajiye basket ya dauko "ga basket dinki thank you soo much"
Hannu tasa ta karba harda dan durkusawa tana karewa fuskarsa kallo wata soyayyarsa kw fuzgarta "ammm...sir nace ba"
"Umhmmm ina sauraronki ya dai"muryarsa a dasashe yayi maganar "nace na lura kamar kana cikin wani yanayi na damuwa na gano hakan ne a fuskarka da kwayan idonka,ina iya hango bacin rai karara a fuskarka"
Da sauri ya juyo ya zuba mata narkakkun idanuwansa da sukayi jajir,itama shi take kallo cikin wani salo da daukar hankali take kallon nasa,shiko mamakin yadda ta gano yana cikin damuwa da bacin rai yasa yake kallonta,har yaushe suka kebe ko sukai dadewar da zatasan bacin ransa da damuwarsa? sabanin matarsa da kullum suna cikin gida tare batasan damuwarsa ba bata duba yanayin da ya shigo gida dashi saidai ta hau complain...hmmmm yau zai gwadata ya gani tunda har kawarta tasan damuwarsa,
Cije lebe yayi ya girgiza kai "babu komi ramlah, Allah ya sauwake,idan baki samu damar zuwa ba goben ki huta sai monday"
Gabanta ne ya fadi jin ya ambaci monday anya zata iya hakuri da rashin ganinsa har zuwa monday kuwa?ina hakan bazai ma yuwu ba "ai nasha magani anyimun allura insha allahu zanyi kokarim zuwa kodan in tallafa maka goben"
"Owk,babu laifi take care"ya tada motarsa ta dan ja baya tana kallonsa "nagode sir Abdallah Allah ya kara girma"
Jinjina mata kai yayi yaja motarsa yayi ribas yana kokarin barin unguwar tana tsaye tana binsa da kallo...murmushi ne ya subuce mata "akwai kamshin nasara,nakai mataki na farko na mallakar Abdallah"ta furta a fili ta juya rike da basket din take takun ta daidai mai kama da yanga.....
VOCÊ ESTÁ LENDO
AUREN FARI....
Ficção Geralwayace miki ana bawa namiji dama?babu abinda yake canja namiji sai ikon allah idan kince zaki iya canja Abdallah to kin yaudari kanki mazaasu hali irin na Abdallah wadanda basu da lokacin matansu saina aikinsu daban suke basa taba canjawa don haka k...