*💥💥AUREN FARI...💥💥*
*SLIMZY✍🏼*
_Wattpad@slimzy33_*SADAUKAR WA:*
*HAUWAU MU'AZU AMIR RUMA...**29*
Wani irin tari sosai jiddah keyi ta dafe kirjinta,dakawa abidah tsawa ummah tayi "yanzun waye yace ki kawo wanan labarin yanzun tana cin abinci?gashinan ta kware ai sai ki dibo ruwa ki kawo mata kuma kada in sake jin kinyi wata magana kinji na fada miki ko?"
Zumburo baki abidah tayi tana kunkuni ta shiga kitchen sai gata da ruwa ta mikawa jiddah ta karba tanasha,
"Ke kuma daga maganar Abdallah sai ki kware?ina ruwanki dashi da har gabanki zaiyi faduwar da zaki kware?kada in karaji,kuci gaba da cin abincinku"umma ta juya tasa kai tayi dakinta,
Idanuwan jiddah sunyi jajir ba karamin kwarewa tayi ba don jin maganar tayi kamar saukar aradu,hakan yasa ta ture kwanon abincin ta kwantar da kanta jikin kujera tana sauke numfashi sama sama,tsuru tsuru aysha dasu nafeesa sukayi dakyar nafisa ta hadiyi yawu tace "Abla...bamuci abincuba fa tun tasowar mu sai drink da muka sha a hanya ki daure mu karasa cin abincin"
Wani d'aci ne ya tasowa jiddah ta girgiza kai hade da murmushi "maza kici autar gwaggo ni na koshi anjima zan kara kafin in kwanta bacci yanzun bari inyi sallah kinga anyi magriba gashi bamuyi laasar ba ko"jiddah ta kike ta dau wayarta tabar side bag dinta tayi gaba,
Jinjina kai ashmah tayi cikin sigar gulma ta waiga ta ga jiddah ta shige sanan ta juyo tana kokarin yiwa abidah magana "ke abida karki kuma wa abla maganar Abdallah tunda gashi ta kware gaba bamu saniba ko mutuwa zatayi"
Cikin sanyin jiki abida ta amsa da kai ta mike tabar nafeesah da aysha a parlor ta shige ciki....
********
Zuhra da rufaida da momy bakinsu yaki rufuwa sun zagaye bilal a kujerar da yake zaune sai zuba masa hira sukeyi table din dake gabansa kuwa shake da kayan abinci kala kala,Momy ce tayi magriba ta fito inda ta barsu nan ta samesu,rike baki tayi tana kokarin karasowa "ikon Allah yanzun bilal tun tafiyata bakaci abincin ba yaran nan sunata zuba maka surutu kamar an kwance radio?"tare suka kwashe da dariya,wani irin nishadi bilal yake jin kansa ciki yau gashi a gidan su yaga kowa saura abbansa,"momy sun dade basu ganni ba suna kewar yayansu ne shiyasa nima nayi kewarsu kuma nadawo da labarai masu dadi"
Tsalle zuhura ta daka ta koma gefensa "dagaske yaya?wani labarin ne hmmmm ai momy ta fada mana kun jone kaida anty jiddah a kt anata zuba soyewa"
Girgiza kai bilal yayi sanan ya nunata da yatsa "ke ina wasa dake ko?wato inata zuba soyayya nine nace miki hakan?"ya Kai mata harar wasa ta sunkuyar da kai ta toshe baki tana dariya kasa kasa,momy kuwa dariyar takeyi musu ta zauna nesa dasu,
"Assalamu alaikum"dady yayi sallama Tare suka hada baki "oyoyo dady sannu da zuwa"
"Ashe mutanen katsina ne suka dawo ai tun shigowata daga gate nake jiyo hira da dararraku kala kala"
Zamowa bilal yayi ya sunkuyar da kai cike da ladabi "barka da zuwa daddy ka iso lafiya?....kada kai daddy yayi cike da farin cikin ganin dansa daya tilo namiji "barka da zuwa big man"ya shafo kansa ya d'ago bilal ya rungumesa a kirjinsa yana bubbuga bayansa....kwallar farin ciki ce ta fitowa momy dake zaune tana kallonsu,....rike hannun bilal yayi "muje sashena muci abincun tare?"
"Kai daddy?ya bilal ya dawo zaka fara ko idan ba muma bin ku zamuyi ba?"cikim shagwaba rufaida tayi maganar hade da mikewa zuhura ma ta mike suka bi banyasu,
Momy ta daga hannunta sama ta furta "Alhamdulillahi"...sanan ta take musu baya suka watse a parlorn...
********
Tagumi ummah tayi tai shiru fuskarta dauke da damuwa tun bayan ta idar da sallar magriba ta kasa motsawa daga inda take zaune,tunanin yadda Abdallah ya iya kwanaki bezo gidan ta ya ganta takeyi ba wato saboda yayi auro ya auro jaraba? Abdallah danta ne ya juya mata baya yau? misscall nawa tai masa be dauka ba be Kuma biyo call din ba,
Afee ce tayi sallama dakin ta nemi gefen ummah ta zauna tana kallonta,tausayin umman ne ya kamata don tasan kaf yaranta babu wanda takeso kamar Abdallah,ruko hannun ummah afee tayi ummah tadanyi furgita tana kallon afee "ummah...ya naga kinyi tagumi? akwai damuwa ko?"

CZYTASZ
AUREN FARI....
General Fictionwayace miki ana bawa namiji dama?babu abinda yake canja namiji sai ikon allah idan kince zaki iya canja Abdallah to kin yaudari kanki mazaasu hali irin na Abdallah wadanda basu da lokacin matansu saina aikinsu daban suke basa taba canjawa don haka k...