*💥💥AUREN FARI...💥💥*
*SLIMZY✍🏼*
_Wattpad@slimzy33_*SADAUKAR WA:*
*HAUWAU MU'AZU AMIR RUMA...**19*
Wani mugun kallo yaya ibrahim yake watsawa Abdallah,huci yakeyi idanuwansa sun gama sauya kala zuwa launin ja...nuna Abdallah yakeyi da hannu yana takowa dab dashi har ya karaso gabansa ya tsaya,wani kallo yake watsa masa kafin ya cije baki ya shafa gemunsa ya girgiza kai "yaro yaro ne,kayi wawta Abdallah kayi wawtar da harabada bazaka sake irinta ba,sanan ka nuna mana dabbanci da rashin ilimin islamiyya da bai wadace ka ba,da kanada ilimi koda zaka rabu da matarka baxakazo gidan surukai kana wanan haukar ba...."kallonsa yake ido cikin ido "ka saki jiddah kace ko?tou dan allah gobe zan sameka a wajen aikinka ka rubuta a rubuce ka bani sanan ka shaida babu kai babu jiddah harabada kuma ka nuna kai din baka fito daga gidan mutunci ba"
Girgiza kai Abdallah yayi kamar zai bugi kirjin yaya ibrahim "niko na fito daga gidan mutunci sanan nidin banine na nuna halin dabbanci ba sai kanwarka da ta nuna ita din jaka ce da aurenta take hulda da aminina"
Cikin tsawa yaya ibrahim yake magana jikinsa har rawa yake "kada ka saki kanwata kace zaka bi ta da sharri wallahi zan maka ka a kotu ina mai tabbatar maka komi kudinka zanyi Sharia dakai"
Wata irin dariya Abdallah yayi ya dage kafadarsa ya kalli sashen da jiddah take tana rike a hannun abidah da ummah wadanda sukai mata kariya lokacim da take kokarin faduwa,
Zaiyi magana ibrahim ya katse sa da nuna masa kofa "fitar mana a gida mara mutunci kawai....kuma karka kuskura ko harabar unguwar nan inganka dabba"ibrahim ji yake kamar ya shake Abdallah irin kallom wulakanci da yake masa,
Shiko Abdallah mamakim cin mutunci da dan uwan jiddah yayi masa yakeyi zai kuma tabbatar masa da shi din mai zuciya ne....ace kanwarsu tayi masa laifi amma yake cin zarafinsa?haka ya fice dakyar yake taka kafarsa ko gabansa baya gani....
A fusace ibrahim ya juyo yana nuna jiddah da yatsa "kinga irin mijin da kika dauko ko?kinga abinda muke fada miki kinga sharrin da ya biyo baya ko yana zarginki da amininsa ina mai tabbatarwa wanda naganki dashi ne a gaban mota da wanda yazo dazun"....cikin tsawa ya daka mata "koba shi bane dan ubanki"parlorn ya amsa,dakyar ta daga kai tana sauke numfashi hawaye na ambaliya a fuskarta tace "shine....kuma yaya ku gafarceni"
Nunata da yatsa yakeyi yayinda ummah da abidah suka kafeta da ido "ku gafarceni...hakika na aikata babban kuskure na muamala da aminin mijina....amma wallahi bans..."
Bata karasa ba ummah ta sharara mata wawan Mari "hauwau me kike shirin fada?kinaso kice dagaske ne abinda Abdallah ya fadi kin aikata"
Dafe kumatu jiddah tayi tana kuka, rungumeta abida tayi tana kuka itama cikin tashi hankali ummah ke salati cikin kuka "jiddah kinci amanar tarbiyyar da muka baki....kuma bari mahaifinki ya dawo dole yasan yadda zaiyi dake"
Neman waje ibrahim yayi ya dafe kai....zuciyarsa nayi masa kuna,kalamam jiddah sun sagar masa da gwiwarsa dikda idan aka bincika yasan tafi Abdallah gaskiya amma meyasa zatayi haka?....
Gudu yake shararawa a mota hawaye ya wankewa Abdallah fuska,cije lebensa yayi fuskar jiddah ke yawo a idamuwansa,sa hannu yayi ya daki sitiyarin motarsa kamar wani mahaukaci haka ya karkata motarsa ya nufi gidansu bilal.....
Bilal kuwa hawaye ya hanashi magana daga zuhura har ummah da rufaida hankalinsu a tashe yake abincin da sukeci dik dire plate din sukayi, shasshekar kukan bilal ce kawai a parlorn sai karar fanka da Ac da falom ya dauki sanyi...sai kuma tv da yake aiki shi kadai,
YOU ARE READING
AUREN FARI....
General Fictionwayace miki ana bawa namiji dama?babu abinda yake canja namiji sai ikon allah idan kince zaki iya canja Abdallah to kin yaudari kanki mazaasu hali irin na Abdallah wadanda basu da lokacin matansu saina aikinsu daban suke basa taba canjawa don haka k...