*💥💥AUREN FARI...💥💥*
*SLIMZY✍🏼*
_Wattpad@slimzy33_*SADAUKAR WA:*
*HAUWAU MU'AZU AMIR RUMA...**28*
Mamakin yadda ramlah ke gumi Abdallah yakeyi kawai yana kokarin karantar yanayin nata tai saurin wayancewa Tana sosa kai "amm...tou shikenan tunda kana ganin zata dawo gareka"..
Maganar da tayi yayi saurin tambayarta "meyasa bazata dawo ba?...akwai wata kulalliya ko wani kulli a kasa kenan wanda kece kika sanshi?"ya karashe maganar hade da tsareta da ido cike da mamaki,
Inda inda Ramlah ta somayi tana sosa kai "ammm...ummm naga yanayin yadda tabar gidan ne shiyasa umm sweeet muje to mu kwanta mana ni inajin bacci"ta kauda maganar ta hanyar marairaicewa cike da shagwaba,..
Wani irin kallo Abdallah ke jifan ramlah dashi wanda yasa tasha jinin jikinta ta kauda kanta gefe zuciyarta ta tsananta bugawa,yana kallon yadda kirjin ramlah ke safa da marwa,meyasa ramlah keyin abubuwa kamar na marasa gaskiya?....meyasa tace kana tunanin zata dawo gareka ne?...kodai akwai wani kulli da ramlah tasani wanda shi be saniba?meye dalilinta na daburcewa bayan itace take kukan kada ya rabu da jiddah a lokacin?itace wadda kejin tausayinsa lokacin da take sharbar kuka a parlorn momy?
Ruko hannun Abdallah tayi cikin sigar shagwaba murya kasa kasa "umhmm umhmmm....dear ya naga dik yanayinka ya canja meyake faruwa?"ta sargafo hannunsa cikin nata tana murza hannunsa,
Kauda kai yayi cikin yanayi na damuwa sanan ya juyo da sauri ya tsura mata ido lokaci daya ya jefa mata tambaya"amm meyasa yanayinki yake canjawa dik lokacin da nayi maganar jiddah?....meyasa kikayi kuka don nafada miki abinda abbah yace bayan kece bakiso in rabu da ita a baya kike kuka?amma yanzun bakison indawo da ita meye dalili?....sanan furucinki yanada maana da kikace kana ganin zata dawo gareka ne?what do u mean?"....kallom da yake mata ne yasa gumi ya karyo mata lokaci daya ta tsinci kanta cikin tashin hankali don tana iya hango tuhuma karara a kwayar idon Abdallah....hakan yasa tai saurin saita natsuwarta ta zare hannunta daga nashi ta juyar da kanta gefe guda cikin minti biyu hawaye ya wanke fuskarta sanan cikin rawar murya tace,
"Kana tuhumata ko?nasan yanzun kana tuhumata da rabaka da matarka dikda nayi hakan ne don in ceto ka daga kangin da kake gabb da shiga....sanan maganar da nayi niba da wata manufa nayita ba,dama nasan hakan zata kasance saboda kana son matarka kuma bakayimun kwatankwacin son da kakeyi mata....zuciyata ta karaya nafara jin tsoro"
Ajiyar zuciya ya sauke ya janyota jikinsa ya rungumeta sosai yana kallon kwayar idonta yasa hannu ta share mata hawaye "its ok....i cant deny of course inason jiddah and ko bayan rabuwar mu still nakasa cireta cikin zuciyata and yanzun hk xuciyata ta sanarmun da nine silar komi and i am ready in gyara laifina kema kiyi hakuri rashin hakkinki da kulawar da bana baki....and sorry to say kibar wanan tunanin kowa da matsayinta cikin zuciyata don haka lets go and sleep"kafin tayi wani yunkuri Abdallah ya kinkimeta a hannunsa,kallonsa takeyi amma fuskarsa tayi mata bakin kirin furucinsa agareta kamar ya watsa mata rushin wuta,tabdijan wallahi akwai matsala sai nayi maganin jiddah wanan karon don tabbas nabari ta dawo gidan nan ina gidan nan naci baya kuma ba sunana ramlah ba sanan niba yar halak bace jinin buzaye.....
********
Makale jiddah take da waya suna hira da mutanen gidansu abidah daga gefen aysha ta fuzge wayar a kunnen aysha,"Albishirinki Abla wai kinsan munga wanan kidahumin mutumin?"
Cikin rashin fahimta jiddaj ta yatsina fuska "wa ke nan abidah?waye kuma kida humi ni hauwau"
"Hmmm to Abdallah tsohon mijinki"jiddah ji tayi kamar abidah ta soka mata mashi a kirji "kuma in fada miki dan beda kunya harda cewa wai mu shiga mota ya rage mana hanya ya kawomu gida abla,nikam bamu shiga ba nan muka barshi ko sallama bamuyi mushi ba mukai tafiyar mu,hmmmm bakiga yadda ya susuce ya koma ba jin munce wadda zaiyi don ita bata gari ya razana nan da nan yanayinsa ya sauya"gaban jiddah ne ya fadi taja ajiyar zuciya ta tabe baki,
ESTÁS LEYENDO
AUREN FARI....
Ficción Generalwayace miki ana bawa namiji dama?babu abinda yake canja namiji sai ikon allah idan kince zaki iya canja Abdallah to kin yaudari kanki mazaasu hali irin na Abdallah wadanda basu da lokacin matansu saina aikinsu daban suke basa taba canjawa don haka k...