22

752 74 9
                                        

*💥💥AUREN FARI...💥💥*

               *SLIMZY✍🏼*
          _Wattpad@slimzy33_

*SADAUKAR WA:*
*HAUWAU MU'AZU AMIR RUMA...*

                      *22*

Daddare Abdallah yana zaune a parlorn mahaifiyarsa kannensa suna zagaye dashi su meenah sarkin rawar kai sai wani surutai sukeyi "ya Abdallah kawai idan anyi aurenku da Anty ramlah ka hadamu da ita muje umarar tare tunda dama next month zamu tafi ko"

"Ehh ai taren zaku tunda lokacin sungama amarci,yauwa Abdallah nace akwai wata hidima ne da zakuyi na bikin mufara shirye shirye don yanzun ne zakai auren da zan nuna farin ciki"

Girgiza kai Abdallah yayi "babu abinda zanyi ummah,ai ba auren fari bane sanan kuma auren kinga yadda zaayishi babu wani shiri bare armashi"

"Haba Abdallah,ya xakace haka bayan yarinyar nan budurwa ce"..... Abbah ne ya fito daga sashensa ta kofar baya ya shigo parlorn sanye da riga da wando brown kaftani hannunsa rike da makullin mota da wayarsa,....dukkansu suka shiga taitayinsu banda ummah dako kallon inda abbah yake batayiba tunda yake fushinsa,

"Barka da fitowa abbah ina wuni"a sanyaye afee ke gaishesa,dan murmushi abbah yayi "barkanki ummulkhairi ya kike"

"Lafiya lau Abbah"ta amsa hade da murmushi,

Da rumaisa da meenah suka hada baki "barka da fitowa abbah"

"Barkanku ameenah da rumaisa"...ya amsa yana kokarin wucewa,

Tsugunnawa Abdallah yayi hade da kaskantar da Kai cikin faduwar gaba da fargabar ko zai amsa ya soma gaishesa, "Abbah barka da fitowa....ina wuni"..abbah beko san Abdallah na wajenba har zai fita ya dawo,

"Hajiya,wato bakida tsoron allah ke ko?ashe bakida hankali bakida tunani?har yanzun bakisan meke miki ciwo ba bakisan rayuwar duniya ba,amma kibi duniya a sannu kinji don zata karantar dake,yanzun nasan cewar ke kadaice kika haifi Abdallah habiba"

"Haba Alhaji....me kake fadi haka ya zakace haka?"

Cike da takaici yace "ehh ke kika haifesa kece keda ikon sashi yayi ko yakiyi,kinsashi ya saki matarsa kuma kina shirin aura masa wata cikin sati biyu,saboda ki ninamin iyakata ma dan uwanki kikasa yaje ya shiga gaba don nemawa danki aure ko habiba?tou kusani taron biki saidai kuyi a wani waje baa nan ba"

Gumi ne ya karyowa ummah ta sa hannu ta share cikin damuwa da tashin hankali take kallon yadda abbah ke magana cike da izza da isa,sanin halin Abbah yasa ta sunkuyar da kai batare da tace komiba zuciyarta ce kawai ke tafarfasa sanan a gaban yaranta yake ce mata batada hankali duniya zata bi da ita, matukar tace zatai masa musu to tasan zai mata abinda yafi hakan,

Har yakai kofar fita ya nuna Abdallah da yatsa,"banaso ka kara ganina a hanya ko a ina ka nuna nidin ubanka ne"cikin daga murya abbah ke maganar,..wata irin razana Abdallah yayi yana kallon Abbah cikin tashin hankaki ga gumi da dama ya gama jikewa dashi "ehh ka kalleni da kyau Abdallah munkai matsayin da zansa doka ka karya saboda ka dogara da kanka kasamu abun duniya...munkai matsayin da zanbaka umarni ka tsallake umarnina kabi umarnin mahaifiyarka,to da kai da ita dukkanku baku isa ba Abdallah kunyi kadan wallahi....dik abinda zakuyi kuje kuyi wani waje amma baa cikin gidana ba don nan munallina ne Abdallah"

Rugowa afnan tayi ta rike kafar Abbah ta fashe da kuka "dan allah abbah kayi hakuri ka yafewa yayah Abdallah da ummah"...kallon afnan yayi cikin takaici da bacin rai ya janye kafarsa ya fice.....

"Ummah,kibi abbah kintashi hakuri kinajin fa abinda yake cewa"rumaisa ke magana kamar zatai kuka cikin damuwa,

Nisawa ummah tayi "zai sauko haka yake idan yayi fushi"....

AUREN FARI....Dove le storie prendono vita. Scoprilo ora