*💥💥AUREN FARI...💥💥*
*SLIMZY✍🏻*
_Wattpad@slimzy33_*SADAUKARWA:*
*HAUWA'U MUA'ZU AMIR RUMA...**ASSALAMU ALAIKUM*
ina matukar godiya da adduoi da dumbin masoyana sukaimun na rashi da nayi,nagode sosai Allah ya saka da alheri allah ubangiji ya bar zumunci nagode nagode sosai banida bakin da zanyi amfani dashi wajen godiya.....*TUKWICI GAREKU* daukacin members na *HASKE WRITERS ASSOCIATION* ...ina matukar alfahari da wanan kungiya nagode sosai da dumbin kauna bazan mance da ku ba harabada slimzy nayi muku son so fisabilillahi.....👏🏼❤️
*14*
Ajiyar zuciya bilal ya sauke ya ja numfashi ya dora mata kyawawan idanuwansa da tun shigowarsa suke rikida daga fari zuwa ja "zan tafi jiddah...ki kula da kanki kinji?kidaina damuwa idan kinayi nima zanyi damuwar"..jinjina masa kai tayi cikin karayar zuciya idonta na fidda hawaye tasa hannu ta goge "tou nadaina,amma dan allah ina bukatar ka a kusa dani""Insha allahu"ya kama hanyar fita,har ya kai kofa ya juyo yana kallonta itama shi take kallo hawaye na sauka a fuskarta idonta akansa,hakanan bilal ya fice zucuyarsa nayi masa zafi ji yake tamkar ya dawo ya zauna da ita,hakika Abdallah kuskure daya zaiyi a rayuwarsa shine ya saki jiddah idan har ya saki jiddah to tabbas shine zai aureta koda zumuncinsu zai kare,haka yakesa kafa batare da sanin inda yake takawa ba idanuwansa a rufe ya fice gidan,kallo mai gadi ya bisa dashi "anya lafiya kuwa cikin gidan nan?"me gadi ya tambayi kansa kafin ya leka ta karamar kofar gate din yana kallo bilal ya tada mota ya wuce...ba gida ya nufa ba phermacy ya nufa don nemawa kansa maganin wanan ciwon kan.....
Dakyar jiddah tasamu tayi wanka saboda yadda zazzabi ke neman yaci karfinta,haka ta fito jiki babu kwari,tsaye tayi gaban madubi tana kallon fuskarta ba laifi kumburin yadan rage amma jan da fuskarta tayi yana nan saima karuwa da yayi,sama sama ta shafa mai ta fesa turare ta bude drawer ta ciro wata jar atamfa doguwar riga super Holland da gyale ja mai stones,ta sa rigar tayi dauri sanan ta yafa gyalen,tana kokarin daukar wayarta taji horn din mota tasam shuaibu ne ya iso don haka bata tsaya bata lokaci ba ta fito daga daki a parlor ta karkashe globes sanan ta rufe kofa ta fito,
Bayan mota ta zauna ta jikin madubi shuaibu ke kallon jiddah,shi kansa gabansa saida ya fadi ganin jan da fuskar jiddah tayi kamar wadda taji a jikinta ta dago manyan idonta suka hada ido sai ya wayance "ina yini hajiya"yana maganar ya tada mota,
"Lafiya lau alhamdulillahi"tace a takaice ta kwantar da kanta jikin seat ta lumshe idanuwanta,wata irin ajiyar zuciya taja babu wanda ya fado mata a rai sai bilal....
******
Dogayen riguna sukayi anko afee da rumaisa da meenah,ta afee baka ta rumaisa milk colour sanan ta meenah red,suna parlor suna kashe hotuna ko ina ya dauki kamshi ummah na gefe zaune ta nade jikinta da lafaya mai shegen tsada jiddah ta iso,"Assalamu alaikum"tace a sanyaye cikin sarkewar murya,wani kallo ummah tayi mata ta kauda kai tamkar taga kashi,suko yan matan a tare suka juyo,rumaisa da meenah ganin jiddah yasa suka hada rai suka juyar da kai banda afee da ta daka tsalle ta rungumeta "oyoyo oyoyo oyoyo antyna,yanzun nake zancenki a zuciyata ince ko zakizo aje tarbar su abbah dake?"tana maganar tana kokarin kallom fuskar jidda wadda ta sadda kanta kasa "ehh afee ai dole ne inzo yanzun ma yayanku yasa aka kawoni driver gidan nan ne ya daukoni"
Karasowa cikin parlorn tayi ta zauna can nesa da ummah,ta sunkuyar da kai gabanta na tsananin faduwa a d'arare tace "ummah...ina yini barka da yamma"
"Barkanki"ummah tace ta kauda kai tamkar taga kashi,wani takaici ne ya lullube jiddah "an wuni lafiya ya aiki?"
Wata uwar harara ummah ta watsa mata daidai ta dago kanta suka hada ido,da sauri ta sadda kanta tana wasa da gyalenta.."lafiya....aiki kuma ba shi kikaga inayi ba uwar iyayi da yaushema kikasan kicemun ya aiki,mtswwww kinzo daga zuwa zakisa infara tada jijiyoyin wuya"
YOU ARE READING
AUREN FARI....
General Fictionwayace miki ana bawa namiji dama?babu abinda yake canja namiji sai ikon allah idan kince zaki iya canja Abdallah to kin yaudari kanki mazaasu hali irin na Abdallah wadanda basu da lokacin matansu saina aikinsu daban suke basa taba canjawa don haka k...