*💥💥AUREN FARI...💥💥*
*SLIMZY✍🏼*
_Wattpad@slimzy33_*SADAUKAR WA:*
*HAUWAU MU'AZU AMIR RUMA...*INA MAI NEMAN AFUWA NA JINA SHIRU KWANA BIYU HAKAN YA FARU NE SANADIN CIWON IDO DANAKE FAMA DASHI KWANA BIYU AMMA INSHA ALLAHU ZAKUJINI KUYI HAKURI DANI KUBAR KORAFI......👏🏼
INA MASOYANA📢📢📢 MASOYA LITTAFIN *AUREN* *FARI* GA RANARKU DON NUNAMIN TSANTSAR KAUNA, KUYI RUGUNTSIMI MU HADU A LITTAFIN *RAMIN MUGUNTA.....* AKAN FARASHI MAI SAUKI 200 KACAL YANZUN HAKA *RAMIN* *MUGUNTA* YA FITA....HADE SUKE DA *RAMUWAR* *GAYYA* DAGA MARUBUCIYAR ZAMANI FEEDHOM....MASU BUKATAR SIYEN TAGWAYE BIYU ZASU BIYA 300
TA WANAN ACCOUNT DIN
👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
2255398727
Zenith Bank
Amina jibril
Shedar biya tun tunbi wanan number 07042277401*37*
Komawa jiddah tayi ta kwanta ganin ramlah ta fita da alamar akwai abinda take boyewa,tunani ne cunkushe zuciyar jiddah....lallai ma Ramlah duniya kenan babu gaskiya kishi takeyi da ita ko me?idan kishi takeyi da ita tabbas ta wahala,ashe babu dadi ita ta aure mata miji a matsayinta na aminiyarta yanzun har zataji zafin dawowarta gidan kenan?idan haka ne kuwa dik yadda takejin zafin abinda Abdallah yayi mata da tsanarsa da takeji zata danne kodan tayi *RAMUWAR GAYYA*(sabon littafin feedhom)....tunda ai *RAMIN MUGUNTA*(littafin mai cike da sarkakiya na slimzy)ta d'ana mata dan tabar gidan.....lamo jiddah tayi cike da tunani kala kala taji horn din Abdallah,ta dubi agogo karfe bakwai da rabi na safe tayi murmushin mugunta...*******
Kwance bilal yake ya tsurawa ceiling din dakin ido tamkar mutumin daya samu ciwon barin jiki cikin kwana daya kacal fuskarsa ta rame sosai ya kara fari....lumshe ido yayi ya bude jiddah ce ta fado masa sai hawaye masu zafi suka shiga zarya a idanuwansa gefe da gefe suke gangarowa....a tare momy da daddy suka shigo dakin ko wanne fuskarsa ba walwala haka suka karaso suka tsaitsaya a gefen gadon,Daddy ne yayi gyaran murya "yadai bilal....katashi lafiya?ya jikin how are you feeling now?"
Kallon daddy yayi ya girgiza kai"am ok"kawai yace a takaice ya rufe idanuwansa rufffff,kallon juna sukai shida momyn "my boy ka bude idonka ka kallemu mana mune fa iyayenka"
Girgiza kai ya sakeyi"bana son ganin kowa a kusa dani ina bukatar kad'aici momy zuciyata cike take da ciwuwwuka kala kala wanda inajin hakan a jikina tamkar bazan rayu ba"dakyar yake fidda maganar,take tari ya sargafe shi nan da nan momy ta karasa ta tallabosa "sannu my boy....kayi hakuri kadaina wadanan maganganun kaji?dama allah be kaddari cewar jiddah zata kasance matarka ba kaji?"....bude idanuwansa yayi yana kallon momy wasu hawaye ne suke kara bulbulowa a idanuwansa,
"Tabbas nayiwa Allah laifi dolene ya hukuntani ta wanan hanyar, ta hanyar hanani auren jiddah....amma ina mai tabbatar muku bazan taba daina sonta ba saboda da soyayyarta na rayu da ita na ginu kuma d soyayyarta zan mutu momy da daddy"
Kada kai daddy yayi "wace irin magana kakeyi haka bilal kamar wadda baiyi imani da kaddara ba?kasan cikar imanin mutum shine yayi imani da kaddara mai kyau da mara kyau"
Murmushi bilal ya sakeyi mai ciwo"tabbas tawa kaddarar itace soyayyar matar aminina a da"
Ajiyar zucuya daddy ya sauke"har yanzun Abdallah amininka ne kuma kana kaunarsa kuma harabada bazaa taba daina kiranku da aminan juna ba dan haka dukkanku allah ne ya jeho kaddara da shedan a cikinku kuma Dole kuyi hakuri ku rungumi kaddara kudawo ku kasance waje daya"
Momy ranta ne ya baci da kalaman daddy "kai alhaji kasan abinda kake fada kuwa?mutanen da basusan halarci ba?"
"Sunsan halarci tunda har yanzun ina tarayya da mahaifim yaron kuma shi yanada yakinin cewar yaronshi ba haka kawai ya aikata hakan ba,tafaru ne ta sanadin shedancin mace wadda yarinyar har yanzun tana gidan a matsayin matar Abdallah,yafiso Abdallah ya gano abinda Ramlah tayi da kansa yayi mata hukunci baa zaunar dashi a fada masa ba"
YOU ARE READING
AUREN FARI....
General Fictionwayace miki ana bawa namiji dama?babu abinda yake canja namiji sai ikon allah idan kince zaki iya canja Abdallah to kin yaudari kanki mazaasu hali irin na Abdallah wadanda basu da lokacin matansu saina aikinsu daban suke basa taba canjawa don haka k...