*💥💥AUREN FARI...💥💥*
*SLIMZY✍🏼*
_Wattpad@slimzy33_*SADAUKAR WA:*
*HAUWAU MU'AZU AMIR RUMA...**18*
Tsaye Abdallah yayi yana bin Ramlah da ido yadda take hawaye yasa jikinsa ya kama rawa, Yana jin wasu kalamai daga bakinta lokacin daya shigo masu kama da almara,yana jin furuci mai kama da rabuwarsa da jiddah....zuba hannu yayi a aljihu ya tsaya tsakiyar parlorn yana kallon Ramlah ...da sauri ta share hawayenta tayi murmushi kanta a kasa ta soma gaishesa "ina yini sir Abdallah"
"Lafiya... menene kike hawaye haka?ina gab da shigowa nakejin wani furuci masu kama da almara daga bakinki,ko zan iya sanin me kike fada?"
Ya zuba mata kyawawan idanuwansa da suke kara narkar mata da zuciya, girgiza kai tayi tana wasa da gyalenta kanta a kasa "babukomi magana ce mukeyi da ummah"
Cikin takaici ummah ta amshe "ki fada masa abinda kikasani karki boye masa saboda hakan cutarwa ne,tunda dama ga halin da muke ciki da iyayen yarinyar gara ki sanar dashi mu nemi mafita"
Girgiza kai ramlah tayi "ummah...ina gudun matsala banason abinda zai shafi auren jiddah. Domin itadin yar uwatace ina matukar kaunarta"...tana gama maganar ta zamo ta durkusa gaban Abdallah "dan allah kayi hakuri ka yafewa jiddah...kada hakkin aure ya kamata inason yar uwata"
Sai hawaye,saukar da ajiyar zuciya yayi,"a halin yanzun nida jiddah munkai matakin da iyayenta suke bukatar raba aurena da ita,wata kil hakan alheri ne dikda inajin sonta cikin zuciyata...babu abinda ya canja daga soyayyar da nakeyi mata,abu daya ne yajzun inaso insan me nakeji sama sama lokacin da nashigo...ki taimakeni ki sanar dani"
Hawaye ne suka zubowa ramlah tasa hannu ta share,ummah ta katseta "kina tunanin sanar damu abinda ke faruwa?kina ganin duniya zata zageki idan maganar ta fito ko?to kisani babu wanda zaisan da maganar nan saini da Abdallah"
Kallon gefen su rumaisa ummah tayi"ku shiga ciki"dik suka mike jiki babu kwari rumaisa bataso hakan ba taso a fadi komai suni,...afee kuwa bugun zuciyarta da furgicin da ta shiga yasa miyaun bakinta ya kafe motsi kwakwara ta kasayi balle ta mike ta shiga daki kamar yadda ummah tace"kece bazaki tashi ba? saina ci ubanki?"sai lokacin afee ta dawo hankalinta,da kyar ta mike jikinta na rawa,mamaki da al'ajabin Ramlah takeyi dama Haka duniya ta lalace?haka rayuwar ta koma?....jikinta na sassarfa ta mike dakyar take takawa tayi hanyar dakinsu.....
Juyowa ummah tayi "umhmmm ina saurarenki"
"Tun farko jiddah ta sanarmun da cewar Abdallah baida lokacinta,don haka ita zata soma hulda da mazan waje tunda komai tayi shi zaa rubutawa zunubin"
Wani irim zabura Abdallah yayi kamar mayunwacim zaki jikinsa na kyarma zufa kawai ke kwarara jikinsa kamar ana watsa masa ruwa jikinsa kamar ansa masa shocking....
********
Cikin sauri Bilal ya fito daga motarsa,ganin yayan jiddah a kofar gate tsaye yana danna waya ya karasa ya mika masa hannu cike da ladabi..."Barka da yamma"yace yana kokarin mika masa hannu su gaisa,
Kallonsa yayi kamar ya taba ganin fuskar,"barka dai...ya aiki"
"Lafiya lau alhamdulillahi...."
Shiru ya biyo baya kansa a kasa yaya ibrahim yace "yadai...waye kake nema ko kana tambaya ne?".
Gabansa ya fadi,to me zaice masa?yazo wajen jiddah ko yaya?sosai keya yayi "ummm... nazo wajen jiddah ne"
Da sauri ya ya Ibrahim ya dubesa "tou daga ina kuma?a ina kasanta"ya kara jefa masa muguwar tambaya a karo na biyu,
ČTEŠ
AUREN FARI....
Beletriewayace miki ana bawa namiji dama?babu abinda yake canja namiji sai ikon allah idan kince zaki iya canja Abdallah to kin yaudari kanki mazaasu hali irin na Abdallah wadanda basu da lokacin matansu saina aikinsu daban suke basa taba canjawa don haka k...