part eleven

102 3 0
                                    

🌹🌿🌹🌿🌹
🌹🌿🌹🌿
🌹🌿🌹
🌹🌿

🌿 *TAWAKKALI 2021*🌿(Labarine nooriya da "mijin yayarta")
_Labari ne me taɓa zuciya_

🌹
🌿🌹
🌹🌿🌹
🌿🌹🌿🌹
🌹🌿🌹🌿🌹

Page2️⃣1️⃣to2️⃣2️⃣

WRITTEN BY

🌹 *AMINA UMAR FARUQ* 🌹
_Kwantagora_

Marubuciyar
*DA SANNU*
*ZUCIYATA CE*
*AFSANA*
*KYAUTAR ALLAH CE*
*ZAUJUN MAJNUN*
*HASKE BAYAN DUHU*
and now
*TAWAKKALI*

_SADAUKARWA GA_
_Aminiyata NAFEESA HUSSAINI Ina roƙon ALLAH yajikanta da rahama ameen ya rabbi_🤲

AminaUmarFaruq
Wattpadhttps://my.w.tt/Wmw7uCRxGcb

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

*® _PEN: WRITER'S ASSOCIATION_*

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
______________________________________

*~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~*
_____________________________________

https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/

*_Bismilahirrahamaniraheem_*

Typing ✍️

"Ummana! ummana!! ummana!!! saida ta kirata sau uku kuma kowani sai ta amsa cikin rawar murya me cike da tsantsan rauni da tsananin tausayin autar nata tace na'am autana,

tasake cewa ummana! tace na'am autana nasan duk abinda kikeji a zuciyar ki ciwo ne me matuƙar zafi, hakan nima nake jishi nayi kuka nayi kuka akan abinda akai maki, amma nayi hakuri domin haka ALLAH yatsara zaya farudake tun ran gini tun ran a.

"Wanda ni ban isa nahana faruwar hakan ba, dan haka inason kema, dan ALLAH kiyi hakuri ki ɗauki *KADDARAR* da ALLAH yaɗora maki kinji?..nasan abinda matuƙar CIWO amman ki daure kinji autana.

"Kai ta ɗago tareda ƙurawa umman ido yayinda hawaye kebin kyakkwar fuskar ta datayi fayau, sai kuma ta girgiza kai cikin rawar murya me cike da sarƙewa, tace "Ummana me nayi mashi" da yazaɓi yaɓata mun rayuwata me yasa yarasa wacce zaya zalunta sai ni?..

"Ummana nice fa *Nooriyan* ki da Abba da yah *Naf* nice fa *Noor* ɗin aunty *Nafee* shine zayai mun fyaɗe Ummana meyasa yai mun haka?.

"Wani irin bugawa ƙirjin yah*Naseer* ya sakeyi fiye da tunani me tunani, har saida yarintse ido tareda kai hannushi saitin ƙirjin shi inda zuciyar shi take bala'i harbawa fiyeda misali yayinda tsoro yasake kamashi,

cikin ranshi sosai yake roƙon ALLAH yasa karta" faɗi shine yai mata fyaɗe..."Cikin sanyi jiki umma tace autana "wanene yai maki fyaɗe?..

"Yayinda cikin wani irin mugun rawar jiki aunty *Nafee* ta damƙo hannun *Nooriyan* bakinta na rawa, tace "eh my *Noor* faɗa mun "wanene yai maki fyaɗe nayi maki alkawani zan ƙwatar maki hakkin ki zanyi shari'a dashi ko "wanene kinji faɗa mun?...

"ahankali ta maida kallonta ga aunty *Nafee* hawaye na cigaba dazuɓa akan fuskarta tamkar anbuɗe fanfo amma batace komai sai girgiza kai da takeyi....

"Shikam yah *Naseer* duk wanda yakalle shi zaya hango tsantsan tashin hankali atareda shi, domin kuwa wani irin bala'in gumi ne yake tsatsufo mashi ta ko'ina musamman agoshin sa wanda kana gani kasan na zallar tashi hankali ne sai sharewa yakeda hankacif ɗin hannun shi,

sosai yaji ajikinshi shikenan yau asirin shi zaya tonu amma kuma azuciyar shi bai fidda rai da rahamar ubangiji shi ba. "Dan haka aranshi yake faɗin ya ALLAH ni bawanka ne nasan nayi maka laifi ina roƙon ka da kayafe mun, ka rufamun asiri ya ALLAH kai gafuru rahim ne, me gafara ga bayinshi dan hak kagafarta mun.

TAWAKKALI labarin nooriya da mijin yayarta labarine me taɓa zuciyaWhere stories live. Discover now