🌹🌿🌹🌿🌹
🌹🌿🌹🌿
🌹🌿🌹
🌹🌿
🌹
🌿 *TAWAKKALI*🌿
(Labarin Nooriya da "mijin yayarta")🌹
🌿🌹
🌹🌿🌹
🌿🌹🌿🌹
🌹🌿🌹🌿🌹Page 5️⃣6️⃣to5️⃣7️⃣
WRITTEN BY
🌹 *AMINA UMAR FARUQ*🌹
_Kwantagora_Marubuciyar
*DA SANNU*
*ZUCIYATA CE*
*AFSANA*
*KYAUTAR ALLAH CE*
*ZAUJUN MAJNUN*
*HASKE BAYAN DUHU*
and
*TAWAKKALI*_SADAUKARWA_
*Aminiyata NAFEESA HUSSAINI Ina roƙon ALLAH yajikanta yaimata rahama amin 🤲 ya rabbi*Wattpad AminaUmarF
✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
*_PEN WRITERS ASSOCIATION_*
✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
__________________________________
*~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~*
____________________________________
https://www.facebook.com/110384724043172/
https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/Typing✍️
*"Nooriya* kinsan abinda kike faɗa kuwa shi "Alh *Naseer* ɗin ne mugu azzalumi?, da sauri tace "eh mugune, yace sannan kuma kikace shine yakashe "yar'uwarki?...
cikin tsananin kukan da yafara cin ƙarfinta tace "eh abba, cike da mamakin ta yace ikon ALLAH *Nooriya* dama mutun yana kashe mutun ne?..da sauri ta kalle shi da idanunta dake zubar hawaye,
"Yace asanina ALLAH shine me kashewa me rayawa kema kinsan hakan, wanda shine yakashe "yar'uwarki bawani ba.
"Sannan a iya sanina Alh *"Naseer* mijin yar'uwarki mutun ne managarci me matuƙar kirki da girmama mutane, alkairin shi yanada matuƙar yawa wanda idan ban mantaba ke" dakanki kinsha faɗamana hakan ni da ummanki ko?..
yana me kallon umma kai ta gyaɗa alamar "eh, sannan yacigaba da cewa to amma meyasa yanzu zaki jefe shi da wayan nan kalamai marasa daɗi, dan nace ki aure shi eye?, cikin tsantsan kuka tace "eh abba ni banasan shi.
"Yace shine zaki bishi da munanan kalamai haka?, bata iyacewa kokai ba sai kuka kawai datake garza yayinda kanta yana boye abayan umma, alamar ƙwarjin abban bazaya bari ta'iya kallon shiba..
yace *Nooriya* faɗamun abu ɗaya dayai maki cikin biyun dakika ce, ina nufin mugunta me yai maki ko wani irin zaluntar ki yai eye?. sosai taji aranta kamar tafaɗa masu, saidai kuma tasan kotafaɗa baza'a taɓa yarda da'ita ba koda kuwa zata rantse ne,
shiyasa tayi shuru ta batare datayi magana ba sai kukan datake aikinyi jikinta kuwa sai faman rawa yakeyi, itadai umma batasamu nacewa ba da alama mamakin kalaman autar tane yai mata yawa,
kamar yanda yah *Naf* shima mamakinta yakeyi har aranshi yana faɗin, meyasa *Hasken* gidansu ta alaƙanta yah *Naseer* da wayan nan kalaman haka? ayanda yah *Naseer* yake mutun me matukar kirki da kyautatawa ga mutane, ayya babu wata aƙasa kuwa?.
"Abba kam wani irin murmushi yai tare da cewa kenan cikin abu biyun ba abinda yaimaki ko?, cikin tsananin kuka me cike da bakinciki tace abba nidai banasan shi ne dan ALLAH kajanye maganar aura,
murmushi yasakeyi tareda cewa *Nooriya* kenan tunda bayyi maki komai ba ai shikenan, dama nariga nayanke hukunci na "bashike" kuma kin sani bana magana biyu, dan haka kisani bawai nafaɗa maki bane dan ina neman shawararki,
a ah nafaɗa makine dan kigane UMARNI ne nabaki, kinga kenan bin umarni na kuwa abune dayazama dole agareki, yana gama fadar haka yamiƙe yazura takalmin shi yafita fuska ahaɗe.
YOU ARE READING
TAWAKKALI labarin nooriya da mijin yayarta labarine me taɓa zuciya
Historical FictionTAWAKKALI Labarin nooriya da mijin Labari ne me taɓa zuciya