part twenty five

86 4 0
                                    

🌹🌿🌹🌿🌹
     🌹🌿🌹🌿
          🌹🌿🌹
              🌹🌿
                   🌹
🌿 *TAWAKKALI*🌿
(Labarin Nooriya da "mijin yayarta")

🌹
🌿🌹
🌹🌿🌹
🌿🌹🌿🌹
🌹🌿🌹🌿🌹

Page 5️⃣1️⃣5️⃣2️⃣to5️⃣3️⃣

WRITTEN BY

🌹 *AMINA UMAR FARUQ*🌹
            _Kwantagora_

Marubuciyar
*DA SANNU*
*ZUCIYATA CE*
*AFSANA*
*KYAUTAR ALLAH CE*
*ZAUJUN MAJNUN*
*HASKE BAYAN DUHU*
and
*TAWAKKALI*

_SADAUKARWA GA_
*Aminiyata NAFEESA HUSSAINI Ina roƙon ALLAH yajikanta yaimata rahama amin 🤲 ya rabbi*

Wattpad AminaUmarF
✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
   *_PEN WRITERS  ASSOCIATION_*
✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
__________________________________
*~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~*
____________________________________
https://www.facebook.com/110384724043172/
https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/

Typing✍️

  "Me kace?. cike da tausayin shi yasake cewa yallaɓa tabbas "madam ta rigamu gidan gaskiya..wani irin mugun bugawa zuciyar yah *Naseer* tayi cikin tsawa yace ƙarya kakeyi matata" bata mutu ba,

yace wlh yallaɓa "madam tarasu ture likita salim yah *Naseer* yai daƙarfi tareda afkawa ɗakin, yayinda likitan yabi bayan shi da sauri yana faɗin kayi hakuri yallaɓai madam tarasu.

"Cikin tsananin tashin hankali haɗeda masifar ruɗani yake faɗin ƙarya ne my wiffy bata mutu ba, cike da masifaffen rawar jiki ya ƙarasa gurin gawar aunty *Nafeen* wacce tuni an rufeta da farin zanin asibitin, kamar dai yanda akeyiwa mutum idan ya mutu musamman a asibiti.

"Zubewa yayi gabanta" jikinshi na tsananin rawa, yasa hannunshi dake masifar karkarwan tashin hankali, yaye zanin cikin azababben ruɗani yace my wiffy doctor salman yafara wasa da aikinsa ke! yauma inaganin yahaukace ne, kinji me yace" kuwa?..

"Mahaukacin cewa yai wai kin mutu fa, nikuma nasan ƙarya ne bazaki mutu kibarni bako?..yaƙarasa faɗi tareda ƙurawa kyakkwar fuskar ido, wacce ke ɗauke da wani irin asirtaccen murmushi gawani annurin haske dake fita tamkar dai kayi mata magana ta amsa.

"Cikin rawan baki yasake furta ai haka ne ko wiffy baki mutuba ko?..yana me jijjagata cike da mugun ruɗani, saidai ganin ko motsi batayi ba yasashi sake jin wani irin muguwar bugawa da zuciyarshi tayi,

cikin tsananin ruɗani yace pls my wiffy karkiyi mun haka wlh zaiyi matuƙar wahala najure rashinki agareni kinji?, so tashi nayi maki alƙawari duk inda ake samo lafiya aduniyar nan zan samu maki, ko duka dukiyata ne zan bayar kinji my wiffy?.

yakarashe faɗi da sa hannuwan shi duka biyu ya tallabo kyakkwar fuskar me cike da annurin rahama
sai still bata motsaba balle ta amsa shi.

_"ALLAH sarki yah *Naseer* rai kam ai bakon duniya dazaran yatafi shikenan bazaya sake dawowa ba_, ganin hakan ne yasake jefashi cikin tsananin ruɗani yayinda yafarajin kanshi yana wani irin azababben sarawa,

"da sauri yamiƙe jikinshi na masifar rawa ya zauna gefen gadon tareda ƙoƙarin ɗagota, zaya rungume yaname sake faɗin pls my wiffy dan ALLAH karki mutu kibarni kinji?..yaƙarasa faɗi tareda karasa ɗagota aikam tafaɗo jikinshi luuuu!,

wanda yake nuna mashi cewa tabbas fa batada rai...wani mahaukacin runguma yai mata da sauri tareda rintse ido zuciyarshi tana cigaba da mugun halbawa, sai kuma yabuɗe ahankali saidai me wani irin duhu ne yai matuƙar mamayema ganishi.

TAWAKKALI labarin nooriya da mijin yayarta labarine me taɓa zuciyaWhere stories live. Discover now