part twelve

100 3 0
                                    

🌹🌿🌹🌿🌹
     🌹🌿🌹🌿
          🌹🌿🌹
               🌹🌿

🌿 *TAWAKKALI 2021*🌿(Labarine nooriya da "mijin yayarta")
_Labari ne me taɓa zuciya_

🌹
🌿🌹
🌹🌿🌹
🌿🌹🌿🌹
🌹🌿🌹🌿🌹

Page2️⃣5️⃣to2️⃣6️⃣

WRITTEN BY

🌹 *AMINA UMAR FARUQ* 🌹
             _Kwantagora_

Marubuciyar
*DA SANNU*
*ZUCIYATA CE*
*AFSANA*
*KYAUTAR ALLAH CE*
*ZAUJUN MAJNUN*
*HASKE BAYAN DUHU*
and now
*TAWAKKALI*

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

   *® _PEN: WRITER'S  ASSOCIATION_*

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️        
______________________________________

*~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~*
_____________________________________

https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/

*_Bismilahirrahamaniraheem_*

Typing ✍️

    
  "Hmmm! *Naseer Hamza Ajingin* kenan uban "Asiya da "Aisha yayan "Nafeesa da "Nazeeya...kyawawan idonun shi yazaro cike da tsoron jin yanda ta faɗi sunan shi gatsau, wanda tunda suke da'ita bai taɓajin tafaɗi hakan ba duk koda irin wasan dasukeyi,

hakan ne yasa yaketa kallon ta cike da mamakita yayinda ƙirjinshi ke cigaba da matsanancin bugawa, aranshi yace wayyo ni *Naseer* shikenan najama kaina raini tsakanin na da'ita saboda son zuciya..

"Wani irin murmushi tayi wanda yafi kuka ciwo sannan ta cigaba da faɗin kana mamaki ne nakira asalin sunan ka ko?....kai ya gyaɗa mata tamkar ƙadangare sai sake kallonta yake, sai kace wani sakarar ko kuma irin yaga wata sabuwar halitta can daban wacce ba mutun ba,

yayinda takeyi mashi wani irin mugun ƙwarjini har yanaji tsoro-tsoron ta yana shigar shi, tace tabbas kamanta cewa kai "yayan mata biyu ne kuma uban "mata biyu shiyasa kayima, yar "wani kuma ƙanwar wani fyaɗe saboda itaɗin ba ƙanwar kabace bakuma ba "yarka bace ko?....

  "Kai yake girgiza mata alamar ba hakaba ne cikin wani irin yanayi me cike da tsantsan rauni da tarin nadama, kai ta kawar daga barin kallon shi ƙirjinta yana cigaba da bugawa hawaye naƙokarin zubowa cike da baƙin ciki tace,

to aiba damuwa daɗin abun kama tiddini ne tidan dukkan abinda mutun yayi shima za'ai mashi.

      "Humm! yah *Naseer* kenan ada idan aka tambaye ni nasan mutun me imani da tausayi da amana zance kaine, amma yanzu idan aka tambaye ni nasan mutun mugu marar imani maciyi amana zance "kaine ta kareshe faɗi da kallon shi,

   wanda shima kallonta yake cike da tsananin tsoron jin mugayan kalaman datake faɗa mashi...tace tabbas kai  mugune yah *Naseer* maciyi amana, wanda ya zalunci ƙanwar matarshi yakuma ci amatar "matarshi wacce ta yarda dashi tabashi dukkan yarda da aminci...

"Kai yah *Naseer* yadafe domin kalaman *Nooriya* suna gab da tarwatsa mashi ƙwaƙwalwa,...hawaye ne masu zafi suka zubo mata sharrr! sannan ta cigaba da cewa kuma kasani bawai naƙi faɗin kai ne kayimun fyaɗe saboda na rufa maka asirin ba,

   "A ah naƙi faɗane saboda nakare mutunci "yayata me sona wacce nima nake so da kauna fiye da kaina, kuma akanta" zan'iya salwantar da farinciki na dan ganin nafaranta "mata tareda kare mutuncita koda ko hakan yana nufin rabuwa da rayuwata ne.

TAWAKKALI labarin nooriya da mijin yayarta labarine me taɓa zuciyaWhere stories live. Discover now