part twenty two

71 3 0
                                    

🌹🌿🌹🌿🌹
     🌹🌿🌹🌿
          🌹🌿🌹
               🌹🌿

🌿 *TAWAKKALI 2021*🌿(Labarin nooriya da "mijin yayarta")
_Labarine me taɓa zuciya_

🌹
🌿🌹
🌹🌿🌹
🌿🌹🌿🌹
🌹🌿🌹🌿🌹

Page4️⃣5️⃣to4️⃣6️⃣

WRITTEN BY

🌹 *AMINA UMAR FARUQ* 🌹
         _Kwantagora_
     
Marubuciyar
*DA SANNU*
*ZUCIYATA CE*
*AFSANA*
*KYAUTAR ALLAH CE*
*ZAUJUN MAJNUN*
*HASKE BAYAN DUHU*
and now
*TAWAKKALI*

  _SADAUKARWA_
_Aminiyata NAFEESA HUSSAINI ina roƙon ALLAH jikanta yaimata rahama amin🤲ya rabbi_

Wattpad AminaUmarfaruq
https://my.w.tt/gKC4azRRocb

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

   *® _PEN: WRITER'S  ASSOCIATION_*

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️        
______________________________________

*~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~*
_____________________________________

https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/

*_Bismilahirrahamaniraheem_*

Typing ✍️

"Ko zaka faɗawa kotu sunan ka?..da ƙyar ya iya bude baki yafaɗa, sannan yanuna mashi yah *Naseer* tareda cewa ko kasan wannan?...,

kallon shi yai, da idanun shi dake cike da mugun tsanar yah *Naseer* ɗin wanda shima kallon shi yai, akaro na farko dayaji tsanar barr jamil yaɗarsu aranshi amma  sai bai nuna hakan ba.

  "Asalima kallon tsananin mamaki yake mashi aranshi kuma yana cewa wai shine yai mashi haka?, humm! Kai! ɗan adam kenan BUTULU me manta alkhari alokaci ɗaya sannan yarama alkairin dakai mashi da mugunta.

"Barr yakasai ne yasake jefama barr jamil tambaya dacewa ko yasan wanene yah *Naseer*,? cike da ɓacin rai barr jamil ɗin yace "eh yasan shi, yace ALLAH sarki to ko zaka faɗawa kotu inda kasan shi?...

yace abokin shine ada dariya Barr yakasai yai tare faɗin ALLAH sarki to yanzu Kuma  fa?..yace shi ba abokin sha bane yace assha ya'akai kuma aka daina abotar?..

cike da ɓacin rai yace saboda shi maciyi amana ne mazalunci ne maha'incine, fasiki mazinaci sawa yake ana ɗauko mashi yaran mutane yanai masu  fyaɗen, sannan yasa ajefar dasu atiti saboda shi mugune...

"Tunda yafara faɗin hakan barr yakasai yake faɗin assha! assha!! assha!!! subhanallahi!! subhanallahi!!subhanallahi!!!, yayinda mutane keta kallon shi cike da mamaki domin yai kamar zararre,

shikam yah *Naseer* ido yarintse zuciyarshi tana wani irin matsanancin mugawa, yayinda aranshi kuma yana faɗin ya ALLAH ubangijina kasani a iya tsawon zamana da wannan bawa naka,

da zuciya ɗaya nazauna dashi ban taɓa cutar shi ko cin amanar shiba kona tozarta shi agaban jama'a ba, amma sai gashi, shi yaci amanata yaha'ince ni sannan yanason ya tozartani agaban bainar jama'a, ya ALLAH dan tsarkin mulkin ka kar kabashi nasara akaina alfarma annabin rahama ameen.

"Sannan yabuɗe idon wayan da sukai jajir inda yazubasu akan barr jamil dake tasakin maganganun, wanda kallo ɗaya zakai mashi kagane cewa hassada da baƙin ciki sunyi ma shi katuntu azuciya.

"Yayinda tuni wasu daga cikin mutanan guri iri masu ƙaramar kwakwalwar nan datake da saurin, ɗaukar jitajita har sun ɗauka da gaskene maganganun shi tunda abokin shine, tabbas zayasan komai game dashi.

TAWAKKALI labarin nooriya da mijin yayarta labarine me taɓa zuciyaWhere stories live. Discover now