part twenty eight

92 6 0
                                    

🌹🌿🌹🌿🌹
     🌹🌿🌹🌿
          🌹🌿🌹
              🌹🌿
                   🌹
🌿 *TAWAKKALI*🌿
(Labarin Nooriya da "mijin yayarta")

🌹
🌿🌹
🌹🌿🌹
🌿🌹🌿🌹
🌹🌿🌹🌿🌹

Page 5️⃣8️⃣to5️⃣9️⃣

WRITTEN BY

🌹 *AMINA UMAR FARUQ*🌹
          _Kwantagora_

Marubuciyar
*DA SANNU*
*ZUCIYATA CE*
*AFSANA*
*KYAUTAR ALLAH CE*
*ZAUJUN MAJNUN*
*HASKE BAYAN DUHU*
and now
*TAWAKKALI*

_SADAUKARWA_
*Aminiyata "NAFEESA HUSSAINI Ina roƙon ALLAH yajikanta yaimata rahama amin 🤲 ya rabbi*

Wattpad AminaUmarF
✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
   *_PEN WRITERS  ASSOCIATION_*
✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
__________________________________
*~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~*
____________________________________
https://www.facebook.com/110384724043172/
https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/

Typing✍️

 
  *"Nafi'u* kaima kazama mar hankali ne irin *"Nooriyitu* ko kuma dai ka koma shaye-shayen ne ban saniba eye?...da sauri ya ɗago ya kalle shi tareda cewa a ah abba wlh ban koma ba, kuma ainasan kaima bazaka taɓaso acena komaba ko abba?..

yace tabbas bana fatan hakan, yace to abba wlh na tuni nadaina shaye-shaye kuma har abada bazan sake komawa ba inshallah!, yace to ALLAH yasa hakan yace da yardan ALLAH abba kadai cigaba dataya ni da addu'a, yace inshallah! ai kullum cikin yinta nakeyi to abba na gode ALLAH yasaka da alkairi.

"Abba yace ameen amma meyasa zakazo mun da maganar rashin hankali kamar yanda ita *"Nooriyan* tazo mun dashi eye?.cikin kwantar da murya yace abba ba haka bane to yane eye?..

cikin ladabi yace abba dama naga kukanta" yai yawane shine nace ayyan babu kamshin gaskiya acikin abinda tafaɗa kuwa akan yah *"Naseer* ɗin?..yace hum! *Nafee'u* kenan wani irin kamshin gaskiya uhum?

"Ciki kwantar da kai yace
abba wai naga tunda "itane ta zauna dasu tsawon shekaru, kaga ba mamaki tasan wani halida yake" aikatawa wanda kilan dalilin shine yasa tace" batason shi, kuma batason auren shi saboda hakan ne nace to ayi hakuri afasa auren.

"Wani asirtaccen murmushi abba yai tareda  cewa bayan fitana tafaɗa maku wani aibun "shine?..yace a ah bata faɗi komai ba, yace to kagani kenan batada wani dalili dan haka ka ƙyaleta" so takeyi tamaidani mutumin banza,

da sauri yace kayi hakuri abban banufinta kenan ba yace to kodai menene aure daine baza'a fasa shiba inshallah!, idan "ita batasan abinda takeyi ba to ni nasani idan kuma bata nutsuba tabi abinda nakeso da'ita" ba zan gyara mata zama sosai dan naga batasan halina ba.

"Saboda haka tashi katafi inda zaka cikin kwantar da murya yace  dan ALLAH abba kayi hakuri inshallah zatabi abinda kakeso, kasan akwai ƙuriciya atare da'ita" dole sai anbi da'ita ahankali kai ya gyaɗa tareda cewa hakane shikenan.

"Jeka ALLAH yai maku albarka yashiryar daku akan tafarkin addini musulunci, yace ameen abba mun gode ALLAH yaƙara girma da lafiya da nisan kwana, murmushi Abba yayi tareda girgiza kai cewa humm! ameen sannan yatashi yana murmushi yashiga gida.

********
"Aban garen yah *Naseer* kuwa cikin wani irin matsananci farin ciki yafito da sauri, biliya direba yaje yabuɗe mashi mota tareda cewa sannun da fitowa yallabai da fatan "hajiya tana lafiya?., cikin farin ciki yace yauwa biliya "hajiya tana nan lafiya qalau sannan yashiga motar yaja suka tafi.

TAWAKKALI labarin nooriya da mijin yayarta labarine me taɓa zuciyaWhere stories live. Discover now