🌹🌿🌹🌿🌹
🌿🌹🌿🌹
🌹🌿🌹
🌿🌹
🌹🌿 *TAWAKKALI*
🌿
( _Labarin Nooriya da mijin yayarta_)🌹
🌿🌹
🌹🌿🌹
🌿🌹🌿🌹
🌹🌿🌹🌿🌹Page 8️⃣4️⃣to8️⃣5️⃣
WRITTEN BY
🌹 *AMINA UMAR FARUQ* 🌹
_Kwantagora_Marubuciyar
*DA SANNU*
*ZUCIYATA CE*
*AFSANA*
*KYAUTAR ALLAH CE*
*HASKE BAYAN DUHU*
*ZAUJUN MAJNUN*
and now
*TAWAKKALI*_SADAUKARWA GA_
*Aminiyata NAFEESA HUSSAINI Ina rokon ALLAH yajikanta yaimata rahama amin🤲ya rabbi*Wattpad AminaUmarF
✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
*_PEN: WRITER'S ASSOCIATION ©_*
✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
______________________________________*~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~*
_____________________________________https://mobile.facebook.com/Pen-Writers-Association-100990022185172
✍🏽Typing
_Bismillahirrahamnirraheem_
"Me kace *Nasnoor*?.. kallon su *Najwa* yai wayanda ruka tsaresu da ido yace kuje falon ƙasa ku kalli cartoon kunji?.. cikin sanyi jiki sukace to har zasu fita sai *Najwa* tace momi cikin ki yadaina ciwo?...kallonta tayi cike da tsoro tace "eh sannan suka fita cikeda murna cikin momin su yadaina ciwo,
sannan tamaida kallonta ga yah *Naseer* wanda zuciyarshi tafara halbawa, cikin rawar murya tace *Nasnoor* naji kace inada ciki?..cike da matsanancin faɗuwar gaban da ya riskeshi ciki lokaci kankani, yake kallonta cikin rawar murya dana baki yace "eh! eh!! my *Noor* haka likita "salim yace" kinada ciki na wata ɗaya da sati biyu,...
"Juya mashi baya tayi tareda sakin wani irin kuka wanda yarasa gane kona menene, ma'ana shin nafarin cikin ne ko nabaƙin cikin ne?.. kallonta kawai yakeyi cike da tsoro yayinda yakejin ƙirjinshi yana cigaba da halbawa,
inda take aranshi yake faɗin yah ilahi! me my *Noor* take nufi kardai ace batason cikin dayake tareda?.., idan ko haka ne kuwa akwai matsala domin shikam yanason cikin nan.
"Jiki asanyaye yamatsa kusada ita yatsaya yana cigaba da kallonta cike da faɗuwar gaba, magana yake sanyi amma yakasa domin yarasa ta inda zaya fara dan haka ahankali yakai hannushi yadafa kafaɗarta,
aikam kamar shi takejira tajuyo da sauri tafaɗa ƙirjinshi ta ruƙunƙumeshi tana cigaba da kukan, tareda faɗin *Nasnoor* ashe dama shine! shine!! da gaske *Nasnoor* shine!!! cike da mamaki yace *Noor* shine wa?..
cikin kuka sosai tace shine yakasheta" tabbas shine yakasheta!!, cikin tsananin ƙullewar kai haɗeda tsantsan tsoro da ruɗani yace my *Noor* wa'aka kashe kuma wanene yakasheta?..
"Da sauri taɗago kai ta kallesh fuska sharɓan da hawaye, tace *RABO NE* shine yakashe my sweet *"Nafee* meyasa Rabon nan yanmun haka?.. meyasa bai raba kuba tayanda zan cigaba da ganinta" adoran ƙasa,
sai ya rabani da'ita" tayanda bazan sake ganinta" ba shin meyasa Rabon nan yai mun haka?..taƙarashe tareda ƙwaƙumeshi tana me cigaba da kuka...
"Cikin rawar jiki yasake rungumeta tsantsan tamkar zaya maidata cikin jikinshi, sannan yace saboda ALLAH ne me ikon zartar da komai ba RABO ba Dan haka my *Noor* kinyi saɓo so kiyi gaggawar cewa astagfillah! da sauri tace astagfillah ALLAH natuba,

YOU ARE READING
TAWAKKALI labarin nooriya da mijin yayarta labarine me taɓa zuciya
Historical FictionTAWAKKALI Labarin nooriya da mijin Labari ne me taɓa zuciya