part eighteen

82 2 0
                                    

🌹🌿🌹🌿🌹
     🌹🌿🌹🌿
          🌹🌿🌹
               🌹🌿

🌿 *TAWAKKALI 2021*🌿(Labarin nooriya da "mijin yayarta")
_Labarine me taɓa zuciya_

🌹
🌿🌹
🌹🌿🌹
🌿🌹🌿🌹
🌹🌿🌹🌿🌹

Page3️⃣7️⃣to3️⃣8️⃣

WRITTEN BY

🌹 *AMINA UMAR FARUQ* 🌹
         _Kwantagora_
     
Marubuciyar
*DA SANNU*
*ZUCIYATA CE*
*AFSANA*
*KYAUTAR ALLAH CE*
*ZAUJUN MAJNUN*
*HASKE BAYAN DUHU*
and now
*TAWAKKALI*

  _SADAUKARWA_
_Aminiyata NAFEESA HUSSAINI ina roƙon ALLAH jikanta yaimata rahama amin🤲ya rabbi_

Wattpad AminaUmarfaruq
https://my.w.tt/gKC4azRRocb

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

   *® _PEN: WRITER'S  ASSOCIATION_*

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️        
______________________________________

*~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~*
_____________________________________

https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/

*_Bismilahirrahamaniraheem_*

Typing ✍️

"Me! maganin ciwon kansa ta jiniki ke" sha my wiffy?..yai mata tambayar jikinsa yana wani irin mugun rawa, yayinda yake ware idon shin akanta tamkar zasu faɗo ƙasa...

saboda mugun tsorata dayai dagani maganin itama kallonshi take da idonta datuni suka cika da hawaye, zuciyarta na cigaba da matsanancin bugawa fiyeda misali tana me girgiza mashi kai, wanda yarasa me take nufi "eh ko a ah!.

"Cikin mugun tashin hakali yasake ɗaukar wani maganin yana dubawa hannun shi kuwa sai rawa yake, wanda hakan zaya nuna maka yashiga tsantsan ruɗani da tashin hakali,

haka yaita ɗaukar magungunan ɗaya bayan ɗaya yana dubawa jikinshi yana rawa, yayinda taketa binshi da kallo hawaye nata malala afuskar ta, saida yakai na karshe sannan yazauna daɓas akasa.

"Yana kallonta da idanun nan nashi me bata tsoro aduk lokacin da yafito cikakken namijin shi. sai kuma ya lumshe ido cikin wani irin mugun yanayi me cike da tashin hakali da firgici,

yafurta my wify pls kiyi gaggawar tadani daga wannan mugun mafarkin da nakeyi marar ɗadi, wanda bana fatan na cigaba dayin shin arayuwata so yi sauri ki tadani kinji? yakarashe faɗe tare da miƙa mata ahannu nufinshi ta taɓashi...

"Kai kawai take girgizawa tareda kallon shi tana wani irin kuka maras sauti, jin shurun bata taɓashin bane yasashi buɗe idon ahankali yana kallonta da idanun shi da tuni sukai ja, cikin rawar murya yace my wify ba mafarki nakeyi bane?..

da sauri ta ɗaga mashi kai alamar eh, yace kenan da gaske kece ke ɗauke da blood cancer? kai take gyaɗa mashi alamar eh! eh!! eh!!!, cikin sanyi murya yafurta my wify tun tsawon wani lokaci kike ɗauke da wannan ciwo bansaniba?,cikin rawar murya tace shekaru biyu abban *"Najwa*.

"Wani irin bugawa zuciyar shi tasakeyi yayinda yazaro idanun shi da suka cikada hawaye, cike da tsananin tsoro da tashin hakali yace shekaru biyu fa kikace wify?..ta gyaɗa kai alamar eh cike da wani irin yanayi
yace innalillahiwa'inna'ilaihirraju'um! haba my wify meyasa baki taɓa faɗa mun ba?..

cikin rawar murya tace kayi hakuri abban *"Najwa* banasan kashiga tashin hankali ne shiyasa banfaɗa makaba.

"Cike da mugun tashin hakali yafurta wayyo ALLAH na ni *Naseer*, nikam wani irin mijine da yake zaune damace tsawon shakaru amma ban taɓa kulada cewa tana ɗauke da ciwon kansar jini ba?.

TAWAKKALI labarin nooriya da mijin yayarta labarine me taɓa zuciyaWhere stories live. Discover now