twenty six

101 7 0
                                    

🌹🌿🌹🌿🌹
     🌹🌿🌹🌿
          🌹🌿🌹
              🌹🌿
                   🌹
🌿 *TAWAKKALI*🌿
(Labarin Nooriya da "mijin yayarta")

🌹
🌿🌹
🌹🌿🌹
🌿🌹🌿🌹
🌹🌿🌹🌿🌹

Page 5️⃣4️⃣to5️⃣5️⃣

WRITTEN BY

🌹 *AMINA UMAR FARUQ*🌹
          _Kwantagora_

Marubuciyar
*DA SANNU*
*ZUCIYATA CE*
*AFSANA*
*KYAUTAR ALLAH CE*
*ZAUJUN MAJNUN*
*HASKE BAYAN DUHU*
and
*TAWAKKALI*

_SADAUKARWA_
*Aminiyata NAFEESA HUSSAINI Ina roƙon ALLAH yajikanta yaimata rahama amin 🤲 ya rabbi*

Wattpad AminaUmarF
✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
   *_PEN WRITERS  ASSOCIATION_*
✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
__________________________________
*~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~*
____________________________________
https://www.facebook.com/110384724043172/
https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/

Typing✍️

   "Sai kuma yai kataccan murmushi tareda cewa ALLAH sarki  Alh *Naseer* ai tun bayan rasuwar "matarka  *Nafeesatu*, nayi tunani hakan yakasance tunda hakan ya halatta to sai kuma naga baka buƙaci kasancewar hakan ba.

"Dan haka sai kawai nakawar da abin araina, tunda ba mamaki nayi maka maganar yazamo babu tsarin hakan acikin zuciyarka,

cikin girmamawa yace ayya Abba bakomai aida kayin mun maganar ma tuntuni wlh zan amince kwarai da gaske, domin haɗa zuri'a dakai abune me matuƙar kyau kuma ALLAH bai haramta ba aure tsakanin da *Nooriya* ba.

"Sannan abba ko bakomai auran *"Nooriya* shine abu mafi dacewa dani tunda tasanni tasan halina tasan yanda zata zauna dani, sannan zata kulada "yaranta su *Najwa* sosai.

"Saɓanin "wacce zanje na auro bansan halintaba batasan nawaba, muzo munasa mun matsala gurin zaman takewar auran, wanda kuma kaga hakan bai daceba ko kuma tadinga takurawa su *Nawwal* tana takura masu nikuma abba wlh bazan taɓa amita da hakan ba.

"Murmushi abban yai cike da jin daɗi da gamsuwa da bayanin shi yace haka ne ko dama na tabbatar, idan nayi maka maganar cewa inaso hakan yakasance nasan bazakai mun musuba, to amma tunda baka buƙaci hakan dakanka ba sai na kyaleka domin kafaɗa da bakinka yafi kima fiyeda ninai maka maganar.

sannan maganar takurawa yara tabbas  wani matan haka nan suke gayi ga ya'yan dabasu haifaba, saidai ALLAH yashirya su sudaina hakan amma ai ɗana kowane kai zaya iya kasancewar wanda ka Haifa bashine zaya kulada kaiba sai wanda baka haifaba, gyaɗa kai yah *Naseer* yayi tareda cewa haka ne abba ALLAH ya ganar dasu yace ameen.

"Sannan abban ya cigaba da cewa tunda yanzu ka buƙaci hakan da kanka shikenan ba damuwa ALLAH yatabbatar da alkhairi, ni Alh Sa'ad karaye nabaka auren "yata *Nooriyatu* akaro na biyu kamar yanda nabaka "yar uwanta,

mutuwace tarabaku to inarokon itama wannan mutuwace zata rabaku, saboda haka duk lokacin da kashirya kakeso aɗaura auran saika zo, kayi mun magana abinda nake buƙata kawai dakai shine sadaki sai kuma waliyyainka kamar yanda shari'a tace".

"Cike da jin daɗi yace to abba inshallah zan turo su" na gode sosai, ALLAH yaƙara lafiya da girma da ɗaukaka yakuma jakwana yace ameen ALLAH yayi albarka nan suka ɗan taɓa fira kamar yanda sukeyi idan yah *Naseer* ɗin yazo,

sannan yai masu sallama har zaya tafi sai abba yace ah! baka tambayi "matan nawa ba?, murmushi yai cike da jin nauyi yace abba ai tunda bangansu" ba nasan suna can gidan,

TAWAKKALI labarin nooriya da mijin yayarta labarine me taɓa zuciyaWhere stories live. Discover now