*IN THE NAME OF ALLAH* ✍🏻
_______________________________MASARAUTAR JAMAL
001_002
*A kishingide yake akwance kan wani filo mai abin burgewa da sha'awa inda yake cin apple kamar baya son ci haka yake taunata,
inda agefensa wata jakadiya nagani zaune sai fadawan da suke masa filfita,
inda wannan jakadiya naji tace ƴallabai akwai bakuwa datake so ta ganka awaje amma tace idan anmata izinin shigowa zata iya shigowa.
Nan yayi wani ɗan jim kaɗan sannan chan naji yace da ita ace tashigo. Jakadiya ce ta naga ta meƙe tafice daga farfajiyar gurin da yarima yake,
inda kai tsaye tayi wajen da wannan budurwa take inda tace ance kishiga nan tabi bayan jakadiya har suka isa inda yarima yake. Da zuwanta naga yarima ya firgita ya meƙe tsaye yana nunata yana cewa kece dama meya kawoki gidanmu eh ?
Irin tambayar dayake mata ne yasa fadawan wajen suka fara kallon² tsakaninsu alamun irin suna mamakin wannan abu da suke gani suna tunanin ko yarima yana tare ne da yammatan banza ne awajen dayafita ko me?
Domin kuwa shigar da ke jikinta ba shiga bace ta ya'yan musulmai ba domin kuwa wata shegiyar riga da wando ne ajikinta wanda babu abin da ya rufe najikinta komai ana gani.
Nan hankalinsa ya dawo kan fadawan dasuka masa tsaye akai yace dasu suje zai neme su an jima inda kowanne a cikinsu ya fara bin hanyar fita awajen.....
Juyawa yayi gare ta yace falmata meya kawoki gidanmu bayan nafaɗa maki koda wasa kada kisa ke kizo gidanmu ko ki manta ne??
Kaɗa kai tayi alamar a'a ban manta ba saboda kuwa koda yaushe da tunaninka nake kwana nake tashi meyasa kasan bazaka aureni ba kamin alkawarin aure ?
Kamin hallaci kenan Jamal??? Meyasa kamin haka ne, meyasa, meyasa??????
😭😭😭😭😭 Wannan wani irin hukunci ne haka koda wa ka ganni ai Kai mai tsayawa ne ka tambayi meyafaru amma kawai kadauke min kadaina shiga rayuwata mena maka ne wai haka?
Please am abeg you Jamal come back to me I need your assistance, please Wallahi I can't live without you inda Anan take kuka ya kwace mata dan ita kanta bata san tafara kukan ba,
inda shikuma gogan naku ko ajikinsa domin ba kowani kuka ne mace ke yi ba ya nakasa da ƙasa ba, inda nan ya nutsu yamaido da hankalinsa kanta nan ya fara cewa is okay falmata ya isa haka kinsan dai bana son kuka ko?
Nan ta ɗaga masa kai alamar eh nasani, nan yace good girl but abinda nakeso kifahimta shine anan yanzu ke idan nace zan aureki zaki yarda ne bayan nagama sanin wacece ke kuma ba akaina kika fara wannan halaye ba bare kice ko nine na bata maki tarbiyya ba ko?
Nan ta ɗago da kanta tana kallonsa dayake ɗan i don't care ne ko ajikinsa da irin kallon datake masa,
nan ya cigaba da cewa falmata kiyi hakuri dan Ni kam bazan iya auren macen dabata san kanta ba bare tarike mutuncin wani to dan haka ki rungumi sorry kinemi wani can dai-dai dake ki aura domin kuwa Ni yanzu nafi karfinki gaskiya.
Wani baƙin ciki ne ya tahomata jitake kamar tatashi tai ta dukansa har ta huce abinda ke ranta,
nan tayi wani murmushin bakin ciki inda ta tako tazo gabansa tace naji bazaka aure Ni ba amma ka rubuta wannan ka ajje komai daren dadewa wallahi sai nasaka kuka da idanuwanka kuma sai na hanaka kwanciyar hankali ga duk wacce zaka aura domin kuwa sai na fallasa ka agurinta na nuna mata kai ba namijin arziki bane da za'a iya aura ba har anunawa duniya ace wannan shine uban ƴaƴa nane domin kuwa dole wata rana sai ango ranta masu domin kuwa kai ba mutumin kirki ba ne, kaje wajen waccan kaje wajen wan ...... kafin ta karasa taji
yadauketa da wani Irin mari akan fuskarta kafin ta ɗago yakara mata wani inda ya fara mata warning akan takiyaye bakinta akan shi idan bahaka ba wallahi zakiji ajikinki dan kafin kibar nan wallahi zan iya karyaki a banza,
inda wannan maganar tasa ta sata sakin wani irin kuka mai bakin ciki cikin kukan tace naji kace haka amma wallahi wulakantanin dakai bakayi abanza ba domin kuwa sai narama kuma zakai nadama wallahi. Kafin ta juya tabar wajen yayi wata iriyar banzar dariya yace wai nadama a ina akeyinta? Ko kinmanta ke kika kawo min kanki?
To Bara na sanar dake wani abu da baki sani ba wallahi idan kafarki tasa ke shigowa gidan nan keda ganin haske arayuwarki har abada banza karamar karuwa ke iskancin naƙi ma karami ne wallahi this is the last warning falmata ko amafarki kada kisake tunani bare kiyi tunanin ramuwar gayya akaina wannan shine batu, karki manta wani abu fa Nipa ina zaune kika kawo min kanki akan nayi amfani dake koda ba ko sisi, kintuna wannan lokacin ??
(Matsalarmu kenan yanzu abinda yake faruwa kenan kije kizubar da mutuncinki awajen wani katon na daban wanda baki san shi ba baki san Asalinsa ba baki san daga wani ciwo tatashi ko yake kokarin kamasa ko yana dashi duk baki sani ba, dan son abin duniya kije kibayar dankanki har ya dinga maki alkawarin karya akan zai aureki hmmmmm shi wani irin mahaukaci ne dazai san yadda kike kuma yazo yace zaki zama uwar ya'yansa kinsan daga jin wannan maganar karyar banza ce to dan haka yar uwa kikiyaye domin kuwa yanzu maza basu da tabbass alalataki abarki da ciwo ajiki koda kuwa ba a miki ciki ba aee dai ancuceki. Allah yakara kiyaye mu baki daya) Amin.
'''Please share and comments
Always you are in my mind fans and family kudai kucigaba da nuna min kauna'''