55_56

58 10 0
                                    

Bissmillahirrahamanir

Ina maki addu'ar samun nasara a gareki sister Fatima Ibrahim Aminu Allah Ubangiji yabaki sa'ar abinda kikaje nema Amin. Tare da sauran yan uwa musulmai.

*****

Ɓangaren yarima kuwa babu abinda ya sauya daga garesa domin kuwa kullum yana cikin damuwa da takaici wanda bai san na menene ba.
Azkar ɗinsa yadakko yafara karantawa, yana cikin haka ne falmata tashigo kanta tsaye batare da wata sallama ba ta faɗa kansa inda nan tafara shagwaba
Haba yarimanah yakake ta wani shareni kamar ba matarka ba meyasa?? Cikin sigar shagwaba take maganar.

Kallonta yajuyo yanayi nan ya fara magana cikin faɗa faɗa
Inda ya fara nuna mata hanyar fita daga inda yake alamun tabar masa daƙinsa..

Kallonsa tayi irin kallon mamaki tana tunanin me mutumin nan yake nufi ne?

Jamal takira sunansa cikin ɓacin rai itama, wai mekake takama dashi ne dakake min duk abinda kaga dama dan kaga ina auranka kuma ina sonka shine kake min haka??

To kidaina sona sai me?? Ummm nace sai me?? Kifitar min a daki yanzun nan nabaki seconds 5, kafin na karya maki kafa, banza ballagaza da baki san ciwon kanki ba, Ni Banda ƙaddara ma mezanyi dake Ni wallahi Bansan ya akayi na aureki bama.
Ina zamana lafiya da matata da yarana amma zuwanki duk farin cikinah ya watse, silarki da shedancinki duk na rasa wadannan abubuwan masu mahimmanci arayuwata, to wallahi Bara nafaɗa maki daga yau daga rana irin ta yau kada nasake ganin kafarki a dakina har sai kin dawo min da iyalina saboda kuwa ko nayi rantsuwa bazanyi kaffara ba da sa hannun ki abatan gimbiyata.
Yana gama fadar haka ya mike ya shige bedroom nasa yabarta nan tsaye tana kuka.

"Kuka take iya karfinta tana buga masa kofa tana rantsuwa akan....wallahi yarima banida masaniya akan ɓatan matarka da yaranka wallahi Allah......kuka ne yaci karfinta sosai inda nan ta sulale taci gaba dayin abinta kamar babu gobe.

*****
"Fulani Maryamu!!!! Na'am mama kinaso ki gama da duniya lafiya???
Eh mama...
Yawwa yarinyar kirki to ina so ki manta da komai da yafaru dake da mijinki ki koma ɗakinki kirike yaranki saboda kuwa mijinki yana sonku kuma ba sakinki yayi ba, koh???
Eh mama
To abinda nakeso dake shine kiyi hakuri ita kishiya ba wata aba bace da take ba mutum tsoro ba, amma dole tana da tsoro tunda baka san wace iri bace za akawo maka ba.

Amma nidai ina so a matsayina na uwa da nake a wajenki dan Allah narokeki kiyi hakuri kikoma ɗakinki ki rungumi mijinki da yaranki.

Hawaye ne yafara zubowa daga cikin idanuwanta ...inda tafara magana kamar haka... Mama shikenan Insha Allah nadauki maganarki kamar yadda kikace hakan xanyi naji zankoma amma ina so kimin hakuri zuwa Jalila su gama wannan makarantar dan kar naciresu kuma karatunsu ya tarwatse.
Dan Allah mama kimin wannan adalcin.

To Bakomai Maryamu baki daɗi sosai Allah Ubangiji yamaki albarka.

Amin mama Nagode, Allah saka da alkairi Nagode sosai da kulawarku garemu.

Haba haba kekuwa Maryam yadda nafisah da salma da safiya suke awajena haka nadaukeku duk daya ne, kenan idan nawa nafisah abu ta gode min kema zakiyi haka kenan?
Murmushi tayi sannan takuma godiya ta tashi takoma bangarenta.

****
Falmata na hanga rike da waya a hannunta, tana ta magana wadda Bansan metake cewa ba amma dai abu ɗaya na iya fahimta a maganarta itace datake cewa yanzu jiddo ya za'ayi kinsan malamin fa yace idan anfara samun matsala mukoma ko?? To yanzu gashi yarima ya kafe akan sai na maido masa da matarsa dole,... Duk da Bansan daga wancan barin me ake cewa ba, amma amsar datake bayarwa yana nuni da amincewar akoma kenan.
Sun gama shirinsu tsaff akan tafiya gun bokansu, wanda suka saka rana.

Bayan sati ɗaya
________

Masarautar JamalWhere stories live. Discover now