MASARAUTAR JAMAL
35_36Wanka yayi ya shirya yana shirin fita sai yaji kira yashigo wayarsa inda nan da nan ya maida hankalinsa kan wayar ganin bakuwar number ne yasa bai daga ba,
cigaba akayi da kiran wayar wanda silar haka ne har yajanyo hankali Maryam,Yarimanah kamar wayarka naga ana kira ko?
Eh kawai manta dasu ina tunanin masu neman taimako ne.
Okay...Haka yagama shirinsa tsaff yawuce inda kafin yafita sai da yatsaya ya sumbaceta sosai...
Kewayen mahaifiyarsa ya nufa inda yake gaisheta.
Shigar sa kenan aka kuma kiransa da wannan number, nan yaji yana kwadayin daga kiran inda yana karasawa cikin parlor yaji wata murya mai sanyi da dadi ta bugi cikin kunnensa
Inda nan ya fara neman hankalinsa yarasa kawai sai ya tsinci kansa da son jin Muryar kawai.Yarima Jamal dafatan kana cikin lafiya?
Lafiya lau!
Uhmm nasan kana so kasan wacece ko?
Eh kam saboda naga sabuwar number ne, kuma sai ya cije inda muryarsa tafara rawa kamar marar gaskiya nan kuwa ba haka bane.
sunana falmatah Umar kabeer
Future wife naka da muke fataWani irin murmushi naga yanayi wanda Ni kaina sai dana rasa na menene??
Yanzu kina ina falmatanah?
Nayi kewarki yadda bakya tunani bana iya bacci idan har banyi tunaninki ba falmatah meyasa kika gujeni?
Kinsan kuwa yadda nakejinki a cikin raina?"hmm tace
Tacigaba da masa kala ai wanda suke dauke hankalin mai sauraro....
Wanda silar haka ne har yamanta a ina yake.nanfa tacigaba da cewa yarimanah ina so naganka Nipa nafika matsuwar na ganmu tare muna rayuwa mai cike da jin dadi.....
Saurin cewa yayi Insha Allah anjima zanzo gidanku kishirya min kanki..
"Okay " bye
"Take care"
Meƙewa yayi yashige can fadar umman tashi mai baban daki, uwar kowa..
Bayin dake kanta ne suna mata filfita suka fara gaishe shi inda yake amsa masu cikin sakin fuska .
Umma ina kwana?
"Lafiya kau yarima, ya iyali?
Alhamdulillah suna gaisheki.
To Masha Allah Nagode.Sai ina kuma daga nan?
Zamuje wajen aiki ne umma..
Okay to Allah taimaka, Allah yayi maka albarka.Amin umma Nagode...
Tashi yayi tafita inda direct yanufi fadar mahaifinsa inda yake suka gaisa a ggaggauceNan yafito ya nufi wajen parking space inda yadauki mota mai tambarin sarautar gidan yanufi office.......
Gidansu falmatah yaje bayan tatashi a aiki, dama kuma tasan da zuwansa
Inda yana zuwa direct yashiga batare da wani shamaki ba...
Parlor ne na alfarma wanda tsayawa fadin yadda parlon yake bai zaiyi a kawai kuyi imagination yadda gidan outside yake😝😃
Sallama yayi tare da zama inda yana zama yaji wani ƙamshi na bugun hancinsa ji yake duk duniya babu kamshin dayake so sai wannan...
Topa.... tirkashi yadai yarima Jamal kodai kudirin falmatah ya fara aiki ne????
Ganinta yayi agabansa tana tamasa rangwada da kwarkwasa tajuya nan tajuya can har hankalinsa ya fara neman gushewa...
Inda tana ganin yanayinsa sai tayi saurin komawa kusa dashi ta zauna
Inda nan kamshin tacigaba da rikita sa ga wata irin kaunar ta dayake ji ga kuma wata irin sha'awa dake neman tasar masa.Ina yini yarimanah?
Muryarta ya tsinkaya
Cikin rawar murya yafara cewa...
Lafiya farin cikina.Wani shegen daɗi yaji ya harbeta nan da nan tafara jin sanyi aranta
Inda tace to ai sai ka sakko kaci abinci ko?Saboda nasan akwai yunwa tare dakai, kaje office kasha wahala.
Wallahi kuwa kamar kinsani kam dan akwai yunwa tare dani, Yakamata kiciyar da masoyinki.
Wani sanyi taji acikin ranta
Nan tafara zuba masa gubar abincin da ta haɗa magani dashiCi yayi yakoshi inda har yake neman kari....
Hira sukayi sosai ta masoyan asali wanda kafin yabar gidan sai da yamata alkawarin aure.........Topa yarima yadai?
#team yarima
#team Fulani Maryam
#team falmatahAKafta🏃🏃🏃🏃🏃🏃