Tadambo writters association
***
"Jamal ne a falon ummansa tare da jalil a kan cinyarsa yana ta wasa da wuyan rigarsa ya hau can ya koma can haka ya dinga yi har barci ya daukesa anan.
Umma ce ta kalli Jamal inda tafara masa magana ...
Yarima jiya da yau kwatakwata banga falmata ba ina taje ne??
Eh umma tace min zataje wani kauye wajen wata mata da tataba taimakon ta acan baya lokacin tana zaman gida.
To to nagane amma kasan anyi alkawari dakai akan kadaina barinta tana tafiya batare da wani daga cikin gidan nan ba?
A'a umma ban manta ba wannan dinma dalilin da yasa nabarta shine dan halliru ne zai Kaita shiya sa nabarta.
To duk da haka dai kada kamanta security da akace asa akanta domin yanzu haka akwai wasu layoyi da jakadiya ta cirosu a wani rami anbinnesu da sunanka da na mahaifinka da matarka a ciki,
Kuma Bama zargin kowa itace ta binne saboda kuwa duk fadar nan Fulani bata da wani abokin faɗa bare kuma ace wanda ta rai na asanina dai babu gaskiya.Amma ance mutum tara yake bai cika goma ba, Allah dai ya kyauta yakare mu.
Amin yace tare da cigaba da cewa...
Umma Ni fa ban dake wallahi da tuni narabu da wannan yarinyar saboda shigowar ta rayuwata ne ta maidani haka amma kiyi hakuri da kalamina.A'a baza ayi haka ba jamalu kayi hakuri komai yakusa zuwa karshe mubarta da halinta indai aikin asiri ne babu inda yake zuwa, koda ma yaje inda akeso baya dadewa yake lalacewa to dan haka ina mai kara baka hakuri kadaure ka kara wani akan wanda kake dashi da Insha Allah asirinsu zai tonu.
Allah yayarda umma nah Nagode sosai. Allah Ubangiji yasa ka maki da gidan aljanna,
Amin yarima kaima ina maka addu'ar fatan alkairi a duk inda kake Allah Ubangiji yakareka tare da iyalanka.
Amin.
Sallama sukayi yatashi yabar mata falon ....
Wajen boka
Falmata nagani kwance tayi reran haihuwar uwarta inda wannan shedanin yake lalata da ita (innalillahi wa'inna ilahir raju'un).
A dinga abu kamar baza a mutu ba, Allah kamana tsari da irin wannan mutanen garin nema duniya kirasa lahirarki ...Sai da suka gama lalatarsu sannan suka fito yabata abinda yabata sannan tatafi....
Drivern daya kawota ne takira a waya yadawo yadauketa
To Hajiya abinda naji yafada kenan.
Kashe wayar ta tayi.
nan tafara tunanin to yanzu idan wannan mutumin yana da ciwo yakenan?
Shikenan yacuci rayuwarta?
Wata irin faduwar gaba taji...Tana cikin yanayin tunanin ne taji horn din motar alamun hallirun yakaraso
Tashi tayi tafita,inda yayi parking tanufa nan tashige mota abinta suka kama hanyar fita daga kauyen.....