11_12

147 16 0
                                    

_Typing_

        TADAMBO WRITER'S ASSOCIATION

        Tsintsiya madaurinki ɗaya
     ___________________________________

https://facebook.com/groups/195183905712588/

*MASARAUTAR JAMAL*

1️⃣1️⃣➡️1️⃣2️⃣

"Jirgin karfe *6:00am* tahau,
inda jirgi ya haura sama cikin gajimare yake ta hazo yashigo kasar ta ta Nigeria,
inda tana sauka taji wata iska mai daɗin gaske ta bugar mata hanci.

"Dirarta kenan ta hango daddynta yana mata welcoming nan ta ruga tayi saurin hugging nasa inda nan tafara cewa daddynah nayi missing naka sosai. Nan daddyn yafara shafa kanta yana cewa nima nayi missed babynah, murmushi sukayi baki dayansu.

Inda driver ya karbi jakar hannunta ya wuce da ita cikin mota ya ajje.

*Dashigar su gida ta ruga da gudu tana ihu tana kiran mummy! mummy !! Nadawo, nan sukayi kicibis ita da mummyn kafin su rungumi juna.

""Mummy nah bakya kewata ne? Ummm mummy?,  haba wane mutum yace baya kewarki Ni na isa namanta shalelena? Kenan zan iya manta kaina, dariya tayi tace yawwa ko kefa mummy ai nadauka ina tafiya kika yayeni.

*Abinci ne aka jera su akan dinning table inda masu aiki suke ta hidimar kawowa.

"Nanny ce tazo tace Hajiya mungama shirya komai, nan mummy tace okay sannu but inaso kikiramin lami kice tazo yanzu yanzu, tohm tace tawuce abinta.

"Mummy ce takalli falmata tace mu baby muje kici abinci ko? Nan ta turo baki zata fara halinnata na son kin cin abinci, mummy banyi wanka ba fa.

"Lami ce tashigo ta katse masu zancen da suke yi, inda tace Hajiya ance kina kirana? gani sai tace yawwa lami dama so nake kije kikara share dakin baby tunda nasan yanzu yakuma daukar datti, tunda tun safe da kuka share baku sake sharewa ba ko?

To Hajiya angama...

      ********
"Bayan wata ɗaya

Falmata nagani cikin wasu arnan kaya wanda gaba ɗaya suffar jikinta ana gani, ita awajenta wannan ba wani abu bane dan tafita a haka.

Falo tafito tana kwala kiran ''Mummy "Mummy

"Inda ake amsa mata naga tanufi  wajen, gaisheta tayi mummy ina kwana? Lapiya lau baby, ina zaki haka kuma da safen nan?

" Wallahi mummy zanje wajen kawata ne queen zamuyi magana akan shirin bikinta.

Adawo lafiya kawai mummy tace mata tawuce.

Filin ajje motoci ta nufa inda ta dauki wata mota mai kyan gaske wadda ta amsa sunan ta mota, ta hau tafita abinta.

* Sokoto road tanufa!
Inda tana tukinta tanajin waqarta a hankali tanaji tana bin waqar. Ahaka har ta isa inda takeso taje.

Dashigarta surrounding ɗin gidan tafara ƙoƙarin ciro wayarta takira queen tasanar Mata tashigo.

Sai wani mai gadi ne yazo yatsaya yana magana amma tayi burus dashi, irin bata san da rayuwar sa awajen ba haka tanuna. To dama tun shigowar ta queen taganta tasaman tagari ɗakinta kafin ta sauka nan tabawa iliya mai gadi izinin yace da wannan matar tashigo ciki, to wannan shine dalilin zuwa gurin ta da yayi saboda dama ba yau tasaba yimusu hakan ba.
Iliya ne yace dama Hajiya ce tace nasanar dake kishiga ciki.
Wucewa tayi abinta kamar bata san aikosa akayi ba.

( Hmmmm rayuwar duniya bakomai bace masu ɗagawa da jiji dakai wallahi kudaina kukiyayi gabanku saboda wata rana. Allah sa mudace, Amin).

______ Shiga falo sukayi suna shewa yaushe rabon da aga juna har anmata, nan queen tafara kawo mata kayan tabawa inda tana gama sha ta turasu gefe, nan suka fara hirar yaushe gamo ahaka hirar ta gangaro har tazo kan maganar yarima Jamal, inda nan take gaban falmata yafadi saboda ko me zai mata bazata taba mantawa dashi ba domin kuwa har yanzu tanajin sonsa aranta.

"Anan ne taji maganar family nasa sunce yafito da matar aure. Suna cikin hirar ne kiran ra'uf

Masarautar JamalWhere stories live. Discover now