Kullu nafsin zaikatul maut Allah Ubangiji yamaki rahama baba gaje #emir daura.
****
Sai da ya gama abinda zaiyi da ita sannan ya ɗagata yakwashi abinda yakeso sannan suka fito.
Wasu irin kwalabe ya ciro acikin wani dan ƙoƙo ya mika mata, bayanin yadda zatayi amfani dashi yamata, sannan suka tashi suka fita hanya suka kama suna tafiya mai tsayin gaske har suka isa wani guri wanda babu kowa a wajen sai tsuntsaye daba sufi a irga ba, maganin nan taciro acikin jagarta tafara shafawa a hannunta tana kiran sunan Maryam tana ta surutai kamar yadda bokanta yafada mata haka tayi sannan suka kama hanyar gida....___Tana bacci taji kamar anfizgeta tashi tayi zaune babu abinda take muradin gani yanzu sai mijinta abin kaunarta haka kawai ta tsinci kanta da tunaninsa yau tarasa meya ke faruwa da ita ne??
Fitowa tayi daga ɗakinta kai tsaye dakin mamma ta wuce tana shiga gaisheta tayi sannan tafara mata maganaummm mama dama cewa nayi tunda yanzu su Jalal sun samu Hutu ina so zamuje gida da su dan jikina yana bani wani abu kamar yafaru amma kuma Ni bansaniba.
To Masha Maryamu Alhamdulillah tunda yanzu da kanki kika ce kina son komawa gida Kinga kuwa bazamu hanaki ba to Masha Allah, yanzu yaushe kike so kutafi?
Sunkuyar da kanta Maryam tayi domin kunyar mama ce takamata domin kuwa ta dauki mama tamkar uwar da ta haifeta saboda ta mata komai na rayuwa yanzu tunda har ta rike mata yara kuma ta daukesu matsayin jikokin ta kamar wadda ta haifi uwarsu.
Kinyi shiru Fulani?
Ahahaaa mama duk ranar dakika ce ranar zan jira kawai.
To shikenan kishirya ko zuwa gobe ne sai muje can jigawar ko?? Amma kafin nan kishirya anjima akwai mai lalle da zatazo sai tamaki keda yar lelena (jalilah),
Murmushi tayi tace Toh mama Nagode Allah kara girma da arziki.Amin Amin Fulani..
****
Sun shirya tsafff abinsu kamar wasu larabawa idan kagansu, jikin mota suka nufa kai tsaye wanda mama ta shige motarta shikuma uncle anas yashiga ta honourable inda nafisah da Fulani suke ciki ta mama kuwa aunty salma ce da Safiyyah acikin ta inda suka kama hanyar fita daga farfajiyar gidan...***
Hanya suke bi sosai suna tafiya, inda har jalilah tafara bacci, Jalil ne ya ɗago kai ya kalli mahaifiyarsa yace Ammi ina zamuje wai ??Gida zamuje Jalil wajen Ummu..
Ammi wacece haka kuma??
Saurin kallonsa tayi hawaye na kokarin taho mata ta boyesu,
Ummu Maman yarima ce ai kataɓa ganin hoton ta ko tare da kai ?? Ko kamanta??
A'a Ammi ban manta ba, amma meyasa bata taɓa zuwa wajenki ba ta ganmu sai mama ??
Tana zuwa mana Jalil lokacin da take zuwa ku kuna makaranta ko kuna bacci sai tace abarku kada a a tasheku.
To amma Ammi meyasa shi yariman dakikace bamu sanshi ba??.
yarima shine babanka (biological), to shi yana kirana kasar waje karatu baya samun lokacin kansa bare har yazo yaganku amma kullum kuna cikin ransa.