21_22

108 13 0
                                    

_Typing_

              TADAMBO WRITER'S ASSOCIATION

        Tsintsiya madaurinki ɗaya
___________________________________

https://facebook.com/groups/195183905712588/

*MASARAUTAR JAMAL*

# ~CONTINUE~

🅿️2️⃣1➡️2️⃣2

Saurin sakin kyautukan da a kamata tafara yi inda nan taji wani irin jiri na ɗaukarta, nan tafada wata duniyar tunani inda tafara tunanin to taya tazama matarsa ? Bayan ita baffan tah yace bazai mata aure ba har sai ta girma tazama kamar bishiyar dabino...lol😂.

"Riƙo hannunta da yayi ne yasa ta saurin dawowa daga duniyar tunanin da ta tafi, nan ya fara janta inda yayi saurin ɗaukarta chanak yabar wajen da ita dan gani yake idan yace tayi tafiya to babu makawa wani zai kallar masa mata.

Bai direta ko'ina ba sai acikin mota inda nan ya fara cewa :- dama dan a tabamaki jiki akayi taron? To wallahi mairama daga yau kinbar makarantar nan tunda dai Ni nake auren ki ba wani ba.

Nan gabanta yafaɗi inda tafara zubar da hawaye tana bashi hakuri akan yabarta tacigaba saura wata 2 duka su gama yayi hakuri dan Allah, inda ko kallo bata ishe shiba yaja motarsa yabar area school ɗin.....

Inda taro yawatse batare da Maryam Jamal takarbi gifts dinta ba ....

*****

Gida yawuce da ita inda da shigarsu yagano baffah tare da mai martaba a farfajiyarsa da yake hutawa wanda ba wanda yake shiga wajen sai mutum mai daraja da ƙima. Wannan kenan,

Yana zuwa gaban  mai martaba yafara cewa ranka yadade, nan Abba (mai martaba) yace ya akayi ne Jamal naganka riƙe da hannun yarinya kamar mai laifi?

Jamal ne yayi gyaran Murya, yace Abbah a gaskiya nagaji nima yanzu ina so naga na kama iyalina saboda kuwa yanzu duniya ta lalace banaso nazo naga abinda ba shikenan ba shiyasa. Kansa akasa yake wanann maganar...

Mai martaba ne yayi gyaran Murya inda yake ɗan murmushi domin kuwa yaji daɗin abinda Jamal ɗin yazo masa dashi dan tun ba yau ba yakeso yaga JAMAL ɗin yayi magana.

To masha Allah naji daɗi da kazo min da wannan Maganar, amma wani hanzari ba gudu Ba kamanta kamana alkawarin bazaka tare da iyalinka ba har sai ta furta da bakinta ta na sonka katuna wannan maganar??????

Saurin ɗago idonsa yayi inda nan ya fara tuna alkawarin da yayi nan fa, ya ruɗe yakasa gane gabas bare arewa.

Baffa ne da ya lura da yanayin dayake ciki yasa shi saurin cewa haba ƴallabai ai magana ta ƙare tunda, tun ba yau ba nafahimci Fulani Maryam tana son yarona yarima dan haka me kuma zamu tsaya jira?

"Daɗi ne Yakama Jamal inda nan yayi godiya ga Allah daya kawo masa baffa cikin lamuransa.

Mai martaba ne yace to shikenan tunda dai abin yazo da haka,  amma a barni na tambayi ƴata tukunna.

Maryamu zo nan kinji yarinyata.

tasowa tayi a hankali kamar wadda kwai yafashe ma aciki tazo gaban sarki inda ta durkusa kasa dashi nan yayi sauri riko hannunta yace a'a Fulani zauna anan kusa dani nima kamar baffanki nake.

Matsawa tayi kaɗan kusa dashi,
Nan ya fara tambayar ta da shin kin amince zaki zauna da ɗa na yarima Jamal a matsayin mijin aurenki? Batare da cutuwa ba??

Shiru tayi tana kallon kowa a cikinsu, inda Jamal yakura mata wasu mayatattun idanunsa, saurin kifar da kanta ƙasa tayi .

Sake tambayar ta mai martaba yayi shin kin amince ko a'a ?

Kifaɗi ra'ayin ki yarinya ta babu wanda zai maki dole kinji ko?

Gyaɗa kai tayi alamar taji.

Ɗago kan dazatayi ne da sunan ba da amsa tayi ido biyu da baffan tah inda shikuma ya daga mata kai alamar ta amince.

"Nan tajuyo ta kalli mai martaba tace, ran Sarki yadade yakai Abba nah na amince da aurar ni dakayi ga yarima Jamal, na amince da auren kuma zan kasance mai biyayya a cikin zaman mu Insha Allah.

__ Wani irin daɗi Dukansu sukaji wanda idan ka cire ita Fulani saboda bata san ya akayi a kamata aure ba tun yanzu kuma ba tare da sanin taba. 

Mai martaba ne yayi gyaran Murya inda yace nasan Fulani Maryam zataso sanin ta yaya akayi mata aure batare da saninta.  ba to wannan ba aikin kowa bane aiki na ne bisa nazari da wasu abubuwa danayi akan ɗa na Jamal ..................

*LABARI* .....

Lokacin da Jamal motarsa ta makale yayi kokarin turata tafita daga chakwalin nn amma ina abin yaci tura, shine sai Allah yajefo masa ke to tun daga Lokacin da ya ganki ne muka kasa gane kansa inda na umarce sa daya nuna min gidanku kuma ya sanar dani ke din wacece, nan yamin bayanin duk abinda na bukata.

Haka na shirya tafiya ta cikin sirri batare da kowa yasan meƙe faruwa ba naje rugarku wajen iyayenki inda silar haka ne har na nemi aurenki wajen baffan ki, amma kafin baffanki yabani aurenki na sha wahala inda yaki yarda sai da kyar. Wannan kenan...

Bayan ƴan satika na turo yarima akan yazo ya nemi alfarma wajen mahaifinki akan yabasa ke yasaki a makaranta kiyi ilimi saboda rayuwa.

Ana haka ne har Allah yasa yarima yaga dacewar agyara wa mahaifinki gidansa amasa gini na zamani,
Amma  mahaifinki yaƙi ya inda yace shi abu ɗaya yakeso a masa, wanda yarima nan yace yafada ko menene yayi alƙawarin yimasa shi.

Baffanki ne yace shi yafison a gina masu masallaci da makarantun islamiyya, inda Jamal yace wannan ba abu bane Mai wahala ba baffa, amma ina so kaban damar saka Fulani a makaranta, ...........

har zuwa inda innatah ta amince shima ya amince....

( idan baku manta ba akwai inda suka zo gida ita da shi inda mahaifinta yafito suka gaisa nan yake sanar dashi abinda ke tafe dashi. To kafin nan yazo da ma sarki ya riga sa zuwa inda wannan zuwa da yayi shine zuwan bayan sarki).

*********
Lokacin da mai martaba yakuma dawowa yadawo ne akan yana neman auren Fulani Maryamu inda mai gari da al'ummar gari suka shaida auren yarima Jamal da Fulani Maryamu akan sadaki ₦100,000. .

Wannan shine asalin labarin auren su.....

Cigaban labari:-

Wani irin sanyi taji aranta tunda tun ba yau ba dama take yawan mafarkin yarima ba dan tun lokacin da ta ganshi taji ta mutu akansa duk da lokacin bata san menene soyayya ba amma ta dalilin yarima tagane me ake nufi da ita.









_Share#comment#like_

Masarautar JamalWhere stories live. Discover now