Bissmillahir rahamanir Rahim
Da sunan Allah mai rahama mai jin kai.Ina maka fatan alkairi sanin innah maskwani alkairin Allah ya isar maka a duk inda kake Nagode kwarai da kulawa Allah yakara arziki. Amin
***
Boka ne yabasu magungunan dasuka bukata baki daya inda ya kafa masu sharuda masu ƙarfin gaske.Inda suka lamunce masa sun yarda da duka sharudan da yace.
Tafiya sukayi inda kai tsaye suka nufi wani kauye domin binne wannan asiri, acikin wata rijiya suka jefa inda suna jefa wa falmata tafara kiran sunan JAMAL!JAMAL!!JAMAL!!!.
Cikin firgici yatashi a baccin dayake yana kiran sunan falmata falmata gani nan zuwa . gareki kina ina? Kizo gareni...
falmata!!!!!!!!!!!!!
Cikin karatsi yakira sunan.Tashi yayi yafito daga bangarensa inda kai tsaye yanufi fadar mai martaba inda yana shiga yakai gaisuwa ga iyayensa wanda acikinsu baba galadima ne kaɗai ya iya amsa wa domin kuwa har yanzu mai martaba fushi yake dashi .
"Baba galadima ne ya kallesa yace yarima naga kamar kana so kafadi wata magana ko?
Eh baba.
To Allah sa dai muji alheri ko kuma maryaman tadawo ne??A'a baba
To bissmillah muna sauraronka.To baba dama.. dama game da maganar yarinyar can ne..ummmm ...fal..ma..ta.
Baba muna son junanmu wallahi kamar zamu mutu dan Ni wallahi baba idan ba a auran ita ba zan iya rasa rain... Bai karasa fada ba yaji Muryar mai martaba inda yake cewa...Wallahi Jamal ko zaka mutu baxaka auri yarinyar nan ba wadda bata da kamun kai bata da daraja a idon mutane, amma kake tunanin zaka aura to ka saurareni dakyau kaji galadima yayi bincike akan lamarin auren yarinyar duka babu abin alkairi da aka jiyo akanta, to dan haka ina kara jan kunnenka akan ka cire maganarta acikin ranka.
Wani irin bugawa zuciyarsa tayi inda kai tsaye ya mike da shirin zuwa gaban mai martaba inda yana tashi yaji jiri na neman daukarsa a haka yadaure yana layi yakarasa wajen mahaifin nasa.
Yana zuwa zama yayi gabansa inda yarike kafafunsa yana neman gafararsa da yardar sa akan yabari ya aureta inda yace... Baba dan Allah na rokeka kasaka baki akan aurena domin yayi albarka wallahi baba ina son falmata zan iya rasa raina akanta baba ka taimakamin umma ma ta amince min da aurenta..
lol kuji min karya wajen Jamal ko a ina umma ta amince🙄🙄🙄🙄.??Janye sa Baba galadima yayi inda ya zaunar dashi yana mai tausar dashi akan yadaina kukan dayake yayi shiru ya hakura Insha Allah zai san yadda zasuyi.
Mai martaba ne yayi gyaran Murya inda yace galadima ina so kasani idan har kaga yaron nan yayi auren nan to babu raina, kuma koda Allah ya ƙaddara sai ya aureta to zai barmin gida baki daya kuma naciresa daga cikin zuri'ata, abu nagaba kuma dole sai ya nemo yarinyar mutane (ma'ana matarsa ), da yaransa kafin nan.Baba galadima duk jikinsa yayi sanyi da jin wannan hukunci da mai martaba yayanke bai masa daɗi ba.
Jamal ne yatashi yana kokarin fita inda da tashinsa kawai jiri yadaukesa ya fadi..
Nan da nan galadima yatashi yanufi wajensa inda sauran mutanen fadan ke zaune suka nufeshi..
Salati wani dogari ya saki lokacin da yaga babu numfashi atare dashi ga jiki duk ya saki.
Asibiti galadima yace anufi dashi .
Inda suka nufi asibitinsu da suke zuwa domin ganin likita...
Da zuwansu a ka karbesa tunda sunsa ko daga ina mutanen gidan suke.
A&E aka nufa dashi inda likitoci suka dunkufa kansa domin ganin sun dawo dashi hayyacinsa, amma ina abin yaki yiwuwa tun suna tunanin zai tashi har suka fara fidda rai kuma suna tunanin ko yashiga comer ne?
"Wani likita ne yafito inda yake ta goge zufa nan yace asamu wani yabiyo shi office zasuyi magana
Baba galadima ne yabisa inda kai tsaye ya samu waje yaxauna nan ya fara masa bayanin sunyi iya kokarin su domin su samu su ceto rayuwarsa amma ina...ai kafin yakarasa yaji Muryar umma tana doctor kada kacemin dana Jamal ya mutu??INNALILLAHI WA'INNA ILAIHIR RAJU'UN
Abinda ta iya furtawa kenan ta fadi anan sumammiya......Topa tirkashi ana wata ga wata
Ga umma sume
Ga Jamal yashiga comer shin comer ce ko kuma doguwar suma ce yayi???
Amsarku ce kawai zata iya fitar sani daga wannan rudun domin kuwa Ni kaina Nashiga rudu fa🏃🏃🏃🏃Taku har kullum
NAFEE KAZAURE