17_18

135 10 0
                                    

TADAMBO WRITER'S ASSOCIATION__*

        Tsintsiya madaurinki ɗaya
    ___________________________________

https://facebook.com/groups/195183905712588/

MASARAUTAR JAMAL


*******

___ Saurin rufe bakinta yayi inda ya fara cewa haba Fulani Maryamu  yazakimin haka daga faɗa maki gaskiya?

Saurin ƙasa tayi da kanta inda tafara cewa AE murna zasu tayani domin kuwa naga yariman danake zancen sa kullum a rigar mu, dan Allah muje kaga innatah da babanah kaji yarima?

"Jimmm, yayi sai kuma can yace to muje amma dai ke zaki rakani duk inda zani ko?
Tunda ke kika makarar dani da surutunki.

Saurin amsa masa tayi da toh amma sai na tambayi innah tah idan ta barni sai naje na rakaka, ko ba haka ba?
Eh yace da itah.

"Inda suka nufi hanyar shiga cikin rigar harɗo nan take masa kwatance har suka kai ga kofar gidansu. Yayi mamaki sosai dayaga gida mai kyau a irin wannan kauyen gashi ko wuta basu dashi amma ya gina wannan gida mai dimbin kyau, domin kuwa akauyen shine babba kuma yana da arzikin sa dai-dai gwargwado.

Shiga sukayi inda kafin su ƙarasa ta waigo taga bai biyota ba nan ta kwala kiran sunansa "yarima! Ya katsaya baka biyoni ba? Ko bakaso naraka kane?

Murmushi yayi wanda yakara bayyana kyawunsa, yace a'a inaso mana, Amma nafiso kifara shiga ki sanar da innarki da baffanki akwai bakon da zaki shigo dashi kinji ko?

"To tace tawuce cikin gidan.
Sallama take kwalawa kamar makauniya, inda innah wuro tafito tana lafiya mairamu?
Zungura baki tayi tace inna nifa kinsan bani son ana cemin mairamu ko? To to to ke Banda abinki ae ba kai tsaye nace wancan ɗin ba ko? Eh duk da haka dai baniso gwara ace min Fulani ta yafi daɗi koba haka ba? Murmushi tayi innah tace to shikenan. Yanzu ya akayi ne kike kwalan kira haka?

Yawwa dama ɗan sarki ne ya biyoni yace yana son yazo cikin ruga ne ya ga mutanan ciki shine nikuma nace sai dai ya fara zuwa wajen baffa nah.

Oh Ni saude ke kam wallahi Fulani baki ji ina ke ina magana da ɗan sarki? Ummmm.

Nifa bani na masa magana ba shine yafara min.

To nidai yanzu ina baffa na ? tunda ke kinki cewa yashigo.

Baffanki yaje gona yanzu zai dawo amma, suna cikin haka ne sukaji Muryar baffa nan Fulani ta ruga tace yawwa baffanah sannu da dawowa,
yawwa yace kafin nan takuma cewa baffa kaga wani bako awaje kuwa acikin wata iriyar mota mai sanyi ga laushi.

Baffa ne yace ae kuwa naga wannan mota amma ban lura da kowaye a cikinta ba saboda ina ta sauri nazo naga kindawo gida ko baki dawo ba.

To yanzu dai baffa kaje kaji meƙe tafe da ɗan Sarkin nan da yace yana son zuwa yaga mutanen ruga.

Tooh yace da ita inda yawuce hanyar waje. Fulani kikawo mana ruwa da tabarma ko, saboda ya zauna ba abar mutum mai girma irin wannan a tsaye ba. Toh tace inda ta wuce ɗaki domin zuwa aiken baffan tah....

Masarautar JamalWhere stories live. Discover now