33_34

70 10 0
                                    

_Typing_

                      *TADAMBO WRITER'S ASSOCIATION__*

        *Tsintsiya madaurinki ɗaya🤝🏻* 💐
___________________________________

https://facebook.com/groups/195183905712588/

MASARAUTAR JAMAL

Office ɗinsa ta nufa kai tsaye tashiga ciki batare da ambata umarnin shiga ba.

Sallama tayi masa inda kafin ya ɗago ya amsa sallamar ta ta har tasamu waje ta zauna inda yana kallonta yaji wata irin tsanarta na karuwa aransa nan yace ..

Meya kawoki office ɗina?

Shiru tayi saboda bata da amsar basa
Nan ya buga mata wata irin tsawa inda yace tambayarki nake kinmin shiru, shin meya kawoki office ɗina?

Wani dogon numfashi taja inda tafara cewa game da maganar aurenmu nadawo shin a ina ta tsaya ne yarimanah ?

Ji yayi gabansa yafaɗi jin furucin daya fito daga bakinta sai ya tsaya yana mata kallon baki da hankali
Canya juyo da hankalinsa kanta yace..
uhmmmm falmata dama nayi alkawarin aure dake ne?

Saurin daga masa kai tayi inda tace Yes natuna maka ranar ne?

Bana bukatar ji maganar shi taji yana fadin haka

Last gani na dake menace maki game da rayuwata da ta iyalina?
Nace kifita daga rayuwata amma baki ji ba ko?

Saurin ɗago kanta tayi tana  kallonsa yadda yake wani kicin kicin da fuska yana nema yagaya mata maganar da baza ta lamunta ba.

Katse shi tayi da daga hannu.. inda tace wallahi Jamal sai ka aureni koda kuwa baka kaunar Allah saboda lokacin dakake cikin jin daɗina bai hanaka kin furta wanna maganar ba saboda haka
Haka zaka sama ranka sai ka aureni idan kuwa ba haka ba zaka aureni ta dole ko kanso ko bakaso....
Inda tana gama fadar maganar takama hanyar fita....

Tsayawa yayi yana tunanin maganganunta na karshe  "ko kana so ko ba ka so wallahi sai ka aureni" to me take nufi kenan?? Bashi da mai basa amsa shiyasa yabar tunanin tacigaba da abinda ke gabansa.

Bayan kwana biyu da faruwar haka tsakanin sa da falmata yaji duk duniya babu macen da yakeson sama da ita.

Inda kai tsaye yawuce dakin gimbiyar tasa, inda ya hangeta kan sallaya tana addu'a sai da ta shafa sannan ya fara mata magana.....

Uhummm mairamu magana nake so muyi dake shiyasa kikaga banfita aiki da wuri ba

Inajinki yarimanah kafadi duk abinda kakeso Ni mai iya yimaka ce domin kuwa kaine farin cikinah,

Wani dadi yaji har cikin ransa saboda yasan bazai samu matsala daga wajen ta ba

Sai nan kuma kunya ta rufesa inda Yakama kamekame yarasa ma mai zai ce mata kawai sai yace ina sonki matata kinzama komai nawa

Saurin sakin murmushi tayi ta ɗago takalleshi amma jikinta yana bata kamar akwai abinda ke damunshi sai kawai tashare tacigaba da binsa ahaka har yamanta halin dayake ciki yabita da lalume har yasamu biyan bukata

Share✅
Editing❎
Vote ✅
Comments ✅

Masarautar JamalWhere stories live. Discover now