68

127 13 0
                                    

"Kallonta yake cikin tsana,
inda nan da nan ta diro daga gaban doctorn tadawo wajen yarima ƙoƙarin kama hannunsa take,
ya ture ta inda ya hankaɗata can gefe, hannu yafara nuna mata alamun kada ki kuskura kizo inda nake. ko ki sake tsautsayin tabani

'kuka tafashe dashi inda take shashekar kukan tana magana.
"dan allah kayji hakuri ka saurareni, duk da na aikata maka laifi amma kayafeni yarima.
na yarda ka yanke duk hukuncin da zaka yanke akaina amma dan allah karufamin asiri kada ka kai maganar nan fada, domin kuwa idan ka kaita kashina ya bushe, wallahi sai an hukunta ni hukunci wanda bansan wani iri bane zai biyo baya ba.

harara ya watsa mata, inda ya maida hankalinsa kan doctor kafin yayi magana doctor yace ran kai dad'e... kafin ya karasa ya dakatar dashi.
"naji duk yadda kukayi baka da laifi kaje kacigaba da aikinka.
To y'allabai nagode allah kara girma.
amin yace, tare da sa kai yafice daga office d'in.

""Kai tsaye b'angarensa yayi inda yatarar da fulani a kitchen tana ta girke girke kamar wadda za ayi baki agidan.
kai tsaye wajen ta yanufa direct yana shiga cikin kitchen ɗin ya rungumota baki ɗayanta kai tsaye daki ya wuce da ita bai tsaya ko ina ba sai kan gadonsu..

Masarautar JamalWhere stories live. Discover now