25_26

110 12 0
                                    

_Typing_

*TADAMBO WRITER'S ASSOCIATION__*

*Tsintsiya madaurinki ɗaya🤝🏻* 💐
___________________________________

https://facebook.com/groups/195183905712588/

*MASARAUTAR JAMAL*

🅿️2️⃣5️⃣➡️2️⃣6️⃣

Alhamdulillah dukkan Godiya ta tabbata ga Allah maɗaukakin Sarki
Inama dukkan Musulmin Duniya Barka da juma'a...

Bayan wata 4 da auransu ne, Falmata tanemi adress din zuwa gidan yarima inda tasamu adress ɗin cikin sauki batare da tasha wata wahala ba.

Sallama naji anayi daga bakin kofar dakina inda nafito da niyyar ganin wacece kawai sai naji saukan duka akaina wanda narasa wani irin laifi nama wannan baiwar Allah,

Sai da suka gama dukana ita da kawayenta sukayi mai isarsu sannan tace...

Ni sunana Falmata wadda mijinki yarima ya yaudara dan haka dama na dade da faɗa masa ya guji haduwa ta dashi domin kuwa nayi promise (alkawari) sai na ɗauki matakin abinda yamin ko akanki ko akasin haka,

Wannan kuma kawayena ne wanda duk abinda nakeso dole su so shi.

Shewa suka kwasa atare inda ɗaya daga cikinsu mai rike da dorina tafara cewa Ni wai ma Banda yarima menene kika rasa da zai zo ya auri Wannan shegiyar mayyar mai fuskar aljanu👹?

"Hmmm kema dai kinfaɗa kawata ko uban me yagani ajikinta da yake so haka?

Nan suka fara kai min duka ajikina inda daga karshe suka rufeni su duka da duka..

Ihuuu nake iya karfina don neman taimako amma ina gidan shiru bawanda yajini saboda kowa harkar gabansa yake,

Kuma babu mai zuwa part Dina har sai idan Ni nanema.

Haka na zauna suka gama duka na su duka,

Inda Falmata tace kuma kishirya wa kanki kaya kafin nashigo dan kin kusa barin gidan nan tunda ba tsoho ya gina ba.

Hawaye nake sosai wanda nikaina bansan da zubar sa ba amma banida zaɓin da yarage sai kuka...

Haka na wuni cikin jini wanda babu wanda yasan da haka acikin gidan.

Sai lokacin da baba hanne tashigo ne ta ganni awannan yanayin ne yasata tayi saurin karasawa wajena wanda tana zuwa tafara ta bani tana kiran sunana

FULANI !!!! Meyafaru dake ne haka????
INNALILLAHI WA'INNA ILAIHIR RAJU'UN!!!!!!!!!!!!

abinda take tafada kenan inda nan tayi sauri tadauki wayata takira yarima take sanar dashi halin danake ciki,

Ba afi minti goma ba sai ga yarima yashigo gidan kamar wanda aka koro haka suka ganshi inda kai tsaye bai tsaya jin komai ba yakwashe ta sai asibiti..... ..

Da zuwansa asibitin wasu nurses yagani inda kai tsaye wajensu yanufa nan yabasu ita sukayi emergency...

*Bayan 2hrs*.

Likitoci ne suka fito daga daƙin da aka shigar da ita inda wani acikinsu yace ƴallabai zakabini office ne akwai maganar da zamuyi dakai.. baiyi musu ba yabi bayansa.

Masarautar JamalWhere stories live. Discover now