This page I dedicated to you sweetheart ( F I Y)💓
***
"Bayan sun gama cin abincine uncle Anas yashigo da sallamarsa, umm mama mutafi ko?
dan yanzu honourable yakirani ankai Salma asibiti ba lafiya. To bansan meke damunta sai dai idan munje...Sallama sukayi da kowa na masarautar inda mai martaba yasa aka ɗauki motoci domin kaisu jaharsu.
Bayan sati biyu da dawowarsu Fulani Maryam ne mai martaba yasa ke ta rasu domin karayi masu nasiha akan suji tsoron Allah, komai mutum zai yi ya dinga tuna Allah.
Mai martaba yagama yi masu nasiha mai ratsa jiki inda nan yaba ma kowa damar yayi magana."Yarima ne yayi gyaran murya alamun yana da abinda zai ce.
Mai martaba yace muna sauraren ka yarima kafadi abinda ke bakinka ko?Allah karawa mai martaba tsawon rai, dama ba akan komai bane sai dan ina son Maryam zata koma sabon gidan dana gina domin kamar can zaifi mata kwanciyar hankali.
Falmata tace tayi saurin ɗagowa tana kallon sa irin kallon Ni zakaci amana, bayan mun gama magana dakai shine zakace wata sakarya takoma to wallahi bazata saɓuba, da sake.
"Mai martaba ne yafara magana, to yanzu dai Ni banida abinda zance game da kai da iyalinka amma kuma dai akwai wata shawara da zan baka Jamal domin kuwa zata amfaneka koda nan gaba,shin kamanta kai ne zaka zama sarki nan bada daɗewa ba??
Shiru yayi yana nazarin maganar mai martaban..
_Sake magana yayi a karo na biyu
Yarima Jamal Ni abduljalal nakusa sauka daga kan karagar mulki na baka a matsayin mai wakiltar kasarka domin kuwa nasan kai ne zakayi abinda zanyi, kuma zaka iya linkawa akan nawa kaga kenan zakafini kwarewa dan yadda na lura dakai kowa yana san ace yau kaine zaka kashewa wasu Shari'a idan sun kawo kukansu.Kabbara aka dauka a fadar tare da yiwa sarki fatan nasara da nisan kwana..
Allah Sarki akace ɗa da mahaifi sai Allah duk da mai martaba ya lura da Jamal baya farin ciki da abinda ya sanar dashi, amma sai yaboye damuwarsa Dan kar ran mahaifinsa ya ɓaci yaga kamar bai isa dashi ba, shiyasa sai ya saki ransa inda yafara dan murmushi wanda zamu kira da shi ba farin ciki ba shi ba baƙin ciki ba.
A haka dai taro ya watse inda aka bar maganar komawar Fulani sabon gida.
Manage pls
04/08/2021