23_24

102 13 0
                                    

_Typing_

              TADAMBO WRITER'S ASSOCIATION

        Tsintsiya madaurinki ɗaya
___________________________________

https://facebook.com/groups/195183905712588/

*MASARAUTAR JAMAL*

🅿️ 2️⃣ 3 ➡️ 2️⃣ 4

Sarki ne yayi gyaran Murya inda hankalin kowa yakoma kansa.

Magana yafara inda yace..

Yarima yanzu yaushe kake so matarka Maryamu takoma ɗakinta?

Saurin bada amsa yayi inda yace mai martaba Ni Ko ayau ma ina so takoma (hmmmm su yarima ba kunya😅).

Nan mai martaba yace to shikenan amma zamuji ta bakin iyayen ita yarinyar ko? Saboda bazamu yanke shawara mu kaɗai ba. Eh haka ne Abba.

Mai martaba ne yajuyo ya kalli baffa inda yace to baffa kaji dai abinda yaronka yace ko? Game da maganar matarsa. Amma yakake gani za'ayi?

Nidai ta ɓangare na bana bukatar komai Ni nayi alkawarin zan mawa mairama komai da uba kema Ƴar sa.

Eh ƴallabai naji amma wani hanzari ba gudu ba da kabari munyi mata koda kayan kitchen ne saboda kuwa nauyin zai maku yawa gwara muma mu rage mak....

inda kafin ya rufe baki Jamal yayi saurin cewa a'a baffa nah kabari komai Abbah yayi tunda dai muma ya'yansa ne 😇

Murmushi mai martaba da baffa sukayi inda aka gama tsara komai acikin barkwanci Anan har aka ajje ranar da Fulani Maryamu zata tafi dakin mijinta....

*******

Bayan wata ɗaya da saka biki.

" A yau ne asabar ranar da mai martaba da baffa suka saka ranar da za bama yarima Jamal  matarsa inda kowa da kowa ke shiri ɓangaren amarya suna shirye² ɓangaren ango ma haka.

*9:30pm* motocine na alfarma aka jerasu a kofar gidan baffa, wanda tun daga kofar gidan baffa har zuwa kofar mai gari motoci ne na ɗaukar amarya, wanda duk wanda ka gani akauyen nan zance yake anya harɗo ba saida Ƴar sa yayi ba? Wasu kuma suce yankan kai yake yi shine a cikinsu wani yaga yarinyar sa yace yana so shine ya basu, kowa dai da irin abinda yake tofawa wasu kuwa fatan alkairi suke wa baffa da innah saboda kuwa yarinyar su tayi dacen miji ɗan sarki guda!.

*FADAR MAI MARTABA YAHYA IBRAHIM*

suka nufa da amarya, adalin sarki mai mulki akan dai-dai  gaba dai gaba dai ja gayya dole aganka kuma dole akyaleka kaci dubu sai ceto babu yadda suka iya dole aganka a hakura shugaban kowa , kaine a gaba kaine a baya. .

Haka fadawan nan suka dinga kirari har aka shigo da amarya.

Nan kowa yawatse yabar yarima Jamal da amaryarsa da mai martaba da Ammi ( *uwar Jamal kenan)?*  inda suka fara masu nasiha akan su rike junansu da gaskiya da amana, Banda jin zan tuka suna amfani dasu, ke kuma Fulani duk abinda mijinki yakeso kidinga bi, kibar abinda baiso. Kinji ko??

Eh naji Ammi Insha Allah!

Yawwa toh Allah yayi maku albarka .

Nan suka ce Amin Dukansu.

Mai martaba ne yakara tashi nasihar akan wadda Ammi tamasu inda yake cewa Jamal dama wannan ranar nake jira tazo naga aurenka to yanzu dai Alhamdulillah tunda lokaci yayi, inaso zanyi murabus daga kan mulki nabaka shi..

Jamal ne yayi saurin kallon Abbansa inda zaiyi magana Abba ya dakatar dashi nan yace ko kana so ko baka so dole sai ka karbi wannan matsayi ma'ana (nauyin da zan daura maka).

Jiki ba kwari yatashi yafice inda Ammi na lura da duk yanayinsa saboda da ma can ba san wannan mulkin yake ba haka nan aka jajuɓa masa, Amma yaza'ayi da ikon Allah idan yace, *kunfayakun*

* Bayan sati ɗaya

Amarya, gimbiya, sarauniya, kuma Fulani mairama agidan yarima na hango hannunta riƙe da na yarimanta inda take ƙoƙarin cirewa amma gogan yaƙi bari har tagaji ta hakura,

"Inda suke takowa a hankali daga mata kalar benen gidan.
Sunzo gabb da karasowa silɓi ya dauke ta ji kake tayi baya zata faɗi kafin takai ga faduwar yayi saurin tare bayanta inda ta faɗa kan kirjinsa nan yaji wata iriyar faduwar gaba wadda tun zamansu bai taɓa jin irinta ba suna a haka ne kawai yaji.... Tana motsa masa inda yayi karfin halin ɗora harshensa akan bakin ta nan ya fara kissing ɗin harshenta.............










Yawan comments yawan typing

*Godiya dubu ga mutanen Jigawa state* 

*30/03/2021*

✍🏻

Masarautar JamalWhere stories live. Discover now