Typing...
*TADAMBO WRITERS ASSOCIATION*
[Tsintsiya maɗaurinki ɗaya]
Facebook link here 👇https://facebook.com/groups/195183905712588/
YouTube channel
https://youtube.com/channel/UCBdlYTQ6OQf0U_T_sOkbKxQTalegram
https://t.me/joinchat/XXHgM8SrIOQ5ZDhk𝑀𝐴𝑆𝐴𝑅𝐴𝑈𝑇𝐴𝑅 𝐽𝐴𝑀𝐴𝐿
53_54
_________________________INA MEKA GAISUWATA GAREKU MASOYA LITTAFI MASARAUTAR JAMAL , KUN NUNA MIN SO NA FISABILILLAHI NAGODE SOSAI NIMA INA MAKU SONSO ❤️❤️❤️😘😘😘😘😘
This page I dedicated to her (hanifa Usman Kazaure )
*****
"Yarima ne yatashi a baccin dayake,
cikin jin haushi inda ya tsinci kansa da jin haushin falmata wanda yarasa dalilin hakan.Juyi tayi acikin baccinta inda tayi wata irin miƙa haɗe da ihu.. wani saurin kallonta yayi inda yace ke wata irin banza ce wai daga tashinki a bacci ba salati ba addu'a ki fara wani ihu, cikin ɓacin rai yake maganar sa.
Baki tasaki tana kallonsa, inda yace kallon fa? Na menene?
Ko kulasa batayi ba saboda takaici, takasa kulasa meƙewa tayi ta wuce banɗaki batare da tace masa kala ba.
Shiga tayi batare da tayi addu'a ba tafaɗa ciki tafara watsa ruwa ajikinta, wanda kafin ta gama wankan saida ta bata wajen 1hr. Kafin nan tafito ta ɗaura alwala tayi sallah."Tashi yayi yawuce apartment ɗinsa inda direct toilet yashiga ya watsa ruwa, kafin yafito.
Ɓangaren mahaifiyarsa ya nufa kai tsaye, inda ya tarar da ita tana ta kallon hoton twins ɗinsa tana hawaye.. wani irin faduwar gaba yaji alokacin da ya ganta sai yaji lokaci ɗaya Fulani tadawo masa cikin tunaninsa inda kai tsaye ya nufi wajen ta yaxauna Yakama kafafunta yakamo inda ya durƙusa gabanta Yana mai lallashinta...
Umma ina mai baki hakuri akan wannan al'amari daya faru kimin addu'a wallahi nikaina sai da nayi auren nan nakejin duk natsani komai na duniyar nan.
Umma ina son matata uwar ya'yana, umma narasa ina zanga Maryamu da yaranta ? Umma kitaimakeni ki tayani nemanta umma kimin addu'a dan Allah.
Ɗago idanuwanta tayi takallesa inda yayi jajur dasu ta buɗe baki tace... nasani Jamal Insha Allahu komai zai daidaita da yarda Allah,
Maryamu zata dawo ita da ahalinta insha'Allah.Allah yayarda umma Nagode da addu'arki gareni.
Bakomai yarima. Ina ita amaryar taka take?Fuska yaɓata alamun kamar baiso tambayar ba, uwa mai fahimtar ƴaƴanta sai ta fuskanci kamar ransa baiso ba da tambayar da ta masa.
A hankali tafara jansa da hira har Allah yasa yasaki jikinsa yafara mantawa da wata damuwa da ya shigo da ita.
**********
📲 Jalila ce na hango da uniform na islamiya a jikinta ta na rike da alkur'ani a hannunta, inda ta taho tana tafiya a nutse kamar ba karamar yarinya ba. Wadda idan kaganta bazakace Ƴar shekara 10 bace, yarinya nutsatsiyya mai hankali ga ilimin addini dana boko Allah yabata dan ko acikin makarantarsu ana ji dasu especially dai jalila dan tafi jalil kokari ta kowani fanni, amma shima ba abarsa a baya ba dan yana da iya kokarinsa dan yafi Jalila kokari a ɓangaren addini duk da yaro ne amma ƙwaƙwalwarsa bata hanashi ɗaukar karatun ba.
Ammi naji suna kiran sunanta inda naga wata kyakkyawar mace kamar matar governor, tafito daga wani bangare na gidan inda kai tsaye take nufar yaran nan da naga suna ta kiran sunanta, wani murmushi tasaki akan fuskarta wanda silar hakan yasa kyawun fuskarta yasake bayyana.
Jalil ne yayi saurin rugowa ya rungume mahaifiyar tasa inda yake cewa Ammi yunwa nakeji kuma aunty salma tace zataje dani mall anjima idan na bata haddar abinda muka yi yau a makarantar mu.
To ɗan gidan aunty salma kada kadamu Bara mu shiga ciki sai kabata haddar ko?
Eh Ammi..
Yawwa yaron Ammi muje to... Hannunsa takama da na Jalila suka wuce cikin gidan.......
Manage please🖊️📝
𝑡𝑎𝑘𝑢 ℎ𝑎𝑟 𝑘𝑢𝑙𝑙𝑢𝑚 𝐧𝐚𝐟𝐞𝐞 𝐤𝐚𝐳𝐚𝐮𝐫𝐞