7_8

237 20 0
                                    

Typing

       TADAMBO WRITER'S ASSOCIATION

        [Tsintsiya madaurinki ɗaya]
     ___________________________________

MADARAUTAR JAMAL

https://facebook.com/groups/195183905712588/

7️⃣➡️8️⃣

"Lokacin da iyayen falmata suka Kaita kasar London domin tayi karatu anan ne ta hadu da wani Basaraken mutum wanda shi ba ruwansa da ƴanmata rayuwarsa yake irin ta saraki wanda suka san jinin na binsu ajikinsu,

dan haka tayi kokarin dole sai ta kulla alaka dashi kota halin ƙaƙanikayi,

anan ne tasamu wata dama daza tayi amfani da ita wajen ganin ta mallaki wannan guy damar itace ;

" lokacin da yarima yashiga lecture room anan falmata tagansa nan take taji yashiga ranta ya kwanta mata har tana tunanin ita fa tasamu mijin holewarta domin kuwa ita burinta arayuwa ta haɗu da kyakkyawan namiji mai tsari irin wanda take gani a Bollywood wannan ne yasa takasa tsayawa ta fidda namijin da ya dace da ita sai kame kame. Shigowar sa kenan cikin hall

yaga kallo yadawo kansa inda nan wani abokinsa abdoulra'uf ya fara kwala masa kira da yarima na ƴanmata koda kudinsa sai da rabonsu kai ba irin tsarin su ba ne kai din na dabanne yarima saraki nan yayi wani shegen smile wanda baka gane irin manufarsa,
domin shi dai Jamal irin mutanen nanne masu son adinga zugasu da abinda suke dashi shiyasa abokanan sa suka fahimci haka to idan suna da matsala da sun fara masa wannan kirari ko nawa suke so kuwa zai basu.

Wannan itace hallayarsa awajen abokanansa don haka duk cikin friends dinsa yafi kaunar abdoulra'uf domin kuwa shima yana da izza daidai tashi,

To ganin irin kaunar da ke tsakanin Jamal da abdoulra'uf ne yasa falmata kulla ƙawance da abdoulra'uf domin kuwa shi ɗin na ƴanmata ne shiyasa duk inda yake zaka ga mata awajen.

Da wannan dama falmata tasamu har tafara magana da Jamal amma ba kamar yadda take mu'amala da abdoulra'uf ba, ana haka ne wata rana suna zaune sai abdoulra'uf yakira falmata awaya suna gaisawa sai yake tambayar ta kawarta queen, nan ne ma har tasamu dama tafara faɗa masa irin son da takema abokinsa JAMAL,

nan yace da ita kibari later we will talk saboda yanzu am busy, sorry nan tace bakomai ra'uf Nagode bye bye okay beb bye.

"" Zaune suke ita dashi akan wani kujera na wajen cin abinci inda yasa akamasu order na abinda suke so nan ya bude lemo ya zuba yana sha yace bismillah ko?

nan ta bude tafara sha inda yace jiya muna magana kuma na katseki ko?
Tace eh kam dama ba komai bane yasa nakeso muyi magana ba akan abokinka ne Jamal ina sonsa ra'uf yadda baka tunani tun ranar dana gansa naji yatafi da imanina wallahi zan iya yimasa komai akan yaban lokacinsa,
Please abdoul na rokeka dan Allah kahadani da abokinka Jamal ina son Jamal kamar rayuwata.

Nan yayi jim kadan yana tunanin tayaya zai fara mawa Jamal wannan maganar dan yasan halin kayansa da jan aji..
da kyar yaso ta,
sai kuma can yayi wani tunani sai yace kodan ma AE dole ma yasota saboda yarinyar Allah ya bata komai irin wanda ake buƙata ga mace, 

nan yace is okay falmata zanyi kokari naga nahada wannan ruhi waje daya insha ALLAH.

nan tayi murmushi wanda yakara fito da asalin kyawunta inda nan tafara masa godiya Nagode sosai abdoul Allah bar kauna Nagode.

Masarautar JamalWhere stories live. Discover now