TADAMBO WRITER'S ASSOCIATION
[Tsintsiya madaurinki ɗaya]
*IN THE NAME OF ALLAH* ✍🏻
3️⃣⏩4️⃣
__________________________________Durkushewa tayi Anan tana kuka tana tsinema Jamal tana, nayi nadama kuma nayi da nasanin baka yarda ta Jamal,
kuka take iya karfinta saboda kuwa abinda Jamal yamata ba karamin abu bane,inda nan tagama kukanta ta mike tayi tafiyarta inda take saka abubuwa dayawa aranta domin kuwa tayi promise akan sai tadau fansar abinda Jamal yamata dan gani take idan tabarsa yaci bilis fa kenan.
( Hmmmm koda wasa kada kiyarda namiji kuyi fada kinemi cewa zaki hanasa zaman lafiya ko wani abu daban domin kuwa idan baki hana sa ba shi zai hanaki domin kuwa idan yafada maki wata maganar sai kinji dama baki san da ruhinsa ba a duniya dan haka mukiyaye)."Tafiya take tana ta sake sake ahanya har ta hau kan titi bata san tahau ba kawai sai kara taji kiiiiiiiii......na mota alamar anbugeta kenan!
inda nan take jini yafara zuba ta kanta.....
mai motar kansa baisan haka ta faru ba domin kuwa shima yana tuki ne yana tunanin wata rayuwar daban inda kawai sai ji yayi ya buge mutum,nan yafito da saurinsa daga cikin motar inda yafara salati yana neman taimakon mutane kafin kace me wurin har ya cika da mutane inda nan suka taimaka masa yasaka ta amota yatafi da ita asibiti..
*KAZAURE GENERAL HOSPITAL*🏨
"Nan naga yanufa da ita inda atake nurses din wajen sukayi saurin karbar ta domin kuwa emergency case ne ko ɗan sanda basu nema ba saboda yarinyar tana bukatar taimakon gaggawa,
idan kuwa akace sai anjira police sunzo to zata iya rasa ranta, akowani lokaci shiyasa sukayi saurin karbar ta.
inda nan aka bashi wata takarda yacike kafin a shiga da ita theatre room, nan yayi signing yayi komai, atake aka shiga da ita aka fara mata aiki domin kuwa falmata bakaramin ciwo taji ba dan har aka gama mata aiki bata dawo hayyacin ta ba.
Ahaka likitoci suka mata allurai har Allah yasa akaga tafara motsa idonta inda atake nurses din dake kanta sukayi murmushin domin kuwa suna so suga sunyi aiki ace yayi kyau dan kuwa idan da sabo sun saba aiki yayi kyau kuma yayi yadda akeso
dan ko farka ka akayi akamaka ɗinki wajen bai nuna tabo domin kyan aikinsu lol sai kace a London 😁😁😁😂 kodan garinku burninku inji malam bahaushe...
Nan suka fita suka sanar dashi halin da ake ciki inda suke sanar dashi har tayi motsi ma domin kuwa aikin yayi kyau sosai nan yayi masu godiya...
yawuce cikin dakin da aka kwantar da ita inda dashigarsa keda wuya yaga tana wasu irin sunbatu mararsa kan gado inda yanufe ta kai tsaye yana mata addu'a adaukarsa ko aljanune da ita inda yaga lokaci ɗaya ta chanja kuma nan ya samu guri ya zauna kusa da ita inda yake cemata sannu ko ƴanmata?
ya jikin naƙi da fatan dai yayi sauki?
nan tadago ta kalli inda take juyo maganar nan taga wata fuska da bazata taba manta wannan fuskarba,
domin shima sai da yaga tajuyo yaga ashe itace nan yafara cewa dama kina nan falmata?
Ita ma lokacin tace da ma kana nan kabeer inda lokaci guda hawaye yafara zuba a idonta tana Wannan wace irin ƙaddara ce na hadu da ita arayuwata??
(lokacin da yamaketa amota yana tunani gashi yamake abu dole atsoroce yafito dan ko kallon fuskarta baiyi ba baisan wacece ba sai yanzu da yazo dubata sannan yaga wacece).
Muje zuwa masoyana
'''Please share and comments
Always you are in my mind fans and family kudai kucigaba da nuna min kauna 🥰🥰🥰🥰🥰'''