_Typing_
TADAMBO WRITER'S ASSOCIATION
{ Tsintsiya madaurinki ɗaya}
___________________________________https://facebook.com/groups/195183905712588/
*MASARAUTAR JAMAL*1️⃣5️⃣⏩1️⃣6️⃣
Horn yake akofar gidan, inda mai gadi yazo yabude masa gate, saka kan motar yayi cikin gidan inda kai tsaye parking space yawuce.
Fitowa yayi,
yayinda ita kuma harta riga shi, shiga parlo inda nan tafara kwala kiran
''Mummy Mummy!Falmata baby!
Waye yamaki wannan ciwon najikinki???Bata jira bata amsa ba ta zaro mayafin ta da jaka tace muje station kowaye sai ya banbance mun tsakanin aya da tsakuwa.
Wanna ciwo kamar me,
ke tukunna ma waye yamaki wannan abun?Juyo Muryar da mummy tayi ne yasata sakin salati.....
tafara kiran sunan kabier, abinda zaka saka min dashi kenan me Falmata tamaka ne da har kake ƙoƙarin kashe min ƴa?
Ummmm?
Tambayarka nake kayi shiru.
Mummy ba haka bane duk abinda yafaru kitambaye ta kiji idan laifi na ne nayarda kimin duk hukuncin daya dace dani.
Nan taja hannunta suka zauna tafara tambayar meya faru da ita ne kuma ya akayi haka ta faru ? Nan takwashe komai tafada mata...
Jikin mummy ne yayi sanyi saboda rashin kirkin da tafara ma Kabir,
nan tace to kunje asibiti ne?Eh tace inda tace to tashi kishiga ɗaki kije kiyi wanka sai muje asake dubaki ko?
Toh tace ta tashi tawuce abinta.
Kabeer ne yace mummy ina yini?
"Lapiya tace dashi.
Mummy Bara nawuce GA magungunan ta nan akwai direction na yadda zatayi amfani dashi,
okay kawai tace ta tashi tabarshi a wajen ta wuce abinta...Tashi yayi yabar parlon yawuce parking space yadauki motarsa yabar unguwar.
*Bayan wata biyu*
" Yarima Jamal ne nagani yana shirin fita shida dogarai, inda yake basu umarnin su koma fada yau shi kadai yake son fita dan yana son zaga gari ne,
nan wani bafade yace ƴallabai kayi hakuri wannan aikin na mai martaba ne domin kuwa yace kada asake bari kana tafiya kai ɗaya,
amma kayi hakuri idan magana ta tabata maka rai tuba nake."Wannan umarni ne nabaku ba wai shawara nake baku ba.
_Jan motarsa yayi yawuce inda zaya domin kuwa yau tashi yayi da sha'awar yazaga gari,
Yana cikin tafiya ne kawai motarsa ta makale ajikin wani taɓo inda yaja yaja yakasa wucewa,
fitowa yayi daga cikin motar inda ya duba yaga menene ya riƙe masa motarsa,
fitowar sa yayi dai-dai da zuwan wata yarinya Ƴar Fulani da kayan su na Fulani ajikin ta,"Assalamu alaikum"
Ƴanmata Barka ko?
Barka dai
da wata iriyar Hausar ta wadda bata fita sosai,
jiyayi gabansa yafadi saboda tunda yake bai tabajin irin Muryar nan ba gashi Hausar ta ma abin daɗi,
nan yace kinga dan Allah taimaka min zakiyi,Dame zan iya taimaka maka nida ba wani karfi gareni ba..
Murmushi yayi domin kuwa maganarta, ta tana burgesa.
nan yace mota na ce ta makale shine nakeso kitayani turawa tunda kinga dai Ni dai bazan iya janta ahaka ba ko?
Tsayawa tayi tana tunanin wannan mutumin anya kuwa mutum ne?
saboda sai Yanzu ta kalli fuskarsa, taga wata irin halitta daba ta taɓa ganin irinta ba, nan tayi sake tana kallonsa,"tambayar daya mata ma bata basa amsa ba "
Shirun dayaji tayi ne yasa sa kara magana yace uhmmmm fillo ko bakiji mai nace ba?
Murmushi tayi tace tohm ɗan sarki naji abinda kace,
amma Kur'anin Allah bazan iya tura maka wannan katotuwar abar nan ba,
sai dai naje nakira maka halliru a rigar mu ya tura maka ita.Tohm yace da ita,
inda yace ko zan iya sanin sunanki?Wani farrrr, tayi da idanunta inda nan yakuma jin gabansa yafaɗi,
"Astagafurullah"
yace a ransa, inda nan yaji tace Ni dai sunana *FULANI* amma Acikin rigar mu ne ake kirana dashi.
Nagaskiya fa?
tsinkar muryarsa tayi da jin yana son sanin sunanta na gaske,*MARYAMU*
amma babu wanda yake kirana dashi saboda sunan innatah ne.
Jindadin hirar ta yake saboda haka nan yaji yana jin wani sanyi idan yana jin muryarta,
nan yajuyo yaga tana kallonsa tace shikenan natafi nakira maka hallirun?
Eh yace da ita,ta wuce abinta domin kiran halliru.
Sai da tayi nisa kaɗan ya kwala kiranta ahankali..
FULANI..
amma idan kinje zaki dawo ko?Eh tace dashi ta ruga abinta🏃♀️,
___Halliru nagani da wani abokinsa suna tahowa wajen da motar yarima take, inda suna zuwa suka fara kai gaisuwa irin ta saraki da ake basu idan anje inda suke.
Haka sukayi ƙoƙarin tura motar har Allah yasa tatashi daga wajen inda tana fara tafiya Fulani ta kwala wani ƙara na murna alamun taji daɗin ganin motar na tafiya.
Fitowa yarima yayi daga cikin motar yabasu hannu sukayi ma juna godiya inda ya dauko wata takarda yaciro wasu ƴan kudade da bazan iya sanin ko nawa bane yabasu. Nan suka fara masa godiya suka karba suka wuce.
FULANI!
Naam dama kaine wai yariman da ake cewa ɗan sarki mai jiran gado?Murmushi yamata yace ya akayi kikasani?
Ni kafara bani amsana tukunna sai na faɗa maka.
Dariya yayi yace to shikenan zan faɗa maki,
nan tafara washe baki tace tohm kaine ko ba kai bane?Eh nine..
Zaro ido tayi tace wayyo Allah na Ni Maryamu yau gani ga yarima ɗan sarki har yana hira dani wayyo Laure wayyo Bintalo kuzo kuga yarima ɗan sarki a cikin rigar mu har muna magana 💃💃💃💃💃
# *Vote#comments#share#likes*
Manage please
*23/3/2020*
_Tuesday_