_Typing_
*TADAMBO WRITER'S ASSOCIATION__*
*Tsintsiya madaurinki ɗaya🤝🏻* 💐
___________________________________https://facebook.com/groups/195183905712588/
MASARAUTAR JAMAL
**Barka da sallah dafatan munyi sallah lafiya, Allah maimaita mana Amin.
*Bayan Jamal yaba ma umma yaran ne yajuya yana kokarin komawa dakin da aka kwantar da gimbiyar tasa...
"Tura kofar dakin yayi yana shiga yayi arba da ita akan gadon tana ta sharar bacci abinta,
_nan ya shiga kallon siffar jikinta yana ayyana abubuwa da yawa aransa...
"Motsa idanuwanta tafara yi inda yayi saurin maido hankalinsa kanta inda ya fara cemata sannu Fulani ya jikin naki?? Dasauki ko, babu inda yake maki ciwo duk atare yake jero mata wadannan tambayoyi?
inda aciki guda ɗaya ta iya amsa masa shine lafiya kalau. Nan ya fara nan da nan da ita motsi kaɗan sai ya fara cewa mekike bukata ko kina son wani abu?? Sai dai tayi murmushi na gefen baki tace a'a Khushi bana son ci komai yanzu burina kawai naganni tare da kai da yaran mu sai yaji wani sanyi aransa inda yace Insha Allah zaki hi sauki soon my wife tace Allah sa, yace Amin..
*****
"Wata nurse ce tashigo inda ta gaida yarima Jamal cikin ladabi, ya amsa mata yana ta wani washe baki saboda kyautar da Allah yamasa ta yara kyawawa masu kama dashi,
yana cikin wannan yanayi na farin cikine har nurse din tagama abinda take bai sani ba yazo fita ne tace to ƴallabai zamu iya sallamarku saboda uwar yaran tana lafiya kamar yadda yaran suke lafiya. Nan yayi saurin cewa toh toh Nagane sannu mungode sosai Allah saka maku da gidan aljanna mafificiya,
nan nurse din tace Amin.... Tayi wucewarta abarta inda tabar yarima yana hada kaya domin sai wani azarzabi yake yau shine yazama uba wannan wani irin gata ne Ubangiji yamasa. .
****
"Gida suka nufa inda tuntuni umma ta riga da tatafi da yaran gida tana ganin idan tabarsu anan bazasu samu wankan kirki ba,
amma gwara takaisu a musu wankan gargajiya wanda koda nan gaba kashinsu da fatarsu zatayi kwari yadda ya kamata..
Horn driver yake inda mai gadi idi yazo ya buɗe gate suka shigar da motarsu...'Dakinta tawuce kai tsaye inda tana zuwa bata zame ko ina ba sai kan gado inda tana kwanciya sai ga yakumbo lami ta shigo dakin tana fadin yo ke Banda abinki mairamu yazaki zo ki kwanta da danyen jiki haka maza tashi kicire kayan nan kafin in shigo da ruwan wanki maza tashi....
Toh tace inda take kokarin tashi domin kuwa batason jan magana mai tsayi dan wani irin bacci ne yake fusgarta mai nauyin gaske...
Gasata yakumbo take inda tafara korafi akan zafin ruwan yayi mata yawa dan Allah yakumbo kisirka kasa wallahi wurin kamar zai daye tana maganar tana zubar da hawaye, nan yakumbo tace yoo ke Banda abinki mairamu idan ba agasaki yadda yadace ba ai lalacewa zakiyi ko so kike kizama tsohuwa mijinki yasake aure? Sai taji gabanta ya yanke yafaɗi sai kawai tacigaba da zubar da hawayenta, ahaka har yakumbo tagama gasata inda tace to Bara nabarki kiyi wanka kuma yanzu amma dan Allah mairamu kidaure kiyi dana zafin nan dana ajje maki agefe ba ason mace sabuwar haihuwa tana amfani da ruwan sanyi ko wajen sha ko wanka, kinji ko?
To yakumbo Nagode sannu.
yawwa tafice abinta,...
inda tana fita tawuce kicin dan hado mata kunun da ta dama tun kafin shigarta wankan nan ta dakko flask din ta nufi ɗakinta inda yaran suna kan gado abinsu sai bacci suke, ta na tsaye tana jiran fitowarta sai taga ta bude kofa inda ta na fitowa tafara mitar wallahi yakumbo ruwan nan kamar zan salke fatar jikina haka na dinga jinsa, yar dariya yakumbo tayi inda tace yanzu bazaki gane amfanin hakan ba sai nan gaba, saboda shi wannan ruwan dakike gani ana sakaku da zafi ba wai ba a sonku bane a'a ana so a gyara ku ne saboda idan cikinku yalalce to kingama aiki a wajen namiji sai dai kizama bango dan zuwa zaiyi yakaro aurensa bbu abinda yadamesa, to kinji dalili... Nan tace haka ne kuma yakumbo Allah dai ya karama na lafiya yakumbo tace Amin ya rabbi.....
"A haka dai har Maryam tayi sati da haihuwa inda ranar suna yara suka ci sunan babanta da sunan mamansa inda suke kiransu da (Jalil da jalila).
Inda ranar sunan yara sunga gata irin wanda kowani uba yakewa ya'yansa.. to sai dai muce Masha Allah, Allah ya rayasu bisa sunnar ma'aiki (s.a.w).
*Bayan arba'in (after 40)*
Fulani ta murmure tayi kyau abinta kamar ba ita bace ta haihu jikinta yayi kyau sosai...
"Yakumbo ce tashigo dakin rike da twins inda ta wuce direct wajen gadon da Maryam din take tameka mata yaran tana kibasu susha saboda sunjima basu sha ba... Karbar su tayi inda tafara shayar dasu cikin nutsuwa da kwanciyar hankali.....
Shigowar sa dakin itace ta maido da hankalinta kansa inda yana kallonta yaji wani irin magana disun sonta na kara fizgarsa nan idanuwansa suka fara chanja launi inda kai tsaye ya nufi inda take nan taji gabanta yafaɗi ganin yanayin dayake ciki nan take ta lura dashi tagane sarai inda yadosa sai ta maida tsoronta kamar bata gane me yake nufi ba sai kawai ya fara lalubarta inda yake mata wasu irin sambatu kamar zautacce nan da nan ya fara aika mata da sako inda sakon yafara kaiwa inda akeso, nan yadinga jagulata har Allah yasa yasamu biyan bukatarsa ......
Wanka sukayi suka fito atare inda suke ta wasa suna dariya inda tashiryasa itama ta shirya kanta...
Muhade a next page
Share
Vote
Comments
Follows
#Nafee_kazaure