T . W. A
M J
45_46
Sallama sukayi inda suka ajje maganar agobe dole azo ayi maganar aurensu.
Dan yanzu hankalin Jamal idan yayi dubu yatashi dan duk lokacin da falmata zata kirasa sai yaji dama suna tare ne, kuma sonta kara shiga ransa yake kamar yadda yake fidda numfashi haka sonta ke sake shiga ransa.Akwana a tashi babu wuya yau kwanakin da umma ta debarma Jamal suna gab da cika domin kuwa yau ya kama saura kwana 2 ta hatgitsa masa komai dayake shirin yi.
Fadar mai martaba Yahaya yanufa inda ya tarar da kowa na zuriar gidan yana cikin dakin,
Ahaka yasaka kansa cikin dakin inda yagaisar da iyayensa baki daya.
Galadima ne yayi gyaran Murya "inda ya fara da cewa ...
Jamal wannan zaman naka ne ba na kowa ba domin kuwa sai yanzu muka fuskanci abinda ke faruwa da iyalinka, hartakai ga tabar maka gidanka.
To yanzu abinda muke so musani shine shin ina itama Maryama take?????Shiru yayi tunda yasan baida amsar basu sai ya kifar da kansa kasa yana wani zare ido. Lol😂
Galadima ne yakuma sake maimaita tambayar daya masa, nan ma yayi shiru.
__Can mai martaba yace tunda baka da bakin magana to kaje duk inda take ka nemo ta kuma wallahi Jamal idan har baka nemo yar mutane ba babu kai babu dawowa cikin masarautar nan, kaje na sallamaka har abada .
Yana gama fadar hukuncinsa yatashi yabar dakin.A haka kowa ya tashi yabarsa inda yana ɗago kansa baiga kowa ba nan da nan ransa yayi mugun ɓaci inda yarasa na menene?
Danshi yasan baida inda zai nemo ta, amma Bakomai xanje duk inda xanje Insha Allah.****
KatsinaFulani tasaki jikinta sosai da yan gidansu nafisat inda tasaba da kowa especially salamatu dan tafi safiya sakin jiki sosai😅😛
A haka har yaranta suka fara sabo da kowa na gidan inda twins basu da gurin zuwa kullum suna tare da mama (mamansu nafisa kenan).
Mama tasaba dasu sosai ji take kamar ita ta haifi mahaifiyarsu,
A haka dai har Allah yasa tazama ta gida inda duk wanda ya shigo gidan zakaga maganar twins kowa twins, Masha Allah.***
Falmata ce take ta kokarin kiran wayarsa amma kwatakwata takasa samunsa inda nan tadinga jan uban tsaki mtssssssssss...
Wanda silar haka har ta janyo hankalin kawarta inda tace...Ke kam dawa kike ta uban tsakinan?
Shiru tamata batare da ta bata amsa ba sai can tagaji tace
Haba ya za ai na dinga kiransa amma wayanshi akashe?Dayake kawartata yar duniya ce sai tace wakenan kike magana?
Yarima mana!.
Wani killer smile tayi Dan dama ita arayuwarta kwatakwata bata son taren yarima da falmata,
Dan bata fuska tayi tace yadai naga kina wani iri kamar mai jin farin ciki da hakan dana faɗa maki?
Gyara zamanta tayi..tace bA farin ciki nake ba ina tunanin mafita ne ya za'ayi kija hankalinsa yaji duk duniya idan bake kika fada masa ba bazai taba yin wani abun ba koda kuwa uwarsa ce tafada masa.
Wata wawiyar runguma takai mata inda tace daɗina dake tawajena kanki yana mugun ja wallahi..
To yanzu dai ya ake ciki? Ina zamuje?
Matso da kawunansu sukayi, suka danyi yar magana kana suka ɗago inda gogar tasaki jiki tana tabama kawarta labarin abinda Jamal yace mata a aurensu za ayi.
***
Kauyen kuraWani daji ne naga sun nufa inda baka ka ganin komai sai bishiyoyi da tsuntsaye daga su babu komai.
Tafiya suke sosai wadda ta daukesu wajen 2_3hrs, suna yinta.
Inda falmatan har tagaji da
tafiyar nan ahankali har Allah yasa suka karasa lafiya.Wani ɗan buka Nagani wanda kamar babu inda mutum zai shiga bare ya zauna yayi rayuwa, amma ahaka naga sun cusa kai direct suka shige..
inda suna shiga wani tsoho Nagani tukuf dashi inda gashi ne duk kansa ga wani irin wari da yake.
Zama sukayi inda suka fara fada masa abinda ke tafe dasu.
Nan wannan tsohon yayi wata iriyar dariya inda yake cewa cikin wata iriyar murya mai amsa amoo, kinzo wurin da babu wanda ya isa yaki baki magani anan wajen domin kuwa kinzo akan gaba,
Dan yanzu haka matarsa bata gida daga ita har ya'yansa dan haka hankalin iyayensa atashe yake dashi kanshi dan baida lokacin da zai saurareki yadda kikeso.
Wannan kenan, kuma mahaifinsa yabasa umarni akan yaje ya maido da yarinyar duk inda take, idan kuma baibi maganarsa ba to ya tabbata babushi babu auren da yake shirin yi kuma zai bar masa masarauta duk inda zaije yaje...
To kinji dai abinda ke faruwaShin boka mai kake tunanin za ayi dan ajanyo hankalin yariman ya tubure akan shi sai Ni zai aura , kuma ita yarinyar ina so asamasa mantuwar ta acikin ransa yamanta da ita yarasa a ina yataba sanin ta ba.
Topa anan akeyinta munji dai abinda falmata da kawarta suke kokarin aikatawa......
AKafta🏃🏃🏃🏃🏃🏃