61_62

66 11 0
                                    

"Fada yanufa kai tsaye batare da tunanin komai ba amma duk da haka yanajin wani irin abu a cikin ransa.

Sallama yayi yashiga batare da ya tsaya dube dube ba ya wuce direct wajen mahaifinsa sarki Yahaya, gaisuwa yafara yi sannan yajuyo yagaida mahaifiyarsa wanda kafin yakai ga hakan ya hangi wani yaro gefen umma yana bacci mai kama dashi sak kamar antsaga kara wani faduwar gaba yaji sai kawai yatsinci kansa da son ganin yaron amma ina ba dama sai yabasar kawai ya gaida mahaifiyar tasa.

Umma ina antashiafiya?

lafiya lau Jamal
Masha Allah
Baka ga baki bane adakin ba???
Sai alokacin yadago buɗe bakin dazaiyi kawai sai ya hangi fulaninsa wanda ko amafarki yaganta bazai mantata ba, bare yanzu da yake ganinta kamar gaske.

Saurin tashi yayi ya nufi wajen su wanda direct wajen ta yanufa batare da wata fargaba ba ko wani abu ba, rungumarta yayi kai tsaye batare da ya tantance itace komai kama da ita ??

Sambatu yafara mata wanda bai da kan gado sai maganganunsa yake....

Gimbiyata yakikamin haka ina kika tafi kika barni?
Kin manta nidin nine rayuwarki kece tawa??

Ko kinmanta kece cikon rayuwata???

Kinmanta yaronmu mune farin cikinsu????

Kintafi kinbarni da tunanin ina rayuwarku zata kasance? Hannunwa zaku faɗa?? Duk banida mai bani amsa sai ke, amma kika tafi kika manta dani.... Menamaki haka Fulani????

Wani irin hawaye ne suka fara zubar mata akan kuncinta wanda silar hakan yasa takara rungumesa tana kuka mai ban tausayi.

Shima hawaye yake iya karfinsa kamar wanda akace masa mahaifiyarsa tarasu.

Kowa a dakin sai da yabasu tausayi saboda irin sambatun da suka dinga yi a tsakaninsu..

*Muryan falmata sukaji tana wani irin zagi kutumar chassss assa ɗin Bura..uba Ni zaka ciwa amana Jamal?
bayan kasan babu aure tsakaninku shine zakazo kana rungumar wannan kwailar yarinyar??

Yar Fulani?

Fulaninma wanda ba asan asalinsu b..,

kafin takarasa taji saukar Mari afuskarta wanda silar wannan mari yasa kowa hankalinsa ya dawo kansa,

Nuna ta yafarayi da hannu keee falmata idan kina iskancinki to ki kiyayeni ki kiyayi matata domin wannan yar Fulani dakike gani tafiye minke sau dubu wallahi, ita yar Fulanin dakike magana takawo min virginity nata dakina kuma tasan Arabia tasan boko ke kuma acikinsu mekika iya??? Mekika sani..?

Mai martaba ne yadaga masa hannu akan ya isa haka Jamal kowa yaxauna a inda yake.

Zama kowa yayi ya gyara nutsuwarsa, inda mai martaba yasa akayi addu'a domin bude taro da addu'a..

Liman ne yayi addu'a sannan akafara jawabi....

Maman mashi ce ta zayyane komai tun daga Zuwan Fulani har ya zuwa yau dawowarta gida..............,

Mai martaba da makarraban fada ne suka fara jajanta abin afili sannan akawa su mama godiya tare da fatan alkairi..

Jawabi sarki ya fara inda aka ma Jamal nasiha sosai mai shiga jiki akan ya riƙe amanar da Allah yabasa, sannan suma matan aka masu tasu nasihar akan surike mijinsu kuma suji tsoron Allah..

Ana cikin yimasu nasiha ne falmata tace... Ranka ya dade ina da magana?

Baba galadima yace mekikeson faɗa ne falmata???

Eh Toh dama ba wani abu bane game da yaran nan da akace zamu zauna da su nidai gaskiya Bazan iya zama da ƴaƴan shegu ba tunda bansan asalinsu ba.

Wata uwar tsawa Jamal yadoka mata
Kafin yafara magana wallahi tallahi falmata kikiyayeni, Ni yarima Jamal ban haifi shegu ba kuma ban haifi ya'yan da ba ya'yan sunnah ba ya'yana ya'yan halak ne dan haka kikiyaye bakinki da harshen ki, nafaɗa maki .

Baba galadima da sauran mutanen wajen ne suka fara lallashinsa akan yayi hakuri yabar maganar tunda dai kowa yasan yaransa ba shegu ba ne Alhamdulillah..

Baba galadima ne yajuyo kan falmata ya kalleta yace... Falmata kintaba ganin jinin sarauta ya aikata laifi anbarsa a cikin gidan yana zaune?????

A'a

Toh Masha Allah
Yara dakike gani ba shegu bane da ubansu kuma da ahalinsu dan yanzu haka kina tare da kowa nasa, to abinda nakeso kigane shine kibi komai ahankali kafin allura ta tono galma kingane abinda nake nufi ko???

Kuma idan baki manta ba lokacin da kukazo keda kawayenki kukama Maryama duka AE da akwai ciki ajikinta silar wannan abu dakuka mata yasa har aka gane akwai juna biyu tare da ita.

To yanzu abinda nakeso dake shine kimanta da komai ki rungumi yar uwarki da ƴaƴan ki da mijinki ku zauna lafiya.

Jin furucin Baba galadima yasa gaba ɗaya jikinta yayi sanyi dan atunaninta gani take kamar duk abinda take baba galadima yasani dan dama can komai take idonsa akanta ( kuma ba dan komai yake mata haka ba sai dan jin wannan bayani da sukayi daga bakin kawarta shiyasaa komai take yana ankare da ita.)

Addu'a aka sake yi ta tashi a taro
Sannan kowa yamike Yakama gabansa....

*****
Yau takama Lahadi yau ne su maman mashi zasu koma jahar su Fulani Maryam tun asuba tatashi take ta shirye shirye da wuri tagama komai nata inda kai tsaye dakin su mama tawuce da aka sauke su tun zuwansu,

Sallama tayi ta shiga hannunta riƙe da farantai mama ce tayi sauri ta tareta suka karasa bakin dining ɗin..

Mama ina kwana??

Lafiya lau Maryamu ya mai gidannaki ???

Yana lafiya mama ina uncle anas din?

Anas yafita naga kamar waya yakema.

Okay tam Bara nafara serving naki kafin shi yadawo.

Haba gimbiya kije kikula da mijinki nidai indan tani Nagode kije Allah Ubangiji yamaki albarka Allah ya raya maki zuri'arki.

Amin mama Nagode sosai kuma Allah yasa kamaki da gidan aljanna.

Amin ....

******

Manage pls zancigaba dayi anjima

Alqalamin

Nafee Kazaure ne

Tadambo writers association
(T.W.A)





Masarautar JamalWhere stories live. Discover now