TYPING...
TADAMBO WRITER'S ASSOCIATION
[Tsintsiya madaurinki daya] _________________________________
https://facebook.com/groups/195183905712588/*IN THE NAME OF ALLAH*
"Lallashinta yafarayi yace falmata meyasa kika gujeni saboda san abun duniya kika je wajen wani bayan kuma kinsan nidin Ni ne na dace dake ba sauranba uhummm?
Nan tayi shiru ta kifar da kanta saboda bata da amsar basa saboda haka tajuya masa baya ta kwanta tana share hawaye..
inda yace da ita Bara naje na samo maki abinda zaki ci daga nan sai na mai dake gida inyaso sai muyi maganar a can.
Wanene kabeer ?
Wacece Falmata ?
__________________
Kabeer ɗan asalin jahar Katsina ne,
babansa irin mutanen nanne dabasa son su tambayi wani abu wajen wani ko wata (ma'ana neman taimako),
saboda ba sa san awulakanta su ko kadan saboda irin Fulanin nanne masu zuciya tagaske,dan haka mahaifinshi ya dage da neman sana'a kowace iri yake yi ahaka har Allah ya taimake shi yasamu sana'ar data riƙe sa shida iyalansa har takai ga yana zuwa garuruwa kai kayan gwanjo inda tafiyar tasa bata tsaya anan Nigeria ba sai da takaisa ga har kasar Niger Republic yana zuwa chan wani gari kusa da border, inda Allah bai barsa ahaka ba nan ya cigaba dakai kaya har Allah ya haɗa sa da wani mutumin kirki nan yasamu komai nasa yana cigaba Alhamdulillah.
Anan har Allah yasa ɗan sa yafara zuwa makaranta kabeer kenan inda ya sakashi wata primary school ta kudi anan Katsina inda yaron yasamu karɓuwa awajen makaranta saboda Allah yabasa kaifin basira sosae saboda yana da background na karatun tun daga wajen mamansa tunda idan yana zaune tana dan koya masa abubuwa. Wannan kenan
"Lokacin da kabeer yashiga primary a lokacin ne ya hadu da Falmata acikin ajinsu lokacin ta rugo da gudu sai ta buge sa
alokacin shikuma ya ɗago da kansa irin cikin jin zafin nan zaiyi masifa sai kawae tace am sorry abhi bangani ba wallahi nan yace bakomai ..
nan tayi murmushi tawuce tace Nagode.To tun daga ranar kabeer da Falmata suka fara ƙawance har takaisu ga shakuwa wadda ba a gane irinta wanda kowa amakarantar dauka ake uwarsu ɗaya ubansu ɗaya saboda wannan kauna dake tsakaninsu.....
Ahaka har Allah yasa suka gama primary sukayi candyn kifi a cikin ruwa😂.
*Wacece falmata* ???
Ita kadai iyayenta suka haifa itace ƴa tilo awajen mamanta da babanta shiyasa suka dauki son duniya suka dora Mata,
bata laifi ba a hukuntata shiyasa tazama lalatacciyyar yarinya yau ka ganta da wannan gobe ka ganta da wannan Allah shirya.Shiyasa lokacin data gama karatun secondary tacema iyayenta ita kasar waje takeso tafita tayi karatu inda kai tsaye mahaifinta ya amince da bukatunta wnn shine dalilin fitar ta kasar waje anan kuma ta haɗu da yarima Jamal....
Muje zuwa masoyana
'''Please share and comments
Always you are in my mind fans and family kudai kucigaba da nuna min kauna 🥰🥰🥰🥰🥰'''