31_32

87 9 2
                                    

_Typing_

                      *TADAMBO WRITER'S ASSOCIATION__*

        *Tsintsiya madaurinki ɗaya🤝🏻* 💐
___________________________________

https://facebook.com/groups/195183905712588/

MASARAUTAR JAMAL  

  "Bangaren umma kuma sai kara gyara Maryam take abin dai ba a cewa komai sai godiyar Allah,

A Haka rayuwa tacigaba da tafiya inda yaran suke girma abin abun burgewa da sha'awa..

**Bayan shekara 2**

Yara sun kara girma sun fara wayo inda suka dakko hallayar mahaifinsu komai nashine jalila ce ma zan ce ta dakko halin mahaifiyarta, wanda duk wani hakuri na uwar ne ta kwasa..

Inda shi kuma uban gayyar Jalil kenan ya dakko hallayar mahaifinsa inda kwata kwata baya son raini gashi muskilin gaske inda har yana nema yazarce yariman..

A haka dai har aka saka su makaranta inda Jalila ita ce babba saboda haka aka ban bata masu aji inda mamansu tace ita idan son ranta ne abarshi a ajin su jalila tunda dai namiji ne, yarima ne yace tunda haka kikeso shikenan Zanyi hakan tunda kinfiso su taso tare, murmushi tayi tace yawwa yarimanah Allah kara lafiya da nisan kwana.
Amin yace...
inda nan kuma ya fara sauya salon zancen....

Soyayya suke mai abun burgewa da tsabta inda Anan sai da yayi wata ajiyar ajikin gimbiyar tasa.

***

Akwana a tashi babu wuya yarima yasamu aiki awani Company inda Allah ya taimake shi ya fara zuwa aiki.. aiki yake sosai babu kama hannun yaro inda kowa awajen yake yabonsa kan kwazonsa da kuma girmama mutane, mutum duk kaskantarsa Jamal baya raina sa duk da kuwa yafito daga tsatson sarauta kuma yanaji da ita.

Wannan ne yasa mutane suke sha'awarsa da duk wani abu daya danganceshi..

Wannan kenan..
"Haka Rayuwa ta cigaba da tafarma yarima yanda yake so, inda ta ko'ina yake samun budi to sai dai muce alhamdulillah..

Bari mu waiwaya muga ya rayuwar falmata take.......

Falmata Nagani da wannan shedanun kawayen nata suna tafiya acikin wata mota kirar Benz inda wata acikinsu mai suna jiddah tace kawata bari kiga mufara kiran wanna malamin muga idan yana gida kawai sai muje direct Dan wallahi shidai aikinsa kamar yankan wukane yanayi komai yayi daidai koda kuwa baka son abun idan har yamaka to wallahi ko a cikin uwarka kake sai kaso fitowa dole,

Shewa suka saka su duka inda falmata tace shiyasa nake mugun yinki wallahi jiddo...
Suna tafiya suna hira har suka isa wannan garin inda malamin yake wanda da zuwansu basu fi minti 5 ba aka shigar dasu gareshi...

Shigarsu kenan malamin yafito daga daƙinsa yana gyara azar zarin wandon sa inda yake ta wangale baki Yana annushuwa yasamu abinda yakeso,

Kallan kallo suke tsakaninsu inda falmata a zuciyarta take cewa ""to shi wannan taya naganshi yafito da wata daga dakin nan kuma da alama ba matarsa ba ce amma ace malamine anya kuwa?? Duk a zuciyarta take wannan tunanin.

Inda sukuma gogayen sun san halinsa dama can idan zai maka magani to dole sai yayi amfani dakai sannan bukatarka zata biya ( wa'iyazubillah, Allah kakara karemu da aika irin wannan Amin.)

Masarautar JamalWhere stories live. Discover now