T. W. A
masarautar jamal
39_40Wani irin kuka take iya ranta wanda kafin kace me har taje bakin gate..
Inda da zuwanta ta ci Sa'a ba kowa dan haka tayi saurin ficewa daga gidan sarautar...
Tashar mota, tanufa kai tsaye inda ita kanta bata san ina zata ba.
Sai ji tayi wasu passengers suna cewa Kano_maiduguri_jigawa_katsina..Nan kawai ta tsinci kanta da fadin motar katsina zan hau.
Nan ya karbi yaranta dake hannunta inda yace muje to Hajiya ga motar can.. sai kishiga ki zauna
Karbar yaranta tayi inda nan tafara tunanin ina zata wata sani a katsina ma?
Tana cikin tunanin ne kawai sai kawarta tafado mata acikin rai da sukayi karatu tare,
Inda nan tayi hamdala, sai can kuma ta tuna"to ni yanzu idan naje katsina gidan suwa zance? Kuma wace unguwa take??
Nan ta faɗa duniyar tunani wanda har akaci Sa'a ta tuna da sunan unguwarsu, inda lokaci guda ta tuna full adress nata. Hamdala tayi ga Allah
Sannan tacigaba da duba yaranta da suka fara bacci tuntuni..***
garin katsina"a tasha aka saukesu inda nan kowa yafara fita ya kama gabansa.
wani mai adaidaita sahune yazo yace hajiya wace unguwa zaki?
nan tayi saurin cewa motar mashi nake nema.
hajiya ae ba anan zaki samu motar mashi ba sai a cikin tasha, dan haka yanzu kizo kihau muje nakaiki inda zaki samu motar.
Toh tace inda ta shiga batare da wata damuwa ba suka nufi cikin sabuwar tasha...
Mota ya tarar mata wadda zata Kaita har mashi.
Kudi taciro ta basa
yaki karba,
inda yace a'a Hajiya kibarshi Ni dan Allah na taimakeki.
Godiya ta masa ta shige mota abinta...*MASHI TOWN*
Haka driver yasauke passengers kowa Yakama gabansa..
Tana nan a tsaye tana jiran abin hawa sai ga wani ɗan Babur yazo ya tsaya yana tambayar Hajiya ina za akaiki ne??
Unguwar kashe Naira zamuje
Oh to shigo kudinki Naira hamsin
Toh ba matsala.
Hawa tayi suka fara tafiya wadda basu dade ba suka isa unguwar kashe Naira.
Inda wannan ɗan machine yace Hajiya gidan wa zaki dan naga ke kamar bakuwa ce agarin ko??Eh tace dashi.
Ina neman gidansu nafisat sani bello ne (carkie)."Sai yace oh Nagane gidansu honourable zakice",
"Allah sarki mutumin kirki bashi da matsalar komai dan kinga ko titin nan da kike gani shine yasa akamana da duk wasu fanfunan ruwa da zaki gani, da makarantu da asibututuwa wallahi duk shine
Ai wanna yaro sai dai muce Allah saka masa da gidan aljanna.Amin tace.
"Inda tace toh yanzu dai ka kaini gidan nasu ko?
Dagudu ma kuwa Hajiya AE zuwa gidansu wadannan mutanen alkairi ne.
Nan suka shiga layin gidansu inda da shiga kasan duk unguwar kowa yasan kowa ne..
Kai tsaye gidansu nafisa muka tunkara inda muna sauka yace min to ga gidan dakike nema nan..Godiya tamasa sosai inda tabashi kudinsa Yakama gabansa...
" Sallama tayi aka amsa mata inda wata sister din nafisan ce ta amsa duk da bansanta ba amma kana ganin fuskar kasan jinita ce.
Gaisawa mukayi inda nace nan ne gidansu nafisah?
Eh tace..
Inda tace nashigo.
nan nashiga parlon gidansu inda ita kuma sistern nata tashiga takira min nafisah.
Da zuwan nafisa sai naga tasaki wani irin ihuu alamun taganeni.
Wani dadi naji araina
inda nan tafara kiran sunana Maryam Jamal dama kina nan??
Wayyo Allah gaskiya baki dadin zuwanki domin kuwa dama ina ta neman yadda zamu hadu Allah baiyi ba.
Shiru nayi inda nake ta murmushin yake wanda nikaina dan dole nakeyinsa..
Can ta kalleni tace amma ba lafiya kike ba wallahi dan naga alamun damuwa atare dake..
Nan tayi murmushin yake inda tafara bata asalin labarin....... komai da yadda akayi har tazo nan ayau.
Shiru nafisa tayi inda tafara bata shawarwari masu amfani..
****
Bari mu leka wajen yarima Jamal shikuma muga wata wainar yake toyawa??Manage pls..
Share
Comments
Vote