49_50

79 8 0
                                    

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai.
Jinjina ba girma agareku iyayena Allah Ubangiji ya kara daukaku A duk inda kuke a fadin duniya Amin..

Wannan shafin nakune kannena  khadija,Maryam, Alamin,Ahmad ,Fatima,yaseer,salahudden. Ina maku sonso fisabilillahi 🥰🥰🥰

Masarautar Jamal
Shafi na arba'in da tara zuwa hamsin.

****

Likitan ne da baba galadima sukayi kanta da sauri  inda likitan yayi kokarin kiran wasu nurses guda biyu domin su taimaka Adora umma agadon dake cikin office ɗin.

Taimakon gaggawa yafara bata inda nan da nan umma tafara dawowa hankalinta cikin karatsi tafara kiran sunan Jamal tana kada ka mutu kabarni yarima kadawo gareni.

" INNALILLAHI WA'INNA ILAIHIR RAJU'UN"... Kalmar da ta iya fada kenan tayi shiru sai wasu irin hawaye kanana dake zubowa da gefen idonta.

Baba galadima ne yamata sannu nan yace da ita ki kwantar da hankalinki halima yarima yana nan bai mutu ba yadai shiga cikin comer ne atunanin likitocin amma muna addu'ar Allah yasa yatashi akankanin lokaci. Amin sukace baki dayansu.

***
Fulani Maryam ce Nagani rike da wasu yan yara masu kyan gaske rike a hannunta yaran sunsha uniform yakarbi jikinsu abin dai abin burgewa ba acewa komai.
Anas Naji nafisat tana kira... Anas Anas Anas, can yafito daga dakin da suke ya nufo inda suke.
Abul ne ya ruga wajen Anas da gudu inda yake uncle uncle good morning?
Morning my son, how are you?
Am fine uncle.
To Masha Allah haka nakesonji dafatan dai ban makarar daku ba dai ko?
Eh uncle.
Okay muje to.
Inda su nafisat yake ya nufa yana zuwa suka gaisa cikin girmamawa yagaida Fulani , cikin sakin fuska ta amsa masa. Domin kuwa kowa agidan yana girmamata especially da sukaga daga gidan da tafito.

Daukar Abul yayi suka nufi wajen parking space inda dayan hannunsa kuma ablah ce yarike dashi suna ta tsokanarsa shikuma sai washe baki yake kamar gonar audu lol😝😂

Makaranta yanufa kaitsaye wanda da zuwansa masu gadin wajen suka bude masa gate ya wuce dayake sunsan juna kuma sun saba sosai da sosai shiyasa da sunga motarsa sun san kowaye acikinta.

***
Umma ce ta tashi a baccin da ta fara tana ma baba galadima maganar tana so taga yaronta ko kallon karshene ta masa wanda kafin takara sa fadar maganar hawaye ya zubo mata.

Baba galadima ne yace tayi hakuri tukunna ana masa wasu gwaje gwajene domin asan awani mataki yake ne. Shiru umma tayi inda aranta dai ji take kamar yarima bazai tashi ba amma sai ta barma ranta tacigaba da yimasa addu'ar samun sauki.

(Haka ake son uwa ta gari idan ya'yanka nacikin damuwa to addu'a ake bukata iyaye suyi ba tunani mexaifaru dasuba).

***
Fulani Maryam ce Nagani kwance kamar wata marar lafiya tayi shiru abinta wanda daga karshe hawayene Nagani suna zubowa daga cikin idonta wanda ita kanta bata san dalilin zuwansu ba.

Amma tunda tashi  da safe bayan tashirya yaranta sai yaji gabanta Yana tafaduwa kamar wani abu zai faru ko kuma yana faruwa. Can kawai sai mijinta yafado mata inda nan da nan taji faduwar gaban takaru.

(Allah sarki kauna duk inda take bata boyuwa)😭😭.. addu'a take tayi iya karfinta duk dan tasamu sassauci amma ina abun kamar kara karuwa yake,  nan kawai ta tashi tashiga banɗaki ta dauro alwala tazo ta tada sallah.. inda take addu'ar Allah ya kawo mata sauki akan komene.

***
Likitoci ne sukayi nasarar samo numfashi sa dakyar inda suna ganin yafara motsi sukayi hamdala ga Allah.

Baba galadima likitannan yakirawo inda yake sanar masa da farfaɗo War yariman. nan baba galadima yaji wani irin daɗi da sanyi sun mamaye shi ba shiri ya nufi dakin da umma take yasanar da ita tashin yariman ai kafin yakarasa umma har tafito da saurinta tana neman inda aka kwantar da yarimanta.
Wata nurse taga tafito daga wani daki sai take tambayarta dan Allah likita ina ne aka kai wani marar lafiya da aka kawo unconscious daxu? Nuna ma umma tayi dakin ta wuce Godiya tamata sannan ta nufi dakin da saurinta inda tana shiga ta hango shi rai ran yana kallon sama, karasawa tayi jikin gadon dayake ta riko hannunsa tafara sambatu yarima kada kabarni ina sonka ina kaunarka duk wani abu dakaga mahaifinka nayi ba wai dan baya sonka bane yake maka haka ba, yana nema maka rayuwa mai kyau ne saboda nan gaba.

Kayi hakuri yarima da auren yarinyar can bata da  tarbiyya ko kadan dan Allah yarima ka hakura Ni zan nema maka auren duk yarinyar dakake so afadin duniyar nan Insha Allah.

Shiru yayi yana jin maganganun mahaifiyar tasa inda nan da na yaji wani irin tausyinta yakamasa,
Yana son yamata magana akan yarinyar amma me bakinsa nauyi yake masa da yazo yin magana.
Kallonsa takeyi nan ta karanci halin dayake ciki sai tayi nurmushi irin nasu na manya ta kallesa da kyau tace nasan kanaso kayi magana akan maganar yarinyar kuma ka kasa ko??
Saurin daga mata kai yayi inda nan ta dafa kafadar sa  tace nasan meke damunka yanzu Jamal insha'Allah zaka dawo daidai.

Daga kai yayi alamun Insha Allah.
Baba galadima ne yayi gyaran Murya yakarasa inda suke yasamu waje ya zauna
Magana yafara yi
Hajia halima Naji duk abinda ya wakana tsakaninki da Jamal kuma nafuskanta lamarin kamar yafaru ne ba ason ransa ba domin kuwa awannan yanayin dayake ciki na lura kamar da sihiri aciki, kuma ba kowa bane yayi wannan abu face yarinyar dayake neman aurenta dan nadade da sanin kowacece ita domin kuwa akwai lokacin da wata yarinya tazo
Nan fada tace tana neman baban Jamal to alokacin nikuma nafito xanje ganin gari sai Naji mai gadi Yana magana akan ita wacece da zatazo ganin sarki kai tsaye.
Sai nazo wajen da suke atsaye suna ta musayar yawu shi yana fada ita tana fada sai nadakatar dasu baki daya, sai nace ke yarinya meke tafe dake sai take cemin ita taimakonmu tazoyi ne tazo wajen mai martaba ne baban Jamal.
Inajin haka nikuma sai Naji jikina yabani wani abu na daban akan yarinyar sai nace wa mai gadi yabarta tashiga amma ya haɗa ta da wani dogari yakaita bangarena.
To yace suka nufi hanyar gida na inda nikuma natsaya ina nazarin maganar yarinyar kafin nan na wuce gidan liman inda nake sanar dashi yazo muje tare koda da wani abun da bamu sani ba, haka liman yataso yabiyoni muka taho fada tare batare da kowa yasan meke faruwa ba.

Nan muka shiga bangarena muka zauna inda yarinya take cemana ga abinda ke tafe da ita nan ta min bayanin komai har zuwa wajen bokayen da sukayi da yadda suka kira Jamal akan hankalinsa ya koma kanta koda kuwa uwarsa ce tamasa magana kada yaji sai ita.

Yarinya tagama zayyane min komai tundaga kan bokan farko da suka je har zuwa na karshe babu abinda ta boyemin

Salati umma tasaka inda nan da nan hawaye ya zubo mata tafara kuka kamar ranta zai fita inda tanaji tana gani za arabata da gudan jininta akan soyayyar wata.
Baba galadima ne ya lallasheta har yasamu tayi shiru sannan yacigaba dacewa.. mu yanzu munyanke shawarar barin ya aureta saboda kuwa idan har bai aureta ba yana cikin tashin hankali dan kuwa tace bazata taba barinsa yayi farin ciki a rayuwarsa ba Kinga kuwa hana auren kamar wata masifa ce muka jefasa ciki. Yanzu kiyi la akari da mAganar yarinyar kike amma me bakinsa yamasa nauyi akan ya tankamaki tunda kuwa ta riga da tagama dashi.

Shiru umma tayi tana nazari can kuma sai tace to amma kana ganin mai martaba zai yarda da hakan????

Manage pls

02/05/2021

Masarautar JamalWhere stories live. Discover now