_Typing_
*TADAMBO WRITER'S ASSOCIATION__*
*Tsintsiya madaurinki ɗaya🤝🏻* 💐
___________________________________https://facebook.com/groups/195183905712588/
*MASARAUTAR JAMAL*
🅿️2️⃣7️⃣➡️2️⃣8️⃣
Bayan wata ɗaya da aikin Fulani yarima yasa aka dakko masa falmata inda tabi ta lalace ta rame kamar ba ita ba falmata yar gayu mai ji da kyau aji amma yanzu duk babu,
Wani bafade ne ya tuso ƙeyarta har gaban yarima Jamal inda nan ya fara turata da karfinsa, danshi tunda tazo gidan nan yaji bata kwanta masa ba ya tsaneta yadda ba ta zato ( nikuwa nace hmmmm falmata ke awajen kowa baki da farin jini 🤔🤔).
Fulani Maryam ce ta tashi tana ganin fuskan falmatan tafara ƙoƙarin barin wajen,
Nan yarima daya fuskanci halin datake ciki na halin tsoron datake ciki kawai sai ya fusge yariketa gam yadda bazata iya barin wajen ba.
"Nan yace da bafaden dake tsaye abayan falmata ...
Uhmm barkono kadakko min dorina da gishiri mai yaji aciki yanzu yanzu nan.
To yace dashi. Inda ya fara tafiya domin cika aikin da aka saka shi.
Barkono Nagani da wata ƙatuwar dorina kamar ta dukan jakai da dokuna, naga ya tunkaro inda suke dayan hannunsa kuma gishiri ne mai yaji aciki.
Yana zuwa ya durkusa yace ƴallabai angama ga abinda kasa ayi nan.
Wani shu'umin murmushi yarima yayi inda yace toh barkono kiramin Sarkin dorina yanzu nan..
"Meƙewa yayi yafara tafiya don cika umarnin yarima".
Sarkin dorina ne yazo gaban yarima nan ya zube yafara meka gaisuwa, inda yarima yace hukunci nake so ama wannan yarinyar da ta dokar min sarauniyata.
"To ƴallabai angama. Nan Sarkin dorina yafara naɗe hannun riga inda yake ƙoƙarin gyara dorinarsa domin kuwa yasan yau zai samu nama gaskiya😂
Daga dorinar dazaiyi Fulani ta kwala wani irin kara awajen nan hankalin kowa yadawo kanta har falmata dake daure awajen,
Saurin dakatar da Sarkin dorina tayi inda tafara cewa.... Yarimana ina neman alfarma 👏 akan arage mata wannan hukuncin Please, saboda yayi mata tsawo dayawa kuma a matsayinta na ƴa mace bai dace amata wannan dukan ba, Ni tama laifi to na roka mata yafiya dan Allah, aduba wannan maganar amata uzuri. Gwara amata wani hukuncin ba wannan ba.
Yarima ne ya kalleta yace babynah yanzu ina kallo nabarta haka tatafi batare da wani sheda ba a jikinta?
Kinmanta ita ce taso tayi silar rasa babynmu?? Dake kanki?
Uhmmmm?"Shiru Fulani tayi Jimmm kaɗan tace... nasani yarimanah amma Ni nayafemata sai dai akiyayi gaba kawai, ko wannan hukuncin da akamata nazaman yari ya ishe ta izna, ko nan gaba zataji tsoron sake aikata aiki irin wannan.
"Rungumota yayi inda yabata sumbata mai kyau😘😘😘😘
Ina alfahari dake matsayin mata da Allah yabani, gaskiya nayi dace da ace natsaya kallon sakarkarun matan mu da tuni angama lalatani abanza ( hannunka mai sanda yayi kenan ma'ana da falmata yake).
"Nima haka yarimanah sai dai mu kara gode ma Allah daya ya haɗamu a inuwa ɗaya👩❤️👨.
Duk abinda suke yi falmata najinsu kuma tasan sarai da ita suke wannan maganganun ...
Sarkin dorina ya katsewa kowa duniyar dayake inda ya fara cewa to ƴallabai yanzu shikenan ba wani hukunci da za amata taci bilis kenan?
__ Eh gaskiya saboda sarauniyata tace ta hakura kaga kenan babu amfanin yin hukunci tunda wadda za'ayi domin ta tace ta yafe.
To shikenan ƴallabai.
*Bayan wata 9*
*******
Fulani Maryam na hanga awata fadarta inda wasu jakadai ne akusa da ita, wata tana matsa mata ƙafafuwanta, wasu kuma suna mata filfita inda acikinsu na hangi wata da katon ƙoƙo tana tahowa wajensu inda da zuwanta tafara miƙa gaisuwa ga sauraniyar gida wato Fulani Maryam.
Ranke daɗe sakone daga uwar kowa (maman yarima), tace kisha yanzu saboda abinda ke cikinki.
Karba tayi batare da tunanin komai ba tafara sha..... Nan tagama shanyewa tasssss sannan ta meka ma zuwaire ƙokon tace Nagode.
*Bayan awa 3*
Fulani na hanga a tsakiyar falon ta tana ta kai da komowa inda tarasa meke mata daɗi a duniyar (ciwo takeji amma takasa gane wani irin ciwo ne. Nikuwa dana fahimta sai naga babu marabar ciwonta da cikin jikinta domin kuwa shine yau ko gobe haihuwa).
Komawa daki tayi ta kwanta akan gado ko tasamu sauƙin ciwon amma ina kamar karasa ake , inda nan ta sakko ta nemi fitowa dan neman maganin da zata sha.
wanda kafin takai ga karasawa bakin kofar taji marar ta tamata wani irin murdawa, nan tafara ƙoƙarin dakko wayarta domin kiran yarima ......... Kira take amma shiru ba a daga ba. Har wajen missed call 20 tamasa
*Lokacin shikuma yashiga meeting yasaka wayarsa a silent shine dalilin rashin daga wayarsa.
Galabaita take sosai inda nan ta kuma ɗaukar wayarta takira umman yarima inda take sanar da ita mutuwa zatayi dan abinka ga fari bata san komenene ba kawai taji dai mararta naciwo...lol😃😃
Umma ce tayi saurin tambayarta meyake faruwa ne Fulani??
Umma marata! marata !! Mutuwa zanyi ki Takamani kada na mutu...
Saurin sakin wayar tayi inda nan ta danna kiran yarima inda aka ci Sa'a yafito daga meeting ɗin kenan ya bude wayarsa yaga missed call 20, shine kiran umma yashigo masa saurin ɗagawa yayi inda tana fara magana tace komai kake kabaro sa kataho wajen matarka domin kuwa ba ta da lafiya nima yanzu take sanar dani tana na taimake ta....... Ai kafin takarasa maganar tuni yakashe wayar yashiga mota.......
Umma ce Nagani tana kokarin kamata su tashi inda Baba kaltume take tayata har Allah yasa suka daga ta suka shiga mota sai asibiti.................
Suna zuwa babu wani bata lokaci aka karbe su, direct dakin haihuwa akayi da ita domin kuwa duk wanda yaganta a yanayin nan yasan haihuwa ce dole.
*After 3hrs*
Kukan jarirai naji dayawa ya karade kunne na inda naka sa ganewa a ina wannan kukan yake fitowa..... .........
..juyawar daxanyi kawai sai naga daddy yarima gaban umma yana meka mata yara😁😁😁😁😛😛😛
Kashhhhhh bahaka naso nabarku ba
Amma next zamu haɗe
😊😊😊😊😊😊😊😊🤩🤩🤩🤩🤩🤩
*Son so nake maku my fans*
❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
_03/04/2020_
~NAK~