This page I dedicate to you Sadeeq mainah Nagode sosai Allah yabar zumunci . Wannan shafin baki dayansa naka ne.
****
Fadar mai martaba baki ɗayansu suka nufa inda na hangi Jamal da iyalansa agefen sarki sai umma da sauran mutanen dake fada, jawabi sarki ya fara inda wazeeri da hakiman wajen suka nutsu kowa yakama hankalinsa,...Tunda har haka tana iya faruwa a cikin al'umma kuma muna gani dole zamu dauki mataki akan haka domin kuwa falmata tayi babban kuskure na aikata wannan laifi da tayi, domin kuwa ko a addini abinda ta aikata dole ta karbi hukuncin sa domin kuwa tayi zina da aurenta, kuma tayi shirka, akan abinda Ubangiji bayaso.
Kowa shiru yayi yana sauraren hukuncin da mai martaba zai yanke, can sukaji yace, Sarkin gida kaje da falmata ataho da wannan boka da take zuwa garesa, domin muji ta bakinsa.
To yallabai, nan Sarkin gida da wasu dogari daga bakin kofa suka nufi hanyar garin nan tare da falmata da yarima don tahowa, da wannan boka,.
****
Tafiya suke sosai cikin dajin wanda baka jin motsin komai sai na tsuntsaye da iska amma banda wannan babu abinda kake iya jiyowa.Wata yar bukka na hanga inda wannan boka yake alfasar shi da mutanensa da suke kauce hanya, Sarkin gida ne ya nusar da Jamal kamar ga gidan can rankai dade, yarima ne ya juyo dan ganin abinda Sarkin gida yake nuna masa, nan ya nuna ma habu driver ga hanyar da zasu bi.
Habu ne ya chanja akalar tukin nasa zuwa ga inda yarima ya umarce da yabi, ko minti 3 ba'a yi ba suka isa dokin kofar bukkar nan, wanda da isar su wajen suka fara jiyo wani irin wari na tashi kamar mushe ya mutu har ya fashe , dode hanci suka fara inda nan take Jamal yaja baya yana rufe hanci dan bai san warin menene ba, alama yayiwa da Sarkin gida ya shiga yafito masu da shi, shigar da zai yi yayi gamo da gawar wannan boka ta ruɓe har tafara tsutsa(innalillahi wa'inna ilaihir raju'un Allahumma ajiirni fimusibati wa'akalifni khairan Minha).
Dawowa yayi da sauri yana sanar da yarima kan abinda ya gani, kafin Sarkin gida yagama bada labarin abinda ya gani tuni falmata ta ruga tashige bukkar bokan tana kwala ihu, kafin kace me tuni tafara ficewa a hayyacinta, tana ta surutai marar sa ma'ana, nan Jamal yasa Sarkin gida yafito da ita tare da bashi Umarnin ya sata a mota su koma gida, duk da yanajin TSANARTA aransa amma yana tausaya mata duk da ita din ba abin tausayi bace.****
Mai martaba ne ya yanke hukunci da kansa inda yasa a kayiwa falmata hukuncin bulala, tare da aiki mai tsanani a gidan kaso.
Wanda atake anan yarima Jamal ya kara tabbatar da sakin da yayi ma falmata agaban shedu.Manage pls 🥰