T.w.A
MASARAUTAR JAMAL
37_38Bayan komawarsa gida babu inda yanufa sai fadar sarki...
inda iyayensa suke nan yaje ya tarar dasu duka zaune yafara meka gaisuwa.
Nan yadago kansa inda ya kalli mahaifinsa yace Allah taimaki mai martaba
Dama magana ce nAzo da ita.Galadima yace munajinka yarima meke tafe dakai?
Nan ya sunkuyar dakai kasa inda ya fara kamekame saboda kunyar abinda zai fada.
Galadima ne yakuma cewa yarima kai muke saurare....Shiru yayi kana can yace ....
Allah ya taimake ka, aure ne nakeso zan sake.
Ba sarki kadai ba hatta galadima da waziri, sai da sukayi mamakin wannan maganar data fito daga bakinsa.Inda nan ran mai martaba yabaci yace akan wani dalili zaka sake aure jamalu?
Shiru yayi tunda yasan baida dalili kuma haka kawai yaji yana son yakara aure..
Galadima ne yayi gyaran Murya.. inda yace munji bukatarka amma munaso kafada mana yarinyar da kake nema yar ina ce kuma waye ubanta??
Cikin saurin murya yace yar gidan Alhaji......nan yakwashe duka labarin asalinta dana mahaifinta yabasu.
Inda galadima yace to madallah Jamal, zamuyi bincike kan al amarin Insha Allah.
Toh Baba galadima Nagode Allah kara girma
Amin yace..
Kana aka rufe taro da addu'a
Inda shidai mai martaba sai tunani yake akan maganar.amma yazaiyi tunda yayansa yyi magana baida abinda zai kuma cewa.
(Tunda asali can galadima shine babba agidansu baban Jamal mai martaba Yahaya kenan, amma saboda hakurinsa da kuma iya jajurcewa shiyasa yazamo sarki acikinsu)..Bangarensa yanufa inda yasameta kwance kan sofa tana kallon wani Film na India, inda hankalinta gaba daya ta maidashi kan Film din, dan bata san yashigo parlon ba.
Kawai sai ganinsa tayi yana shafa mata fuska ta bayanta,
Saurin firgita tayi inda nan tasaki wani kara har saida takusa faduwa, yayi saurin tare ta
Wani murmushi yasakar mata inda itama ta maida masa martani danata smile din.Zama sukayi sosai inda ya kalleta yace so nake muyi magana ta fahimta matata..
Okay inajinka..
Kiyi hakuri da abinda zan faɗa maki dan Allah ki fuskanceni,
Ba wai dan bana samun komai wajenki ba a'a ba haka bane,Ina so zan kara aure ne!
Wani irin faduwar gaba taji ta sameta alokaci guda
Nan da nan tafara hawaye tana cewa dame na rage ka dashi yarima?
Meka nema karasa awajena?
Nan da nan hawaye ya cika mata fuska
Inda shi kuma ya fara lallashi yana bata baki ahaka dai har tayi shiru
Inda yacigaba da cewa wadda zan aura bazata gwada maki komai ba kinfita komai bbu abinda zata nuna mk,awajen Jamal kinfi kowace mace saboda haka Ni kaina wannan auren jinsa nake kamar ƙaddara dan wallahi yarinyar banajinta a can cikin raina kamar yadda nakejinki..
Yarinyar ba kowa bace face..falmata.
Wani irin kara ta saki wanda kafin kace me har ta ...........
Tofa ana wata ga wata
Shin mekuke tunanin Fulani tayi .
1 suma tayi?
2 shake wuyan Jamal?
3 fita tayi daga gidan ??
Ko kome???Amsarku nake jira itace zata bani damar karasa maku book din nan
Share✅
Comments✅
Vote✅
Following ✅
Editing❎